Tun bayan yakin Gaza, an dinga tuhuma da yin tambayoyi game da irin wannan cinikayya ta kayan yaƙi daga ɓangarori daban-daban har ma da gwamnatin kanta. Hoto: AFP

Daga Jonathan Kuttab

A ƙarshe dai Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC ta ba da umarnin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa Yoav Gallant kan laifukansu na yaƙi, musamman ma hana sghigar da kayan jinƙai Gaza da kuma saka mutane a cikin yunwa a matsayin makamin yaƙi.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wani muhimmin al’amari ya faru inda ‘yan majalisar dattawan Amurka da dama suka kada kuri’ar hana izinin sayar da wasu makamai da alburusai da Isra’ila ke amfani da su a Gaza.

Shekaru da yawa, babbar ƙa'ida ce ta Majalisar Dattijai da Majalisar Dokokin Amurka cewa taimakon Isra'ila lamari ne mai tsarki, al'amari na ɓangaranci, inda ba za a iya ba da wata hujja ko tattaunawa mai muni ba. Ba a la'akari da abubuwan da suka shafi kasafin kuɗi balle yin wata muhawara kan manufofin ƙasashen waje.

Wannan ya kasance gaskiya musamman a batun taimakon sojoji da sayen makamai. Sanatoci daga manyan jam’iyyun biyu, sun kasance tamkar ko dai shaho ne ko kurciya a kan ba da taimakon soja, kai tsaye sun goyi bayan sayar da kayan yaƙi ga Isra’ila.

Tun bayan yakin Gaza, an dinga tuhuma da yin tambayoyi game da irin wannan cinikayya ta kayan yaƙi daga ɓangarori daban-daban har ma da gwamnatin kanta.

Kuma umarnin da kotun ICC ta yi a baya-bayan nan na kama shugabannin Isra'ila ya kara dagula lamarin, tun da a yanzu kasashe 124 ne suke jin ya wajaba su yi aiki da wannan sammaci, lamarin da ya sa da wuya ‘yan majalisar dokokin Amurka su ci gaba da kauce wa umarnin.

Karya doka

Sanin yadda Isra'ila ke karya dokoki, gwamnatin Shugaba Joe Biden a lokuta da dama ta yi amfani da da'awar fasaha da kuma wani lokacin ƙarya don kauce wa amincewar Majalisar Dattawa na wasu nau'o'in ko adadin makamai da harsasai (tana guje wa hanyoyin taruka da aka saba a al'adance).

A cewar wasu majiyoyin na Isra’ila, Isra’ila ta yi amfani da harsasai masu yawa a cikin watan farko na yaƙin, domin tana sa ran duniya ko Amurka za su tursasa yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin makonni, wanda a zahiri hakan ya kai ga harsasanta suka ƙare, kuma ta buƙaci a kawo mata ɗauki cikin gaggawa.

Yayin da ake samun rahotannin yau da kullum na take hakin bil'adama a Gaza, da suka hada da hana abinci da ruwa da kai hare-hare a asibitoci da sauran gine-ginen fararen hula, da ma hare-haren da ake kai wa ma'aikatan agaji da kungiyoyi, wasu sun fara neman Amurka ta yi amfani da nata dokokin.

Waɗannan dokoki musamman sun haramta bayar da agajin soji idan ana amfani da irin waɗannan makaman don take haƙƙin ɗan'adam ko kuma hana samun agajin jinƙai.

A haƙiƙa, jim kaɗan gabanin zaben Amurka na Nuwamba, gwamnatin Biden ta aike da wata takarda ta musamman ga Isra'ila game da buƙatar ba da damar shigar da kayayyakin agajin Amurka, musamman ga mazauna yankunan arewacin Gaza da ke fuskantar ƙawanya tun watan Oktoba.

Wasikar ta bayyana matakan da ya kamata a dauka ciki har da adadin manyan motocin da ya kamata a ba su izinin shiga, tare da yin barazanar amfani da dokar Amurka da ta dace idan ba a dauki wadannan matakan cikin kwanaki 30 ba. Duk da haka, gwamnatin Amurka ba ta bibiya lamarin ba ta hanyar tabbatar da barazanar tata.

Dabarun yaudara

Daya daga cikin hanyoyin da Isra'ila ta guje wa hakan shi ne dagewar da take yi wajen hana 'yan jaridar ƙasashen waje samun damar shiga Gaza, sai dai idan an saka su ne a cikin tawagarsojinta, sannan kuma ta kasance ita ke faɗar yadda za su bayar da rahoton.

Wannan lamari ya hada da manufofin da ba su da ƙarfi, ta yin amfani da wasu manhajojin AI kamar "Where’s Daddy," don kai hari da kashe 'yan jarida na gida a Gaza.

Sama da ‘yan jarida 170 ne aka kashe ya zuwa yanzu, wanda ya ninka adadin ‘yan jaridan da aka kashe a wasu yankunan da ake fama da rikici a shekarun baya-bayan nan, idan aka hada su.

Dakile wadannan muryoyin ya bai wa hukumomin Isra'ila damar musanta cewa suna amfani da yunwa a matsayin makami, har ma sun bayyana cewa babu wata matsala a kasa.

A haƙiƙa, ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama da yawa sun adana bayanan ayyukan Isra'ila na kai hare-haren bama-bamai a cibiyoyin rarraba bama-bamai da lalata abubuwan da ke cikin su da kuma kashe ma'aikatan agaji.

Hujjojin da aka gabatar wa kotun ta ICC da kuma Kotun Duniya kan shari'ar da Afirka ta Kudu ta gabatar, wanda ya kai ga wani bincike na farko na kisan kare dangi ya ƙara jawo Allah wadai daga duk faɗin duniya.

Amurka na mayar da hankali

Yayin da a al'adance Amurka ba ta faye bai wa irin wadannan shari'o'i na kotunan duniya muhimmanci ba, sai dai idan abin ya shafi makiyanta, haƙiƙanin wadannan rahotanni na haifar da wani sabon yanayi inda a karon farko a tarihi aka tilasta wa majalisar dattawan yin magana kan batun magance halin da ake ciki.

Ba arashi ba ne cewa wani Sanata Bayahude (Sanata Bernie Sanders na Vermont) ne ke jagorantar wannan yunƙurin. A wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar kwanan nan, kashi 62 cikin 100 na Yahudawan Amurkawa suna goyon bayan dakatar da bai wa Isra'ila munanan makamai tare da yin amfani da su wajen matsa wa Netanyahu lamba kan tsagaita wuta da kuma yarjejeniyar sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Matsayin AIPAC, duk da haka, yawancin Amurkawa ciki har da Yahudawa suna goyon bayan hana irin wannan mummunan makamai.

Wasu Sanatoci da dama, musamman a jam’iyyar Dimokuradiyya, suna jin ta bakin ‘yan gundumominsu cewa ba za su iya yin shiru ba ko kuma sanya takunkumi ga ci gaba da samar da muggan makamai da muggan alburusai da aka yi amfani da su wajen lalata gine-ginen farar hula da kuma kai farmaki ga mutanen d aba sa dauke da makamai.

Makaman da aka kada kuri'a a kansu sun hada da harsasan tanka na mm 120, da manyan bama-bamai da JDAMs da jiragen yaƙi na F-151A.

Duk da haka, yawancin Amurkawa suna jin rashin jin daɗin sauya ra'ayi daga matsayin masu sa ido da suka yi gum da bakinsu zuwa masu hannu kai-tsaye a kisan ƙare dangin da ke gudana.

Yayin da damar samun irin wannan nasarar kada kuri'a ba ta da yawa ba tare da goyon bayan Fadar White House ba, wani lamari ne mai ban mamaki cewa har ma an yi la'akari da irin wannan kuri'a.

A karshe Sanatoci 19, kusan kashi daya bisa uku na jam'iyyar Democrat, a zahiri sun kada kuri'ar adawa da muradin Fadar White House da AIPAC na haramta sayar da wadannan makamai ga Isra'ila. An dai yi watsi da matakin, inda sama da Sanatoci 80 suka kada kuri'ar ci gaba da bai wa Isra'ila makamai.

Kuma kamar yadda aka zata, Amurka ta yi watsi da sammacin kotun ICC. To amma tun da ita ba mamba ba ce a Kotun ICC ba ne, to ba wajibi ba ne ta girmama ta. Wani abin da ya fi ɗaure kai shi ne, jami’an Amurka na barazanar sanya wa kotun kanta takunkumi, da alkalanta da masu shigar da kara domin nuna goyon baya ga rashin hukunta Isra’ila.

Marubucin maƙalar, Jonathan Kuttab lauyan Falasdinu ne, kuma mai fafutukar kare hakkin ɗan'adam. Ya girma a Urushalima, ya yi karatu a Amurka, inda ya sauke karatu daga Jami'ar Virginia Law School. Shi memba ne na Ƙungiyoyin Lauyoyin New York, Palestine da Isra'ila.

Togaciya: Ra'ayoyin da aka bayyana a nan na marubucin ne, kuma ba sa wakiltar ra'ayi, komahangar editocin TRT Afrika.

TRT World