Yunkurin kasar Gambiya a shekarar 2019 da kuma bajintar da Afirka ta Kudu ta nuna a shekarar 2024 kan batun Myanmar da Isra'ila, zuwa ga kotun duniya ta Majalisar Dinkin Duniya (ICJ) kan take hakkin ɗan Adam da yiwuwar kisan kare dangi, ya haskaka nahiyar Afirka a idon duniya.
Da farko dai batun shari'ar da Gambiya ta gabatar bai wani dauki hankali duniya ba, amma makamancin lamarin ya sake kunno kai bayan da Afirka ta Kudu ta bayyana irin ta'asar da Isra'ila ke yi a Gaza.
Daga baya ne kasashen Afrika 52 suka hada kai da Afirka ta Kudu, akasari kasashen yankin kudancin duniya ne, inda suka bayyana damuwarsu game da rashin adalci da take hakkin Falasdinawa da ake yi karkashin mulkin mallaka na Isra'ila.
Yayin da kashe-kashe da lalata ababen more rayuwa da Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza, Afirka a matsayinta na nahiyar da masu tsara manufofin yammacin Turai da manyan kafafen yada labarai na duniya suka yi watsi da ita, ta matukar kebe kanta.
Bayan matakin kotun ICJ, shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya shaidawa kungiyar Tarayyar Afirka a kwanan baya cewa nahiyar Afirka ita ce mabudin hadin kai da ci gaban kasashen kudancin duniya.
Wannan kyakkyawar fata ce da wani da ke sa ido wanda ya fito daga wajen Afirka ya bayyana.
Tabbas, Afirka na da albarkar karuwar yawan al'ummarta yayin da sauran kasashen duniya ke yin kwangila. Amma dole sai kasashen Afirka sun fara gyara tare da adaidaita kansu.
Afirka a matsayinta na nahiya na bukatar shawo kan matsalar siyasa da yakin basasa da kuma cimma turbar ci gaba mai dorewa a fannin tattalin arziki da muhalli kafin ta iya zama nahiyar da za ta jagoranci yankin Kudancin Duniya.
Ƙarfin tattalin arziki
A mafi yawan lokuta, kyakkyawan fata game da makomar Afirka yana dogara ne akan wasu dalilai na zamantakewa da tattalin arziki da kuma "bazirar ɗan adam."
Manyan ƴan kasuwa a duniya da kuma ƴan jari-hujja sun kwadaitu da hasashe karuwar yawan jama'ar Afirka, inda tunaninsu ya fi karkata kan kasuwanni da riba.
A halin yanzu kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya kamar China da Indiya, har ma da Turai da Amurka, suna kallon Afirka a matsayin tushen samun ayyuka masu arha da albarkatun kasa.
Masu tsara manufofi da masu sa ido suna mai da hankali ne kan yawan jama'a da kuma albarkar kasuwanni a duniyar jari hujja.
A yanzu haka, jimlar yawan jama'ar nahiyar Afirka ya kai mutane biliyan 1.4 , kusan kashi 18 cikin 100 na al'ummar duniya da kuma hasashen samun karin kashi hudu cikin 100 a shekarar 2024.
Nan da shekarar 2050, ana sa ran al'ummar nahiyar Afirka za ta karu zuwa mutane biliyan 2.4, kuma za ta kai sama da kashi daya bisa hudu na yawan al'ummar duniya.
Idan muka duba hakan a ƙasa da shekaru talatin, idan aka cire annoba da yunwa ko rikice-rikice da yaƙe-yaƙe na cikin gida daga ciki za.
Nan da shekara ta 2100, an yi hasashen yawan al'ummar Afirka za su kai biliyan 4.2, baya ga hasashen yawan al'ummar Asiya da aka yi kan mutanen yankin zai kai biliyan 4.8.
Akwai fa'idoji da dama a yankunan da ke da yawan jama'a kamar na bambancin al'adu da haɓakar tattalin arziki da kuma ƙari a yawan buƙatun kayayyaki da ayyuka.
Ana dada mai da hankali kan tattalin arzikin kudaden shiga (GDP) na kayayyakin cikin gida na kowanne mutum da ke yankin kudu da hamadar Saharar Afrika, wanda ya samu ci gaba sosai a cikin shekaru biyar da suka wuce.
Adadin yana bai wa masana tattalin arziki da masu tsara manufofi kwarin gwiwa, Toh a zahiri mai hakan ke nufi?
Yanayin siyasa da rashin zaman lafiya
Yayin da hasashen alkaluman suka yi nuni zuwa ga kyakkyawar makomar Afirka, sai dai wasu alamomi sun ba da dalilin samun tsaiko.
A cikin tsawon shekaru goma da aka kwashe ana yakin basasa da rikice-rikicen yankuna sun yi sanadin raba mutane sama da miliyan 40 da muhallansu a nahiyar.
Kimanin mutane miliyan 5.4 ne suka mutu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango tun daga shekara ta 1998 sakamakon rikici da wasu abubuwa da har yanzu ba a kai ga magance su ba.
Sudan, wacce ta taba zama ''kwandon aije burodi'' a Afirka kana kasa mafi girma a nahiyar kafin rabuwarta a shekarar 2011, ta sha fama da rashin kwanciyar hankali da yakin basasa.
Ya zuwa watan Janairun 202, an kiyasta cewa an kashe mutane 13,000 zuwa 15,000 akewayen babban birinin kasar da kuma yankin Darfur.
Masana sun yi gargadin cewa kasar na cikin mumunan hadari. Tuni mutane miliyan 5.9 suka rasa matsugunansu sannan mutane miliyan 1.4 sun yi gudun hijira don neman mafaka .
Kazalika, wasu utane miliyan 25 ''suna matukar bukatar agajin jin kai, inda suke fuskantar matsalar abinci da kuma hadarin yunwa," in ji Alex de Waal, Babban Darakta na Gidauniyar Zaman Lafiya ta Duniya.
Yayin da duniya ta fusata da kisan gillar da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza, ita ma Sudan na bukatar kulawar gaggawa.
Ana fama da tarin wasu rikice-rikice a yankin yammacin Sahara da Sudan ta Kudu,da Somaliya daMozambique, da kuma Chadi wadanda su ma suke bukatar kulawa cikin gaggawa daga shugabannin kasashen Afirka.
Baya ga yaki, muradun kasashen waje ga arzikin ma'adinai na nahiyar suna karkatar da dimbin albarkatun da al'ummar Afirka ke bukata zuwa ga asusun sirri masu zaman kansu da na waje.
A manyan Tafkunan Afirka, yawancin tashe-tashen hankula da ake fama da su sun ta'allaka ne kan albarkatun ma'adinai da galibi ya shafi ƙasashe 10.
Rikicin tsakanin kasa da kasa da ake ci gaba da fama da shi, da kuma amfani da sojojin haya na nahiyar da na waje, da kuma cinikin albarkatun ƙasa don musaya da makamai na tattare da keta haƙƙin ɗan adam, batun da ke buƙatar a gaggauta gyara su.
Iftila'i na sauyin yanayi ma babbar barazana ne ga Afirka. Batun yana tsakanin sauran ƙalubale da dama da nahiyar ke fama da su - ci gaba da talauci da ruwa da ambaliya da kuma rikice-rikicen siyasa - haɗin kai kawai suke buƙata wajen kara lalata muhalli.
Yawan karuwar al'ummar Afirka yana kara habaka birane cikin sauri, yayin da ake samun karin sabbin birane, ana ɗaɗa hasashen samun munanan barazana ga muhalli.
Tsaro da jin daɗin ɗan adam za su kasance cikin haɗari mai girma idan ba a mai da hankali wajen gaggauta magance waɗannan abubuwa ba.
Farfadowar Afirka
Don gina kyakkyawan fatan shugaba Lula, babban abun da za a ba fifiko shine rage barazanar bala'o'in da mutane ke haddasawa a nahiyar, musamman na muhalli.
Yin hakan zai bukaci karfin hadin gwiwar jama'ar Afirka da kuma rage dogaro da kasashen waje, wanda zai haifar da ci gaban dan Adam mai dorewa da ci gaban da ya dace ga bukatun nahiyar.
An dade da kudurin sake farfado da Afirka, sai dai farfadowar ba abu bane na lokaci daya, ya ta'allaka ne wajen tattara karfi da albarkatu tare da sakamako masu fa'ida da canji.
Gyara kurakuran da aka samu tare da amfani da damammakin da ake da su oza su taimaka wajen samar da ci gaban da al'ummomin Afirka suke bukata.
Rage dogaro daga waje zai ba da dama ga ƙasashen Afirka su ba da fifikon ga bukatun kansu.
Sannan akwai bukatar kasashe su fi ba da fifiko kan bukatunsu na cikin gida fiye da bukatun manyan masarautun duniya, kuma ta yin hakan, za su iya tinkarar ka'idojin kudi na duniya.
Kazalika ana bukatar da a bada fifiko wajen inganta cibiyoyin da za su hada kan Afirka.
Mbeki ya soki tsarin mulki a yankin kudu da hamadar sahara. Ya yi nuni kan yadda ake samun shugabanin Afirka da ke wawasar arzikin kasashensu, mafi akasari waɗanda suka fifita amfanin kansu ko ta halin kaka a matsayin babbar matsala da ta cancanci gyara.
Shugabanci na gari zai farfado da yanayin tattalin arziki mai dorewa, hadi da kwanciyar hankali da gaskiya a siyasa, shawara Mbeki zai bai wa jama'ar nahiyar Afirka damar su ba da gudummawa ga wayewar ɗan adam sannan su kasance masu cin gajiyar waɗannan nasarorin kamar yadda Diop ya yi hasashe.
An gudanar da tsarin jari-hujja a duk faɗin nahiyar ba tare da la'akari da wasu ƙananan hanyoyi ba.
Akwai bukatar a kara wayar da kan jama'a don halkinta nahiyar wa al'ummar da za su zo a gaba, tare da samar da damammaki na ci gaban ɗan 'adama da ake bukata don makoma mai ɗorewa.
Da farko dai dole sake farfadowar Afirka ya kawo canji ga mazauna nahiyar sannan wa duniya. Arzikin nahiyar ya ta'allaka kan al'ummominta daban-daban da harsuna da al'adu da addini da ayyukanta.
Marubuci ɗan Nijeriya Chinua Achebe ya yi nuni da hakan ta hanyar rubuce-rubucensa a lokacin da yake kara bayyana bukatar rikewa da kuma kula da "tsohuwar kimar nahiyar "inda ya ce kada a rasa komai ga tsarin zamani da kuma son rai.
Idan makomar Afirka za ta iya adana labarun tarihinta masu ƙima da mutunci, zurfin hange da sarkakiyar hasashen da ke tattare da al'adunta maban-banta.
A shekaru goma da suka wuce, aƙalla al'ummomin Afirka biyu sun ba da fifiko ga mutunta ƙimar ɗan'adam - muhimmin koyarwar ɗabi'ar al'adu da addini da kuma tatsuniyoyin Afirka - don zaburar da duniya wajen kiyaye mutunci da adalci a Gaza da sauran wurare.
Fiye da kowane lokaci, nahiyar Afirka na buƙatar waɗannan kyaututtukan don haɓaka makomarta mai dorewa.
Marubucin, Ebrahim Moosa,Farfesa ne kan ilimin Musulunci da Al'ummomin Musulmi a Makarantar Keogh na Harkokin Duniya, a Jami'ar Notre Dame da ke jihar Indiana, Amurka.
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.