Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa na buga tambari a jikin takardun farko na jigilar kaya a karon farko karkashin Yarjejeniyar AfCFTA a tahsar jiragen ruwa ta Durban. / Hoto: Reuters

Daga Patrick Wanjohi

Afirka a yau, na bukatar bude dukkan iyakokinta ga juna domin habakar tattalin arziki da kasuwancin Afirka.

Iyakokin kasashe na kawo nakasu ga cigaban tattalin arziki. Yanayin kasuwanci na ci gaba da gamuwa d abiyan haraji da kudade don isa ga wasu yankunan da ke wajen kasashensu.

Kuma ba shi da ma'ana a ce dan Afirka ya biya kudi ya karbi Visa don zuwa wata kasar a nahiyar.

Dadin dadawa, wannan tunani da sabon tsari zai amfani 'yan Afirka da yawa matukar aka yi amfani da shi.

Tsohon Shugaban Kasar Ghana Kwame Nkrumah, a wani rubutu da ya yi a 1968 mai taken "Me ya sa dole Afirka ta Hade Waje Guda", ya ce "Idan muka bari aka rarraba kawunanmu, to za a sake yi mana mulkin mallaka, sannan a dinga yi mana dauki daya-daya."

Idan aka kalli batun karara, rushe iyakoki ta fuskar kasuwanci abu ne mai kyau kuma ingantacce a siyasa, amma a hakikanin gaskiya yana da wahalar aiwatarwa. Yau, akwai hanyoyi daban-daban na lallaba gwamnatoci don tabbatar da wannan manufa.

Tambayar a nan ita ce, ta yaya dukkan kasashen Afirka za su bude wa juna iyakokinsu ga kasuwanci ba tare da illata tattalin arzikinsu na cikin gida ba, tare da kuma tabbatar da tsaron cikin gida da amfanin al'ummarsu ga tsarin?

Tarayyar Afirka ta ce mafi ga wanna ta dogara ne kan Yarjejeniyar Kasuwanci Ba Tsaiko Tsakanin Kasashen Afirka (AfCFTA). Ana ci gaba da ayyukan tabbatar da aiki da wannan yarjejeniya.

Hadewar yankuna

A takaice, yarjejeniyar AfCTA na son kawo sauyi ga Afirka don mayar da ita kasuwa mai 'yanci ga kasuwancin kayayyaki da gudanar da ayyuka.

'Yan Afirka sama da biliyan 1.3 za su sayo da dayar da kayayyaki ba tare da wani shinge ba, kuma su amfana da kasuwar da ke da jarin sama da dala biliyan 3.4. Wannan tunani da aka fara kawo wa a watan Mayu, 2019, na son amfana da dibin jama'a don habaka kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka.

Idan aka aiwatar da yarjejeniyar sosai, hakan zai zama babban matakin samar da Afirka marar iyakoki ta fuskar tattlin arziki.

Daya daga cikin abubuwan da AfCTA ta kawo shi ne a cire harajin kasuwanci da kayayyaki tsakanin kasashen nahiyar. Har yanzu ba a aiwatar da yarjejeniyar baki daya ba a kasashen Afirka da yawa.

Duk da wannan kalubale, akwai nasarori da ake gani, wadanda ke nuni karara ga kyawu da amfanin wannan yarjejeniyar ga kasuwancin Afirka.

Andrew Mold, Shugaban AfCFTA a HukumarTattalin Arziki na Majalisar Dinkin Duniya a Afirka da ke ofishin Gabashin Afirka, ya bayyana cewa bincika ya yi nuni da yadda bangarori irin su aikin noma, samar da kayayyaki da ayyuka ke habaka sosai.

"Ayyukan gwaji da UNECA ke yi sun ce akwai karin kasuwanci da kashi 35-36 a kasuwanci tskaanin kasashen nahiyar, amma idan ka kalli bangaren samar da abinci da noma, misali, za ka ga karin da aka samu ya kai kusan kashi 50, na ayyuka kuma ya kai kashi 40, idan har aka tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar baki daya," in ji Dr Mold.

Wannan babban labari ne, musamman idan har kana ayyuka a bangaren noma. Bangaren noma a Afirka na bayar da kashi 15 na kudaden da nahiyar ke samu a cikin gida, wanda ya kai dala biliyan 100.

Labari mai dadi a nan shi ne ida kasarku da makotanta suka sassauta ka'idojin kasuwanci, irin su janye harajin shigo da kayayyaki da haramcin fita da su, tare da kuma rage kudaden da ake kashwa wajen samar da kayayyaki, hakan na nufin za a kashe kudi kadan a samu riba da yawa, da samun damar fadada masana'anta da daukar nkarin ma'aikata.

Ba iya bangaren noma kawai ba, har ma a dukkan sauran fannoni haka abin yake.

Cudanya mai ma'ana

Tarayyar Afrika ta cenasarar AfCFTA ta dogara ne kacokan kan yadda mutane za su dinka kai komo ba tare da tsaiko ba.

Alkalumanta sun bayyana cewa a yayinda mambobin Tarayyar 32 suka sanya hannu kan yarjejeniyar shige da fice ba tare da takura ba, kasashe hudu daga ciki ne kawai suka fara aiki da ita. Wannan na koma wa ga aniyar siyasa ta shugabannin Afirka.

Cigaban kasuwancinku na bukatar motsi ba takura, tallata hajojinku, neman damarmaki, haduwa da ganawa da mutanen da ba ku sani ba. Cigaba sosai na bangaren yawon bude ido zai samu fifiko sosai.

Kungiyar hadin Kan Kasashen Gabashin Afirka, misali, sun yi nisa a wannan bangaren. Dan kasar kenya zai iya shiga Uganda da katin shaidar zama dan kasa kawai, haka ma dan Uganda zai iya shiga Kenya. Babu bukatar Visa.

Kenya ma ta kara daukar wani babban mataki mai kyau na janye Visa da dukkan 'yan kasashe da ke son zuwa kasar, kawai mutum zai nemi izini ne ta yanar gizo kafin ya taso ya taho, sannan ya biya kudi sai ya shiga kasar.

Sai dai kuma, har yanzu ta cire wasu kasashen Afirka daga daga biyan kudade a wannan tsari nata na ETA, saboda kasashen sun sanya hannu da Kenya kan janye wa juna visa da biyan kudi tuntuni. Kasashen sun hada da Comoros, Afirka ta Kudu, Ethiopia, Congo, Eritrea da Mozambique.

Aiki da kyakkyawar niyya zai iya habaka sashen yawon bude ido idan aka amince da ita a nahiyar. Tun da yawon bude ido na daga fannoni biyar da AfCTA ta baiwa fifiko, kwararru na da ra'ayin cewa yawon bude ido zai taimaka wajen hadewar yankuna da habaka kasuwanci.

Geoffrey Manyara, Babban Jami'in Tattalin Arziki na UN ECA, sashen SRO-EA a Afirka, ya ce bincikensu ya nuna cewa akwai alaka sosai tsakanin yawon bude ido da kasuwanci.

"Yawon bude ido ne ke janyo kasuwanci, bari a ba ku misali, shi ne daya daga cikin masu fitar da kaya da ya zo Rwanda a wani lokaci a baya a matsayin 'yan yawon bude ido, amma ya gano akwai dama a wannan bangaren, kuma yana kan gaba wajen fitar da kaya," in ji Manyara.

Wata hanya da tattalin arziki zai iya saukaka wannan shi ne Sararin Samaniya Mara Takura. Kamfanonin Jiragen Saman Afirka irin su Kenya Airways, Ethiopian Airlines da RwandaAir, na iya hada kai waje guda maimakon yin gogayya baki daya. Wannan na nufin sauaka kudaden da ake cajar kamfanonin da na jiragen dakon kaya a tsakanin kasashen nahiyar.

Kasuwar Sufurin Jiragen Sama Tilo ta Afirka (SAATM), ginshiki wajen hadewar kasuwancin nahiyar waje guda, kuma an kaddamar da ita a taron Tarayyar Afirka na watan Janairun 2018.

Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki Mahamat, ya ce sararin samaniya kyau zai kai ga karin jiragen sama da hade yankuna waje gida tsakanin biranen Afirka daban-daban, ba wai manyan biranen kasashen kawai ba.

Dadin dadawa, za a samu raguwar kudin tikiti da rage awannin tafiya, madalla ga janye zama da ajje fasinjoji a filayen jiragen saman nahiyar.

Sama da kasashen Afirka 30 ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar amma aiwatar da ita ne ya zama kalubale.

Kudin bai daya

Sakamakon yawaitar nau'in kudade a nahiyar, sai dalar Amurka ta zama kudin bai daya a kasuwancin Afirka. Idan kasarka ta asali na iya hada kai da wata kasar don samar da kudin bai daya a Afirka da za a yi amfani da su wajen kasuwanci, kudin kasuwanci zai yi sauki.

Hakan zai saukaka kasuwanci, mutumin Masar zai samu saukin kasuwanci da dan Afirka ta Kudu kon kasar Burundi da zai yi kasuwanci da dan Loiberia ba tare da damuwa kan kudin kasar waje ba.

Kazalika, dole ne ku habaka fasahar sadarwarku, kamar idan kana son nasara a kasuwancinka. Saboda haka, nahiyar na bukatar yare guda daya. Ko Swahili, Hausa ko Yoruba, dole ne mu amince da yare da daya da za mu dinga gudanar da kasuwanci da shi.

A yanzu kuna da dukkan abubuwan da za ku habaka kamfanoninku nan da 2063 da Afirka ke byurin cimma manufarta. Ana bukatar rushe iyakoki da shingayen tattalin arziki, yarjejeniyar AfCFTA ta tanadi hakan karara, amma gwamnatinku ce za ta yi aikin samar a kasuwa guda.

Sakatariyar AfCFTA, ta bayyana cewa kasashen Afirka 54 sun sanya hannu kan yarjejeniya, kuma 48 sun saka hannun fara aiki.

Idan aka zartar da ita yadda ya kamata, Tarayyar Afirka ta ce za a cire mutane miliyan 30 daga tsananin talauci, sannan dan kasuwa kuma zai samu amfani sosai.

Yanzu ne lokacin daukar mataki. Kamar yadda Kwame Nkrumah ya bayyana a rubutunsa "Mu a Afirka ba za mu iya jira ba; kar mu jira har lokacin da gazawarmu ta mamaye sannan muka kasa amfana da wannan dama."

Marubuci, Patrick Wanjohi, kwararre ne kan sadarwa da ke da Cibiyar Habaka Ayyuka ta Afirka, Babbar Cibiyar Afirka ta cigaban ayyuka da kasashen Tarayyar Afirka suke mara wa baya da daukar nauyi.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zo daidai da ra'ayi, fahimta da kuma manufofin editan TRT Afrika ba.

TRT Afrika