Daga Yahya Habil
Fadar shugaban kasar Namibia a kwanan nan ta fitar da sanarwa tana watsi da abun da ta kira "Goyon bayan Jamus ga kisan kiyashin da gwamnatin Isra'ila mai nuna wariya ke yi wa fararen hula a Gaza.
Wannan na zuwa ne a lokacin da Jamus ke watsi da nuna ƙin amincewa da zargin da Isra'ila ta aikata na kisan kiyashi a Gaza da Afirka ta Kudu ta gabatar a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya.
A wani bayani da aka yada a shafin sada zumunta na X, Namibia ta tunatar da kisan kiyashin da Jamus ta yi wa jama'arta a matsayin kisan kiyashi na farko a karni na 20 (1904-1908).
Sanarwar ta ce Jamus, wadda har yanzu ba ta amince da kisan kiyashin ba, ba ta da bakin da za ta yi zance kan kisan kiyashi ga dan'adam ba.
Saboda Jamus, kamar yadda fadar shugaban kasar Namibia ta sanar, ta sha wahala kan yadda ta gaza daukar darasi daga mummunan tarihinta.
Tare da yadda Namibia ke sukar Jamus da kai Isra'ila kara kotun kasa da kasa da Afirka ta Kudu ta yi, an fara wani abu sabo ko na yayi, inda kasashen Afirka ke zama kan gaba wajen ganin an yi aiki da dokokin kasa da kasa kan laifukan yaƙi da aka yi wa bil'adama.
Mummunan hali
Tabbas, kasashen Afirka ne kashin bayan hukuncin da aka dauka a Babban Zauren Majalisar DInkin Duniya mai lamba 3379, wanda bayyana kishin kafa kasar Yahudawa a matsayin wani nau'i na nuna wariya da launin fata.
Dadin dadawa kuma a kwanan nan, Gambia ta kai ara kotun ICJ kan batun kidsn kiyshin ds ke yi jama'ar rohingya. Haka kuma, a baya0bayan nan Gambia ta kai kara kotun ta ICJ lan batun kisan kiyashi Myammar inda ake zargi na karkashe jama'ar Rohingya.
Sakamakon haka, kasashen Afirka sun cike gurbi da aka samu a tare da zama muryar dalilin da zai sanya a kawo adalci nan da nan, wanda aka rasa a baya, saboda Kasashen Yamma da ke juya duniya a yau suna ta nuna munanan halayensu ta sigogi daban-daban.
Dadin dadawa, kasashen Afirka sun jagoranci yaki da zalunci da mulkin mallaka saboda yadda 'yan mulkin mallakar suka dinga cutar da Afirka. Ana fadin 'yan Afirka ma sun san bakin mulkin mallakar da aka yi, hakan ya sanya suka "Nuna Ba Sa So" na har abada a manufofin Yamma.
Kuma idan aka zo batun Isra'ila da ayyukan kisan kiyashin da take yi ga Falasdinawan Gaza, ba arashi ba ne cewa Afirka ta Kudu ta zama wadda ta kai Isra'ila kara kotu.
Ba a daure suke ba
Wannan ya zo a daidai saboda Afirka ta Kudu na da sauran takaici na lokacin nuna wariyar launin fata a kasar, wato tsarin nuna wariya ga bakaken fata, a kasar da farare 'yan tsiraru suke shugabanta daga 1948 zuwa 1991, kuma kasa ce ta Isra'ila tun kafa ta a 1948.
Afirka ta Kudu a yau ba a daure take da igiyar muna nuna wariya ba, kuma a madadin haka, wadanda suka yaki fararen fatar ne ke shugabantar kasar, wanda a baya suke ƙawance da Isra'ila.
Dadin daɗawa, duk da ba a ambace ta a rubutun baya-bayan nan da fadar shugaban kasar Namibia ta yi ba, to Namibia ma na da irin wannan ra'ayi, saboda halin da Namibia ta taba tsintar kanta a ciki ba shi da bambanci da na Afirka ta Kudu.
Bayan haka kuma, a baya ana kiran kasar da Kudu Maso-Yammacin Afirka kuma tana karkashin gwamnatin Afirka ta Kudu har zuwa 1990.
Saboda haka, Namibia ma na da hujja sakamakon yadda ita ma ta wahaltu daga mulkin fararen fata tsiraru na Afirka ta kudu, ba wai kisan kiyashin da Jamus ta yi musu ba a farkon karni na 20, wanda aka azabtar da jama'ar Herero da Namaqua da ke Namibia.
Kamar yadda za a iya tsinkaye, al'amarin game da kisan kiyashi na kama da abin da ke faruwa a Gaza, wanda ke bai wa Namibia wani karin dalili da karfin gwiwa na kalubalantar hare-haren da Isra'ila ke kaiwa.
Sabon tsoron da Jamus ke ji
Namibia, kamar 'yar uwarta Afirka ta Kudu, na kokarin tabbatar da cewa darussan da ta koya daga mulkin mallaka ba su tafi haka kawai ba, kamar yadda yake a yau suna kare martabar Falasdinawa, suna kare manufofin duk wadanda ake zalunta.
Ba kamar Jamus da ta yi mata mulkin mallaka ba, Namibia na da ikon dauka da koyon darussa da dama daga tarihinta.
Ta hanyar halin da kasar ta shiga, Namibia ta fahimci cewa 'yancin kanta wanda ya samu bayan kisan kiyashi da mulkin mallaka na nufin ta tabbatar da ba a sake samun afkuwar wannan rashin adalci ba.
A daya gefen kuma, Jamus ba ta yi aiki da darussan cewa kar a yi kisan kiyashi ga kowa, ba wai Yahudawa kadai ba.
Maimakon haka, sai ta zama mai rufe idanuwanta ga zaluncin da Isra'ila ke yi saboda tana tsoron kar a sake bayyana ta a matsayin mai ƙyamar Yahudawa.
Wannan ba abin mamaki ba ne yadda ,manufar Jamus bayan yakin duniya na biyu ta ajje a kasar a gurbin mai nisantar nuna rikici a duniya.
Laifukan da aka yi
Saidai kuma, wani abu da kamar Jamus ba ta sani ba shi ne cewa nuna goyon baya ga Isra'ila, kamar sake dabbaka wancan hoto nata na mai goyon bayan rikici a duniya ne.
A wajen Namibia, da sauran kasashen Afirka, baya ga wannan matsayi mai girma, na kyakkyawar dabi'a, amma suna da sauran aiki a gabansu idan suna son su zama murya mai bayar da umarni da yaki da zaluntar dan adam a duniyar yau da ake ta karkashe bani adam.
Ya kamata kasashen Afirka su mayar da hankali ga laifukan da ake yi wa dan'adam a wasu wurare, musamman a cikin nahiyar, amma kuma suna zaune ba sa nuna halin ko in kula.
Sannan ne kadai Afirka za ta samun kanta a matsayin farfadowa a tarihi, sake dawo da wayewar kansu, saboda hali nagari ne tushe da mahangar habakar duk wata wayewa.
Marubuci, Yahya Habil dan jarida ne mai zaman kansa da ke Libiya, wanda ya mayar da hankali kan harkokin Afirka. Yana aiki tare da wata kungiyar bincike a Gabas ta Tsakiya.
Togaciya: Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana a wannan makala ya zama daidai da ra'ayi ko manufofin dab'i na TRT Afirka ba.