Daga Ambassador Mahboub Maalim and Nuur Mohamud Sheekh
Rikicin da ke kara ta'azzara a Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo na tunatar da cewa rikice-rikicen da aka gaza shawo kansu na iya yin tasiri kan tsaro da zaman lafiyar yankin, wanda ke da yiwuwar fadada zuwa rikici tsakanin kasashe.
Ya zama lallai Tarayyar Afirka (AU) da Hukumar Cigaba Tsakanin gwamnatoci (IGAD), a matsayin manyan masu ruwa da tsaki wajen hana rikici a yankin da samar da sulhu, su dauki darasi daga rikcin Kongo don hana afkuwar makamancinsa a Kahon Afirka.
Gaggawar amfani da diflomasiyya don kare rikci ba ta taba zama babban abu ba, a yayin da rikicin yankin ke shirin tsallaka wa cikin sauri zuwa wasu yankunan, ya lalata wajen da dama yake da rauni tare da gayyato wasu daga waje su tsoma baki tare da nuna gogayya da juna.
Kahon Afirka ya kasance daya daga cikin yankunan da ke fama da rikicin siyasa a nahiyar, inda ake ta takaddamar iyakoki, jayayya da rarrabuwar kan siyasa, da tsoma baki kan harkokin yankin daga kasashen waje wanda ke barazanar zaman lafiyarsa.
Alaka mai tsami tsakanin kasashen yankin
Muhimman batutuwa su ne rikicin Ethiopia da Eritrea, rikici tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu da aka gaza warwarewa, ciki har da matakin karshe kan Abyei, rikicin kan iyaka tsakanin Sudan-Ethiopia da aka dade ana yi kan Al Fashaga, da karin rikicin da ake samu game da amfani da Tekun Maliya a Gabar Aden,
Misali, Yarjejeniyar Abyei ta 2005, wadda ke da manufar tabbatar da matsayin yankin, har yanzu ba a samu damar wanzar da ita ba.
Kwamitin Tsaro na Majalisar DInkin Duniya ya sha nanata damuwarsa kan jinkirin da ake dauka na aiwatar da yarjejeniyar da munanan yanayin tsaro, yana mi kira ga dukkan bangarori da su yi aiki da yarjejeniyar.
Haka kuma, rikicin iyaka na Al Fashaga tsakanin Ethiopia da Sudan, yankin mai muhimmanci da dimbin albarkatun gona, ya sha janyo arangam, tare da lalata alaka tsakanin kasashe.
Kwamitin Tsaron na MDD ya bayyana wajabcin warware wadannan rikice-rikice ta hanyar tattaunawa, a yi aiki da dokokin kasa da kasa, da girmama darajar iyakokin kasashe.
Akwai bukatar mafitar diflomasiyya.
Kusurwar Afirka ya zama wani dandali na nuna hamayya tsakanin kasashe, inda manyan kasashen duniya da na yankin ke kokarin smaun karfin fada a ji a sha'anin tattalin arziki, ayyukan soji da diflomasiyya a yankin.
Tsoma hannun kasashen waje, ko ta hanyar kai makamai, samar da sansanonin soji, ko zuba jarin tattalin arziki, na yawan ta'azzara rikicin cikin gidan kasashen da rarraba kawuna.
Hatsarin rashin yin kyakkyawan nazari na da girma, a yayin da bukatun da suka saba da juna a tsakanin masu ruwa da tsaki na iya janyo babbar adawa, wanda ke sanya yunkurin diflomasiyya ya zama marar amfani gaba daya.
An tanadi Tsarin Gargadin Wuri na Tarayyar Afirka (CEWS) da Shirin Gargadin Wuri Kan Rikici na IGAD (CEWARN), don mayar da martani ga barazanar da ke zuwa kafin ta tabarbare.
Sai dai kuma, wadannan dabaru sun ga cim-ma gaci saboda karancin kudade, rashin isasshen horo, da gazawar ayyukan gwamnati.
Babban kalubale shi ne rashin haduwa waje guda da juna tsakanin bukatun kasashe, yanki da nahiya, wanda a mafi yawancin lokuta ke janyo shiga tsakani marar tasiri.
Halin ko in kula na kasashe mambobi da ke son barin yarjejeniyar tsaro na kara gurgunta kokarin AU da IGAD na daukar matakai.
Yawan karya yarjejeniyar tsagaita wuta
A yayin da Kwamitin Tarayyar Turai da IGAD sun taka rawa a yunkurin sasantwar da aka yi a baya, rashin daidaiton hukumomi ne ka yawan kawo cikas ga kokarin nasu, rashin tabbatacciyar dama, da ma rarrabuwar kai tsakanin kasashe.
Manufar daukar matakai daga kasa da ke da aniyar tantance rawar da AU da Kungiyar Tattalin Arzikin yankin ta REC, da ma IGAD, na maimaita kokarin da suke wanda ke tafiya a tutar babu.
Kuma ana daukar mataki ne bayan an samu matsala, ba wai matakan kare afkuwar ta ba.
Har ma a yanayin rikici tsakanin kasashe, Yarjejeniyar 2018 da aka sake dawo da ita kan Rikicin Sudan ta Kudu, da IGAD ta tanada, ta fuskanci kalubalen aiwatarwa, tare da yawan karya yarjejeniyar tsagaita wuta da jinkirin kawo sauye-sauyen siyasa.
Haka zalika, Yarjejeniyar Kawar da Rikicin Ballewa Daga Kasa ta Ethiopia ta 2022, da aka kulla karkashin Tarayyar Afirka, ba ta samu cikakken zama ba har yanzu, kuma na bayyana karancin wanzuwa tsare-tsaren shiga tsakani.
Yakin basasar da ake ci gaba da yi a Sudan, watakila shi ne babban misalin dusashewar karfin fada a jin Tarayyar Afirka da IGAD; duk da dimbin kokarin diflomasiyya, babu kungiyar da yi nasarar tabbatar da tsagaita wuta ko kare fararen hula daga munanan abubuwan da aka yi.
Hatsarin da kokarin bai-daya na Afirka ke fuskanta
IGAD ta yi fafutuka ajen shiga tsakanin Eritrea da Ethiopia, duk da kasancewar su biyun mambobinta ne.
Rikicin da ake ci gaba da yi tsakanin Eritrea da Djibouti, rikicin da ya bar hankulan kasashen duniya, cikakken misali ne na gibin gaza bayar da kariya ta hanyar diflomasiyya.
Ba tare da hukumomi masu karfi a fagen kasa da kasa, wadannan rikice-rikicen na fuskantar barazanar sake dawo wa da arangama da makamai.
Wajabcin ayyukan diflomasiyyar neman kawar da rikici da yanke hukunci bai taba zama wani abin gaggawa ba a Kahon Afirka.
Dole ne Tarayyar Afirka da IGAD su rabu da ragwancin hukumomi da nuna halin ko in kula na siyasa don aiki da karfinsu a matsayin manyan masu wanzar da zaman lafiya da tsaro.
Wannan na bukatar karfafa tsarin gargadin farko, inganta ayyukan shiga tsakani, da kuma jan hankulan kasashe mambobi da su yi aiki da yarjeniyoyin zaman lafiya da kawar da rikice-rikice kafin su afka wa kasashensu.
Dole ne batun nan na cewar Afirka ta warware rikice-rikicen Afirka ya zama mai aiki ba wai a baki da takarda kawai ba, dole ne a yi aiki da tsarin a aikace da kuma niyya mai kyau, ana bukatar kudade da kayan aiki don warware matsalolin tsaron yankin.
Gazawar daukar matakai cikin gaggawa, ba iyakacin yankin zai jefa hatsari ba, har ma da zaizaye kokarin bai daya na Afirka wajen sauya fasalin makomar tsaronta a duniyar da ke kara rarrabuwa.
Marubutan, Ambasada Mahboub Maalim jami'in diflomasiyyar Kenya ne kuma tsohon Sakataren Zartarwa na IGAD. Nuur Mohamed Sheekh Mai Nazarin SIyasa ne na yanki.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.