Daga Nadia Ahmad
Yunkurin Amurka na aikawa da kayayyakin agaji zuwa Gaza ta hanyar saman tekun Gaza yana tafiya da kyau. Mako daya kawai hanyar wadda aka yi wata biyu ana yi a kan Dala miliyan 320 ta yi amfani da ita, kafin ta lalace saboda rashin yanayi mai kyau, kuma har yanzu gyara ake yi.
Taimakon mutanen Gaza da kayayyakin agaji abu ne mai kyau a zahiri. Sai dai idan aka lura da kyau cikin tsanaki za a ga akwai wata manufar ta kara kawo rudani a yankin da yunkurin kwasar ganimar makamashi.
Lura da dadadden tarihin boye-boye da kamun kafa da ya dabaibaye harkar man fetur da iskar gas, za a iya cewa akwai wata manufar daban da Amurka da ita wajen gina wannan hanyar.
Hanyar ta yi daidai da tsarin Amurka na amfani da wasu dabaru wajen aiwatar da wasu boyayyun manufofinta, musamman idan ana batun gas. Irin hakan ne ya auku wajen kara ta'azzara sabani tsakanin Ecuador da Mexico da kuma tsakanin Guyana da Venezuela.
Jibge sojojin Amurka
Samar da hanyar ta kara fito da tsarin Sakataren Gwamnatin Amurka Anthony Blinken na tsoma baki a harkokin yankin Gabas ta Tsakiya da rura wutar yaki ta hanyar amfani da sunan diflomasiyya.
Duk da alkawarin da suka dauka na kawo karshen yake-yake da dabbaka kare hakkin dan Adam, har yanzu Gwamnatin Shugaba Biden ba ta aiki da da'awarta.
Akwai alamar tambaya a kan yunkurin gina hanyar domin taimaka wa mutanen Gaza daga bala'in da suke ciki.
Yawancin kayayyakin agaji dole su ratsa ta iyakokin kasashe, amma har yanzu takunkumin hana kai kayayyakin agaji da Isra'ila ta kakaba wa Falasdinu yana nan, wanda ya hana kai musu dauki na kayayyakin amfani da na masarufi.
Da wannan ne ake ganin aikin na Amurka akwai wata manufar. Babbar matsalar ma ita ce kara kai sojojin Amurka a yankin.
Yadda Amurka ta aika da karin sojoji 1,000 wai domin sa hannu a aikin agajin ya kara saka shakku a kan samar da hanyar, musamman ganin yadda Amurka ke ba Isra'ila agajin soji.
Wannan kai sojojin da ake yi kusa da Gaza zai iya taimakawa wajen kara kusantar da Amurka da Isra'ila zuwa Gaza da, da kuma saukaka musu hanyoyin cimma bukatunsu, ciki har da satar gas da yake jibge a yankin.
Wannan zai iya zama gaskiya ga Kamfanin Chevron, wanda ya dade yana aiki da Isra'ila wajen hako iskar gas kuma yake aiki da wasu kamfanonin Isra'ila a wasu muhimman ayyuka.
Blinken yana amsa tambayoyi a Gidan Gwamnatin Amurka da ke Birnin Washington a ranar 21 ga Mayun 2024. Hoto: Reuters
Kamar yadda Shugaban Kasa Donald Trump ya dauko tsoho Shugaban ExxonMobil Rex Tillerson a matsayin Sakataren Gwamnatinsa, shi kuma Shugaba Biden, Blinken, wanda tsohon babban mashawarcin kamfanin Chevron ne ya dauko, saboda kwarwarsa a diflomasiyyar makamashi.
Yadda Blinken ya yi tafiye-tafiye guda 75 zuwa kasashe 84 ya nuna cewa a shirye yake a aikin diflomasiyya.
Sai dai a daya gefen kuma, ana ganin duk wannan yunkurin bai rasa nasaba da kokarinsu na jefa hannu a bangaren man fetur da iskar gas na wasu kasashen.
Yadda Blinken ke zirga-zirga a duniya, ya nuna manufar gwamnatin Amurka a fili na fifita son ransu da fifita bukatunta a kan Kare hakkin dan Adam, musamman ganin yadda ta kawar da kai daga kisan kiyashin da ake yi a Gaza. Da a ce Blinken yana da wani take, da ya zama, "A tarwatsa su, a kwashe gangunan man fetur dinsu!"
Hannun Chevron
Aikin da Amurka ta yi na samar da hanyar da kuma kasancewar sojojinta a yankin zai iya taimakawa Chevron wajen samun shiga tekun Falasdinu da hako albarkatunta ba tare da la'aikari da ka'idojin muhalli na Falasdinun ba.
Samun shigar Chevron kasar ta Falasdinu zai sa Isra'ila ta samu makamashi na bagas ta bayan fage.
Samun dama a kan iskar gas a yankin zai sa kamfanin Chevron da kamfanonin Amurka su kara arziki, amma kuma zai kara rura wutar rikicin yankin. Kara fadada masana'antar makamashin Isra'ila da Amurka ba abu ne da kasashe suke kauna ba.
Kamfanin Chevron yana da tarihin wajen harkokin lalacewar muhalli da tauye hakkin dan Adam, musamman idan akwai batun man fetur da iskar gas.
Wani boyayyen Kamfanin kwararru na WestExec da Blinken da Michèle Flournoy suka kirkira a shekarar 2027 domin aikin ba da shawarwari sun sa an kara sa alamar tambaya a kan gaskiyar gwamnatin Biden da kuma yiwuwar sa hannun kamfanin a harkokin gwamnatin kasar.
Bayan Biden ya dare karagar mulki a Fabrailun 2021, ne sojojin Myanmar suka hambarar da gwamantinsu na dimokuradiyya.
Chevron, wanda ke da tarihin aiki tare da kamfanonin gwamnatin sojin kasar, sannan ya shiga tsakani wajen hana a kakaba wa sojojin takunkumi da zai hana su aiki.
Wani misalin shi ne, Kamfanin Chevron ya yi kunnen uwar shegu da hukuncin biyan Dala biliyan 9.5 ga kasar Ecuador saboda gurbata muhallin kasar ta hanyar daukaka kara, tare kai karar lauya Steven Donzinger da zarginsa da cin hanci.
Hakan ya sa wani alkali a Manhatta ya yi watsi da hukuncin Kotun Kolin Ecuador na biyan diyyar.
A karshe-karshen shekarar 2024, a Taron Tattalin Arziki na Duniya na bana, Blinken ya gabatar da jawabi a game da matsalolin da za a iya fuskanta bayan yakin na Gaza da yankin Gabas ta Tsakiya, inda ya nanata muhimmancin samar da kasar Falasdinu zai zaman kanta.
Shi kuma Shugaban Chevron Michael Wirth ya nuna fargabarsa a kan matsalolin kasuwancin mai da hauhawar farashinsa saboda yakin.
Yadda Gwamnatin Biden ta ki sa baki a irin tauye hakkin dan Adam da ake yi a Myammar da na Isra'ila da kuma alakarta da tsohon ma'aikacin WestExec sun sa kara bayyana alamar shakku a kanta.
Tsarin Chevron a baya na muhinmantar da mai a kan komai ya nuna cewa kamfanin na shiga gwannatin sosai domin cin ribarta ne.
Daukin kasashen MENA
A daidai lokacin da ake cigaba da wannan tata-burzar, ya zama dole kasashen Gabas ta Tsakiya de Arewacin Afirka wato MENA su dauki mataki domin hana Amurka da Isra'ila wannan cin kashin. Hana kai man fetur zuwa Isra'ila ba karamin illa zai mata ba wajen illata tattalin arzikinta.
Yana da kyau kasashen su kakaba wa Isra'ila takunkumi tare da tursasa ta da dage takunkumin hana kai kayayyakin agaji zuwa Gaza ta kuma satar albarkatun Falasdinu.
A yanzu da zaben Amurka ke karatowa, yanzu ne lokacin da kasashen na MENA ya fi dacewa su dauki mataki wajen matsa lamba. Za a iya biya maka dukkan bukatunka a shekarar zabe, sannan dukkan kasashen biyu a yanzu ba sa bukatar wata matsalar da wata kasa.
Yanzu babu lokacin da za a cigaba da zaman jira- mutanen Gaza suna cikin wahalar da za su iya cigaba da zaman jira ba domin wahalar karuwa take yi, sannan kamfanin Chevron da ke birnin California na Amurka na sace musu albarkatu ta bayan fage.
Harkokin diflomasiyyar Biden sun nuna yadda yake zaban wasu kasashen Musulmai yake kyautata musu, amma yake muzguna wa wasu.
Yadda kasar ta dauki batun kai kayayyakin agaji zuwa kasashen Syria da Afghanistan da sauransu ya nuna yadda suke muhimmantar da son ransu a kan taimakon agajin.
Idan akwai gasjiya, dole Blinken da Biden su fito wajen bayyana ayyukansu a zahiri, sannan su ba bukatun Falasdinawa muhimmanci a kan albarkatunta.
Wannan kuma na nufin a dage takunkumin hana kai kayayyakin agaji da zuba jari tare da tallafawa Falasdinu wajen zama kasa mai cikakken iko.
Zaman lafiya mai dorewa na bukatar kididdige kisan kiyashi da Isra'ila ta yi a Gaza da samar da hanyar hadaka wajen kasuwancin makamashi mai kyau da sauki, ba wai amfani da karfin soji ba wajen satar albarkatun wata kasa da sunan agaza mata.
Ta hanyar adalci da bayar da 'yanci tare da la'aikari da bukatun Falasdinawa na kayayyakin agaji sama da riba ne kawai kamfanoni irin su Chevron za su taimaka wajen rage walahar da mutanen Gaza suke ciki. Lallai yanzu ne lokacin da ya kamata kasashen MENA su kawo dauki kafin lokaci ya kure musu.
Nadia Ahmad Farfesa ce a bangaren shari'a da take zaune a Orlando da ke Jihar Florida, kuma mai bincike a Cibiyar Tsaro da Kare Hakkin na Rutgers kuma daliba mai nazarin digirin digirgir a fannin muhalli a Jami'ar Yale. Tana cikin wadanda suka assasa Kungiyar Ceasefire a 2024.