Labarin mutuwar Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka Henry Kissinger a ranar Laraba ya janyo kalamai da mayar da martani da dama.
A matakin kasa da kasa, Kissinger ya yi shuhura da zama a kan gaba na masu goyon bayan juyin mulki ga shugaban kasar Chile Salvador Allende a 1973 - amma kuma ya jagoranci manyan manufofin Amurka a lokacin rabuwa da mulkin mallaka, a kasashen da Portugal ta raina a Afirka.
Manufar Kissinger ita ce bunkasa karfin Amurka kan ikon kasashen Afirka.
Shi ne babban jami'in Amurka na farko da ya ziyarci Afirka ta Kudu da ke fama da nuna wariya a tsawon shekaru 30, a lokacin da yake matsayin Ministan Harkokin Waje inda ya gana da Firimiya John Vorster a 1976.
Kamar yadda jaridar New York Times ta rawaito, 'yan sandan Afirka ta Kudu sun kashe dalibai bakaken fata bakwai a zanga-zangar da ta biyo baya.
Wannan wani bangare ne na salon murkushe kudancin Afirka da ke fuskantar shugabancin fararen fata da tsoron kwamunisanci da asarar rayuka.
A lokacin ziyarar ta 1976, Kissinger ya shiga tsakani don bai wa fararen fata tsiraru nasarar diflomasiyya, kuma ya zama abokin ƙut da ƙut na Ian Smith -- shugaban gwamnatin farar fata ta UDI a Rhodesia.
Jerin nasarori hamsin na Kissinger ya yadu sosai da samun makaranta da dama bayan shekaru hamsin.
A wata wasika ga shugaban Amurka Nixon a 1970 ya bayyana Congo a matsayin "daya daga nasarorinmu a Afirka" -- an yi kisan gilla ga Shugaba Lumumba watakila da taimakon CIA a 1961 -- kuma Shugaba Mobutu Sese Seko na kokarin hada kan jama'ar Congo." Ya yi ganawa da dama da Mobutu.
Sai dai kuma, babban tasirin da Kissinger ya yi a nahiyar Afirka ya samu ne ta hanyar ganin kasashen da Portugal ta yi wa mulkin mallaka sun samu 'yancin kai.
A yayin da ya zuwa 1960 dukkan kasashen da Ingila, Faransa da Belgium suka yi wa mulkin mallaka suka samu 'yancin kai, amma Portugal da a lokacin take karkashin jagorancin Salazar - ta yi gwagwarmayar hana kasashen 'yanci a wani bangare na burinta na ci gaba da zama mai karfi."
Tabbas talakawa da jahilai da dama na Portugal sun ci gaba da yin kaura zuwa Angola a shekarun 1960.
Kafin zama Sakataren Harkokin Waje na Gerald Ford, Kissinger ya kasance mai bayar da shawara kan sha'anin tsaro na kasa ga Shugaba Nixon.
Ya zama Sakataren Majalisar Tsaron Kasa wadda ta fitar da rahoto kan Afirka a ranar 10 ga Afrilu 1969.
Wannan ya bayar da cikakken goyon baya ga mulkin mallakar Portugal, maimakon a samar da yanayin 'yantar da kasashen kuma sai aka fara yakin kwatar 'yancin kai a Angola, Guinea-Bissau da Mozambique.
Firaministan Portugal Marcello Caetano na gwamnatin Estado Novo (daga baya ya zama ministan kasashen da ake wa mulkin mallaka) ya yi nuni da cewa an biya Amurka ta hanyar ba ta damar amfani da sansanin soji na Azores a Tekun Atlantika.
Ya zuwa farkon 1970, ta bayyana karara cewa yaki da Portugal ke yi da kasashen da take wa mulkin mallaka ba zai yi nasara ba.
Lamarin ya zama mummuna ga dakarun Portugal a Guinea-Bissau wanda ya janyo Boren Carnation a Portugal a ranar 25 ga Afrilun 1974, wanda sojojin da suka dawo daga yakin Afirka suka gudanar.
Duk da haka, Kissinger ya ci gaba da kaawance da gwamnatin Portugal, kuma Wasikar Ma'aikatar Harkokin Waje da aka fitar bayan taron watan Yulin 1974 ta rawaito shi na cewa Amurka ba za ta amince da Guinea-Bissau ta shiga MDD ba sai Portugal ta amince da hakan.
Wannan ne ya share fagen mummunan shiga tsakanin da Kissinger ya yi, wanda ya zo a Angola.
A lokacin da dakarun kama guri zauna da mulkin mallaka na Portugal suka bar Angola a karshen 1974 da farkon 1975, sai aka fara yakin basasa.
Duk da cewa kwaminisawan MPLA na kan ganiya, Kissinger ya shiga tsakani tare da goyon bayan kokarin Afirka ta Kudu na baiwa 'yan adawa makamai a kudanci - musamman 'yan UNITA.
Kamar yadda masanin tarihi Piero Gleiejeses ya rubuta a sakonsa game da Kissinger, wannan abu ne da ya kusa ya janyo rikicin zubar da jini da yakin basasa a Afirka bayan mulkin mullaka.
Ya zuwa Oktoban 1975, shiga tsakanin Amurka da Afirka ta Kudu ya hana afkuwar yakin basasar.
Kungiyar UNITA ta yi tattaki a babban birnin Luanda. Amma a wannan mataki, Kissinger ya makance tare da bin bangare daya ta hanyar shigar da dubunnan sojojin Cuba da Fidel Castro ya aiko daga Havana a karkashin Farmakan Carlota: mayakan na Cuba sun hana afkuwar yakin inda suka taimaka wajen wanzuwar gwamnatin MPLA a Luanda.
Duk da haka, shiga tsakanin da Kissinger ya yi ya zamarwa Angola babban bala'i. An ci gaba da yakin basasa har bayan shekaru 30 lokacin da UNITA ta amince da an yi galaba a kanta, a 2002.
Ya zuwa wannan lokaci, an kashe 'yan kasar Angola tsakanin 500,000 da 800,000 inda aka raba sama da miliyan daya da matsugunansu.
Ƙawancen Afirka ta Kudu da Amurka ya ci gaba har zuwa yakin Culto Cuanavale a 1988, sun yaƙi dakarun Cuba da suka kasance a Angola tun bayan shiga tsakanin Kissinger.
Sakamakon mutuwar Kissinger, daya daga cikin wutar rikici da bala'in da ya biyo bayan samun 'yancin kasashen Afirka ya shiga tarihi.
A yanzu za mu iya nazari kan Yakin Cacar Baki a Afirka, da yadda Amurka ta yi kokarin tabbatar da tsarin tafiyar da tattalin arzikin kasashen don sace albarkatun da suke da su.
Akidar nuna wariya karara ta Kissinger, da goyon bayan 'yan nuna wariya irin su Mobutu da suka taimakawa Amurka wajen cimma burinta na tattalin arziki.
Wannan lokaci ne na fahimtar yanayin tattalin arziki da siyasar nahiyar, kuma dole a tsaya a fayyace tasirin da manufofinsa suka yi a nahiyar.
Marubuci, Toby Green, farfesa ne na Tarihin Afirka Kafin Mulkin Mallaka da Al'adu a Kings College da ke Landan.
Togaciya: Ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya zo daidaida ra’ayi ko ka’idojin aikin jaridar TRT Afrika.