Daga Ian Proud
Watan da ya gabata na karshen shekarar 2024 ya shaida zangza-zangar fararen hula a babban birnin Georgia, Tbilisi da kuma yadda kafafen yada labaran Yamma suka dinga bayyana lamarin a matsayin "zanga-zangar goyon bayan Turai".
A yayin da ruwa ya kure wa dan kada ga wa'adin mulkin shekaru shida na Salome Zourabichvili a 'yar karamar kasar da ke iyakar Turai da Asiya, masu sharhi na Ƙasashen Yamma sun dinga kokarin ganin an ƙi rantsar da sabon shugaban kasa Mikhaeil Kavelashvili tare da bayyana shi a matsayin wanda bai halasta ba.
Zourabichvili ya nuna tirjiya ta hanyar kin yin murabus duk da ta bayyana kararara Jam'iyyar 'Georgia Dream' ce ke da rinjaye a zabe.
Amurka da Birtaniya sun taka rawarsu ta hanyar saka tankunkumai ga jami'an gwamnatin jam'iyyar 'Georgia Dream'.
Mun zura idanuwanmu don ganin yiwuwar wani juyin mulki zai afku. A karshe, Kavelashvili ya karbi rantsuwa ba tare da wata matsala ba, sai kuma kafafen yada labarai na kasashen waje suka koma bayar da wasu labaran.
Sauye-Sauye a Kundin Tsarin Mulki
Juya bayan agogo ga tsarin Disamban 2018, rantsar da Zourabichvili a matsayin zababben shugaban kasa na kai tsaye ya yi daidai da fara aikin sabon kundin tsarin mulkin kasar.
Sauyin ya zama wani martani ne ga damuwa kan rashawa a tsarin zaben Georgia tun bayan samun 'yancin kai a 1991.
Sabon kundin tsarin mulkin ya wajabta cewa shugaban kasa zai zama kamar na je ka na yi ka ne, kuma daga 2024, wakilan majalisa ne za su dinga zabar sa. Wannan irin tsarin da ake amfani da shi a kasashen Turai, ciki har da Jamus.
A saboda haka, sauya kundin tsarin mulkin Georgia zuwa tsarin da ake da shi a mafi yawancin kasashen Turai ba laifi ba ne. Kuma Zourabichvili ma ba ta nuna rashin amincewa ga tsarin ba kafin bazarar 2024.
Sabon kunin tsarin mulkin y kuma samar da tanade-tanaden wakilcin zabuka da zabe ta kwamfuta, wanda a lokacin 'yan adawa ma suka nuna amincewa da shi.
Ya zuwa 2024, Jam'iyyar 'Georgia Dream' ta lashe zabukan 'yan majalisa na 26 ga oktoba da kashi 54, inda sauran kananan jam'iyyun adawa suka samu kashi 37.
A yayin da jami';an sanya idanu na OSCE suka gano kura-kurai a bangarori da dama na zaben, amma sun kuma ce an shirya shi yadda ya kamata.
Zourabichvili ya jagoranci gangamin neman kar a amince da sakamakon, kuma Birtaniya, Amurka, suka taka rawar goyon bayanta.
Dan majalisar wakilai Joe Wilson, shugaban tawagar Amurka ta Helsinki kan tsaro da Kwamitin Hadin Kai a Turai, ya yi kira ta shafin sada zumunta da kar a amince da sakamakon da ya kira "Mummunan Mafarkin Georgia", abinda yake nufin jam'iyyar 'Georgia Dream'.
Kwamitin na Helsinki ya kuma yi kira da a saka takunkumi ga jami'an Georgia, kuma a ranar 19 ga Disamba, Amurka da Birtaniya sun saka takunkumi ga jami'an ma'aikatar harkokin cikin gida su biyar.
A ranar 27 ga Disamba, Amurka ta sake saka takunkumi ga jagoran jam'iyyar 'Georgia Dream' Bidziza Ivanishvili, kamar yadda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya bayyana, inda ya ce dalili shi ne "yin kafar ungulu ga makomar Georgia".
Tarayyar Turai ta dawo da neman Visa ga jami'an diplomasiyyar Georgia da ke son shiga kasashensu wanda a baya ba sa bukata.
Zanga-Zangar farko a Tbilisi ta biyo bayan zaben 26 ga Oktoba wadda ta koma rikici, aka kuma yi fargabar rikicin na iya koma wa kamar na Kiev, wanda ya janyo juyin mulki ga shugaban Ukraine na wancan lokacin Viktor Yanukovych a watan Fabrairun 2014.
Bambancin sa Tbilisi shi ne an so a samar da yanayin juyin mulki da shugabar kasar Georgia za ta ci gaba da kasancewa a kan mulki ba bisa ka'ida ba.
Game da hakan, Zourabichvili ta zama 'yar gwagwarmayar siyasa mafi muni da ke neman dama, inda ta so yin amfani da zargin kura-kurai a zabe don ci gaba da zama a kan mulki.
Sai dai kuma, rikicin da y biyo bayan zaben, duk da ya yadu sosai, sai ya koma zanga-zangar lumana da 'yan sandan Georgia uka yi kokarin magancewa cikin tsanaki.
Turai da Amurka sun so daukar nauyin kifar da halastacciyar gwamnati a Tbilisi inda ba su nasara ba, kuma a yanzu muna cikin rikicin kkan yadda kasashen Yamma za su sake kulla dangantaka.
Me ya sa Turkiyya ke da muhimmanci
Abubuwan da suka afku a baya-bayan nan na bayar da isassun hujjoji cewa maimakon bin zabin Turai da Amurka, ya kamata Georgia ta mayar da hankali ga hadin kai sosai da masu kusnaci da ita, wato Turkiyya.
Kamar Georgia, hanyar da Turkiyya ke bi na shiga Tarayyar Turai ta sauka daga kan layi.
Duk da cewa an bayyana dakatar da shirin shigar, Ina tantamar cewa wata rana Turkiyya za ta iya samun damar zama cikakkiyar mambar tarayyar.
Asali dai, ban taba tunanin kungiyar da ke da dukkan mambobi Kiristoci za su karbi kasa Musulmai irin Turkiyya ta zama mambarsu ba, kuma idan tafiya ta yi tafiya, za ta zama kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Turai.
Tsadar karbar Turkiyya a Tarayyar Turai na da babban kalubale sama da na karbar Ukraine wadda za ta lalata kasafin kudin Tarayyar.
Game da Georgia, manufar Tarayyar Turai ba ta wuce ta gina kasa, wanda jam'iyyar 'Georgia Dream' ke wa kallon tsoma baki daga kasashen waje.
Gaskiyar zance shi ne, kamar yadda na rubuta a baya, cewa Georgia ta tafka babbar asara bayan sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci marar shinge da Tarayyar Turai a 2016.
Game da Ukraine kuma, Tarayyar Turai na son kasa irin Georgia wadda wakila ba za a iya samu ba, kuma Georgia na son amfana da tattalin arzikin Turai wanda kuma Turan ba lallai ta yarda ba.
Haka zalika kamar hanyar 'Euro-Atlantic' da 'yan majalisar dokokin Amurka ke magana a kai - wata alama ce ta shiuga NATO a nan gaba - zabi ne marar kyau ga Georgia.
Saboda jefa ta cikin yaki da Rasha a 2008 saboda yunkurinta na zama mamban NATO a wancan lokacin, zai zama abu mai wahala ga shugabannin Georgia su sake dawo da wannan tunani.
Wannan bai sanya Georgia zama mai goyo bayan Rasha ba. Har yanzu Georgia ba ta da alakar diplomasiyya da Rasha, kuma 'Georgia Dream' na son karbe yankunan da suka balle na Abkhazia da Ossetia ta Kudu.
Turkiyya ta dauki matakin zama a tsakiya da nuna dattijantaka kan dimokuradiyyar Georgia bayan gudanar da zaben.
Saboda kusanci da juna, Turkiyya da Georgia suna gina kakkarfan kasuwanci da zuba jari tsakaninsu.
A yayin da alakar kasuwancin ta fi amfanar da Turkiyya saboda girmanta, tana da rarar dala biliyan biyu kowacce shekara, kuma hakan ya tabbata saboda kasnacewar Ankara mafi girman zuba jarin kai tsaye a Georgia.
Wannan kawance na da muhimmanci a lokacin da Turkiyya da makotanta na kudu suke da muhimmanci ga Turai wajen samar da makamashi sakamakon yadda Rasha ta cire Turai daga kasuwar makamashinta.
Hanyar dakon gas ta kudu - da ta taso daga Azerbaijan, Georgia da Turkiyya - ta samu karin matsayi bayan matakin da Ukraine ta dauka na yanke safarar mai zuwa Turai daga watan Janairu.
Turkiyya da Georgia sun zabi kar su kalli takunkuman Turai kan Rasha, saboda sun san irin illar tattalin arzikin a wannan mataki zi janyo musu.
A yayin da take da muhimmanci a tsakanin kasashen NATO, Turkiyya ta sha yunkurin ganin an sulhunta a Ukraine ta hanyar taron sulhu na Istanbul na 22 ga Fabrairu ko rawar da ta taka wajen tabbatar da Yarjejeniyar Safarar Hatsi a Tekun Bahar Maliya.
Jam'iyyar Dream ta Georgia ta bayyana damuwarta game da yakin Ukraine, saboda yadda yakin ya illata t - saboa rashin yawn jama' da suke da shi - sannan da kwararar 'yan Rasha da Ukraine tun bayan fara yakin.
To, idan aka yi duba ga sha'anin tsaro da siyasa, Turkiyya da Georgia na da hadin kai babba da kuma kakkarfar huldar diplomasiyya.
A yayin gwamnatin Jam'iyyar Georgia Drea, ta sake mayar da hankali kan sauye-sauye a kasar da sake gina tattalin arzikinta, Turkiyya za ta ci gaba da zama kawarta kuma madogararta sama da Tarayyar Turai da Amurka.
Marubuci, Ian Proud tsohon jami'in diflomasiyyar Birtaniya ne kuma marubucin littafin 'A Misfit Moscow: How British Diplomacy in Russia Failed.'
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.