Joseph Boakai ya taba rike mukamin mataimakin shugaban kasa na tsawon shekaru 12 / Photo: Reuters  

Daga Henry Karmo

An rantsar da Ambasada Joseph Nyumah- Boakai a ranar 22 ga watan Janairun 2024 a matsayin shugaban kasar Laberiya na 25 bayan nasarar da ya samu a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Oktoba, inda ya kayar da shugaba mai ci George Weah da tazarar kuri'u sama da dubu ashirin.

Shugaban kasar mai barin gado George Weah ya samu yabo daga bangarorin siyasa na ciki gida da wajen kasar, saboda rawar da ya taka wajen rungumar kaddara ta nasarar da abokin hamayyarsa a takarar shugabancin kasar ya samu.

Ya amince da hakan ne kwanaki uku gabanin sanarwar nasarar a hukumance daga hukumar zabe ta kasar NEC ta fitar.

Wayar tarhon da shugaban mai shekaru 57 ya yi wa Joseph Boakai na taya shi murna kwanaki kadan kafin sanarwar hukumar zaben kasar a hukumance ya kubutar da kasar daga fadawa tashin hankali - da aka dade ana fama da rikicin siyasa.

A matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa na tsawon shekaru 12, ya yi aiki tare da Madam Ellen Johnson Sirleaf, mace ta farko wacce ta shugabanci Laberiya kana ta dawo da kasar kan turba bayan fama da rikice-rikice na tsawon shekaru 14.

Sun yi haka ne ta hanyar sake fasalin kasar ta fuskar shugabanci na gari wanda ya kai ga kafa cibiyoyin yaki da cin hanci da rashawa da albanzaranci a cikin gwamnati.

A shekaru shida, masu sukar gwamnatin George Weah sun yi zargin cewa gwamnatinsa ta lalata wasu kyawawan tsare-tsare da gwamnatin da ya gada ta kafa ta hanyar soke wa'adin mulki daga hukumomin da ya kamata su kasance masu cin gashin kansu.

Kalubalen da ke gaban Boakai

Sabon shugaban kasar da aka rantsar, Joseph Boakai, ya karbi ragamar mulkin kasar ne a daidai lokacin da al'ummar Laberiya ke matukar bukatar ci gaba da kyautatuwar rayuwa.

Tun bayan zabensa, 'yan kasar suke ta kiraye-kiraye a kafafen yada labarai na cikin gida don neman sabuwar gwamnati kasar ta tabbatar ta yi bincike tare da tattance lalitar da gwamnatin mai barin gado ta bari.

Ta hanyar yin hakan ba tare da nuna shi a matsayin kokarin farauta ba, da kuma rage yawan ayyukan ma'aikata da gwamnatin Weah ta rubanya zai taimaka wajen sanya kwarin gwiwar jama’a kan matsayar Boakai na yaki da cin hanci da rashawa da almubazzaranci a gwamnati.

Kazalika sai Shugaba Boakai ya kara azama wajen aiki kan kalubalen da ke tattare da samar da kudi mai yawa na biyan albashin ma'aikata.

A Lokacin da Shugaba Weah ya karbi mulki a shekarar 2018, kudaden albashin gwamnati ya kai dalar Amurka miliyan 297. A shekaru shida ya karu zuwa dala miliyan 304.

Sabon shugaban na bukatar ya mayar da hankali wajen yin duba kan dabarun daidaita albashi da gwamnati George Weah ta yi wanda ya rage mafi karancin albashin da ma' aikatan gwamnati ke karba da kuma zargin bata tsarin biyan albashin ma’aikatu da hukumomin gwamnati domin sama wa ‘yan banga da magoya bayansu gurbi a cikin gwamnati.

Gudanar da kasafin kudi

A yayin da ya karbar ragamar mulki, ya gaji daftarin kasafin kudi na miliyan dari shida da ashirin da biyar, kwatankwacin dalar Amurka dubu hamsin da bakwai (625,57,000).

Kasafin kudaden da ake son kashewa na cikin gida ya kai dalar Amurka miliyan 594.54, kwatankwacin kashi 95 cikin 100, yayin da aka yi hasashen jimillar kudaden da ake kashewa na sassan gwamnati zai kai dalar Amurka 31.03, ko kuma kashi 5 na jimillar kudaden da ake shirin kashewa.

A cikin daftarin kasafin kudin, albarkatun da ake da su suna mayar da hankali kan kashe kudi na wajibi na adadin adadin dalar Amurka miliyan 594.54 da aka ware.

An ware kudaden da ake kashewa akai-akai kuma an tsara su ta hanyar fifiko kamar haka: Ayyukan bashi (Na cikin gida da na waje), Biyan kuɗi ga ma'aikata, Tallafi, Kayayyaki da sabis na Bangaren Ilimi da Lafiya da sauransu. A cewar ma'aikatar kudi ta kasar.

Ya yi daidai da sashe na 17.1 na Dokar Kula da Kudaden Jama'a ta Laberiya. A dokar, kasafin a matsayinsa na kudaden aiki, ya kamata majalisa ta yi bincike a kai, a farko makon nan ne aka mika kasafin kudin ga majalisar.

Baya ga kudin biyan karatu

Da irin wannan kasafin kudin, shugaba Boakai zai soma ne da aikin tunkarar kalubalen da ake fuskanta a fannin kiwon lafiya ta hanyar tabbatar da cewa asibitoci a fadin kasar suna aiki da kuma samar da magunguna ga marasa lafiya da ke neman magani.

Domin tabbatar da hakan, yana bukatar ya magance jin dadin ma’aikatan jinya da likitoci ta hanyar biyan alawus da albashi musamman a yankunan karkara.

A fannin ilimi, yana bukatar ya zarce kudaden da George Weah ke biya na samun damar yin karatu a jami'o'in gwamnati a kyauta da kuma biyan kudade zana jarabawar Afirka ta yamma WAEC wa daliban aji 12.

Yana bukatar ya tabbatar da cewa an biya malamai albashi mai tsoka domin su ci gaba da koyarwa a kai a kai.

Samar da ingantaccen ilimi ya kasance babban kalubale, a tsawon shekaru ba a baiwa bangaren kulawa sosai ba idan aka yi la’akari da yadda ake yi wa malamai da shugabannin makarantu musamman a makarantun gwamnati.

Dalibai musamman wadanda ke halartar makarantun gwamnati sun gudanar da zanga-zangar neman gwamnati ta biya malaman da suke yajin aiki albashi domin a koma karatu.

A wasu lokuta, makarantu har yanzu ba su da wuraren zama ko kayan aikin. Idan shugaba Boakai zai inganta fannin, yana bukatar ya mai da hankali ga kananan abubuwa da ke da muhimmanci.

Tsarin kasashen waje

A shekarar farko da ya hau kan karagar mulki, Shugaba Boakai zai dora alhakin sake fasalin kasar ta hanyar shaidawa duniya cewa Laberiya ta sake shirin yin kasuwanci kuma ta daina kasuwanci kamar yadda aka saba.

Zai bukaci shawo kan masu zuba jari daga kasashen waje kan dalilin da ya sa za su zuba jari a Laberiya.

Zai bukaci tabbatar da cewa bangaren shari'a ya kasance mai cin gashin kansa ta hanyar rashin tsoma baki a cikin ayyukansa wanda zai iya ba da kwarin gwiwa ga jama'a da duniya kan dalilin da ya sa za su iya saka hannun jari a Laberiya da kuma yadda tsarin shari'a ke aiki ga kowa da kowa.

Mawallafin, Henry Karmo, dan jarida ne da ke zama a Monrovia na kasar Laberiya, yana mai da hankali ne kan labaran cikin gida da abubuwan dake faruwa. sannan marubici a mujallar Frontpage Africa.

Togaciya: Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana a wannan makala ya zama daidai da ra'ayi ko manufofin dab'i na TRT Afirka ba.

TRT Afrika