Daga Emir Hadikadunic
A tsawon shekarar da ta gabata, isra'ila na kan ƙaddamar da ƙazamin yaƙi kan Falasɗinawa, da sunan farautar Hamas da Hezbollah da wasu waɗanda ba gwamnati ba, ta hanyar jefa wa Gaza kwatankwacin bamabaman nukiliya guda shida.
A makwannin baya bayan nan, isra'ila ta kuma halaka galibin kwamandojin soji da shugabannin siyasar Hezbollah. Amma, abin da yafi ɗaga hankali shi ne, har yanzu ba a yi galaba kan Hamas ko Hezbollah ɗin ba.
Mummunan yaƙin mai rassa kuma mai bazuwa ta fuskoki da yawa a yankin Gabas Ta Tsakiya babu alamun zai ƙare, abin da ya sa da wahala a iya hasashen makomarsa.
Duk da haka, idan aka yi waiwaye, nasarorin soji na gajeren lokaci da Isra'ila ta samu suna tare da wasu muhimman rashin nasara ta fuskar dabaru.
Bari mu fara da ƙetare manufofin soji isra'ila da aka yi.
Yaƙi mara ƙarshe
A wani yanayi na yi wa kai, Gwamnatin Isra'ila da kanta ta ƙetare ginshiƙin manufofin sojinta - wato gajeren yaƙi mai tasiri.
Shekara ɗaya ana gwabza yaƙin, Isra'ila na fama da ƙiƙi-ƙaƙan dabaru, tana kokawa da yaƙi ta fuskoki da yawa da ba shi da alamar kawo ƙarshe.
Rundunar sojin ta galabaita kuma sojojin sa-kai suna jan ƙafa wajen amsa goron gayyatar yin faɗa a wannan yaƙin da bisa alama ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Ayyukan sojin ya haifar da nasarori na gajeren lokaci, da suka haɗa da kashe kwamandojin sojin Hezbollah, da raunata Hamas a Gaza da kuma samun ikon tafiyar da mahaɗar Rafah tsakanin yankin da Masar.
Amma ba su iya haifar da nasarori na lokaci mai tsawo ba. Ta fuskar soji, isra'ila ta kasa maido da tasirinta na iya ɗaukar matakin gani-ga-wane.
Gwamnatin Benjamin Netanyahu ba ta cim ma kowane daga cikin muradunta na yaƙi da ta gindaya ba, da suka haɗa da rusa Hamas; da sako duka waɗanda aka yi garkuwa da su; da maido da mutanen da hare haren da ake kai wa arewacin isra'ila babu ƙaƙƙautawa suka sa suka tsere daga muhallansu.
Har yanzu Hamas ce ke da iko da galibin yankunan Gaza, yayin da dakarun Isra'ila ke ci gaba da dawowa suna gudanar da ƙarin samamen soji a wurare irin su Jabalia da Khan Younis, yankunan da a baya ake ɗauka an ƙwace su daga hannun Hamas. Sama da ƴan isra'ila mutum 100 da ake garkuwa da su har yanzu suna hannu.
A Lebanon, a maimakon su janye zuwa kudancin Rafin Litani kamar yadda isra'ila ta yi tsammani kuma ta buƙata, a kullum Hezbollah na kai hare hare kan cibiyoyin sojin Isra'ila ta hanyar yin amfani da jirage marasa matuƙa da kuma rokoki.
Har yanzu wasu mazauna arewacin isra'ila su 70,000 ba sa zaune a muhallansu. A taƙaice, daga Hamas har isra'ila babu wacce aka sa ta saduda, kuma yaƙin na ci gaba da gudana babu wata takamammiyar matsaya.
Bugu da ƙari, kuɗaɗen da Isra'ila za ta kashe kan al'amuran soji a shekarar 2024 sai ya ninka na shekarar da ta gabata sau biyu. Ɓangare mafi tsoka na ƙarin ana kashe su ne kan "na'urorin kakkaɓo makamai" da makaman atilare da kuma albashin sojojin sa-kai.
Shi ma batun "tattalin arziƙin makaman roka" shi ma yana ƙara ɗaukar hankali, yayin da na'urar kakkaɓo makamai ta isra'ila ta ninninka makamin da take kakkaɓowar tsada.
A wajen Iran, kuɗin da aka kashe wajen ƙera na'urar kakkaɓo makamanta ya ninka wanda ta kashe wajen ƙera makaman nata aƙalla sau uku, a faɗar wata majiyar isra'ila. Kuɗaɗen da Isra'ila ke kashewa ya ma fi ƙaruwa yayin da take kakkaɓo jirage marasa matuƙa da rokoki masu araha da Hezbollah da Hamas ko kuma ƴan Houthi a Yemen ke harbowa.
A ɗaukacin tarihinta na yaƙi, isra'ila ba ta taɓa dogaro da taimako daga ƙawayenta kamar yanzu ba, musamman ma Amurka. Hakan saboda galibin makaman da take kai hari da su ta dogara ne da taimaka mata da su, har da ƙari, da Amurka ke yi akai akai.
Durƙushewar tattalin arziƙi
Baya ga ƙetare manufofin sojinta, shekarar da ta gabata an sheda cewa tattalin arziƙin isra'ila ya faɗa cikin mummunan yanayi.
A sulusin ƙarshe na shekarar 2023, musamman a makwannin da suka biyo bayan fara yaƙi a Gaza, GDP Isra'ila ya yi ƙasa da kashi 20.7 (a shekara).
Wannan koma bayan cikin hanzari ya faru ne sakamakon raguwar yin amfani da kayan da aka sarrafa da kashi 27, da raguwar da aka samu a kayayyakin da ake fita da su waje da kuma gagarumin raguwa da aka samu a zuba jari a gida da waje.
A halin da ake ciki,harkar gine gine ta durƙushe baki ɗaya, yayin da fannin yawon buɗe ido ya fuskanci babban akasi wajen halartar masu ziyara da kuma samun kuɗaɗen shiga.
A cewar kamfanin da ke bincike harkokin kasuwanci na CofaceBDI, kamfanin Isra'ila aƙalla 60,000 za su dena aiki wannan shekarar.
Bugu da ƙari, an rage matsayin bayar da bashi na Isra'ila sau da dama wannan shekarar, inda na baya bayan nan ya fito daga wajen Moody's, Wanda ya yi ƙasa da matsayin da matakai biyu, daga "A2" zuwa "Baa1" tare da bahagon hasashe sakamakon bazuwar rikicin zuwa kan Hezbollah.
Sannan kuɗaɗen da yaƙin zai laƙume tsakanin shekarun 2023-2025 yanzu an yi ƙiyasin zai kai dala biliyan $55.6, a cewar Bankin Isra'ila.
Saniyar ware a harkar Diflomasiyya
Babban kalubale na uku da Isra'ila ke fuskanta shi ne mayar da ita saniyar ware a idon duniya. Tun ranar 7 ga watan Oktoba shekarar da ta gabata, aƙalla ƙasashe tara, Turkiyya, da Jordan da Bahrain da Columbia da Honduras da Chile da Afrika ta Kudu da Chadi da kuma Belize - imma sun yanke hulɗarsu ta diflomasiyya da Isra'ila ko kuma sun rage mata armashi.
Bugu da, ƙarin ƙasashe guda tara da suka haɗa da Spain da Norway da Ireland da kuma Slovenia sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa a hukumance.
Ƙoƙarin ƙulla hulɗa da ƙasashen Larabawa a yankin - muhimmin abu sosai a dabarun diflomasiyya na isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya a ƴan shekarun da suka gabata - yanzu an jingine batun, wataƙila ma har abada kenan.
Yariman Saudi Arabia mai jiran gado Mohammed bin Salman, alal misali, ya bayyana a makwan jiya cewa, ƙasarsa ba za ta ƙulla hulɗar diflomasiyya da Isra'ila ba, idan babu ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta.
Wannan matsaya, na nuni da wani babban koma baya ga manufofin ƙasashen wajen Isra'ila, wanda bisa al'ada, ya mayar da hankali kan ƙulla hulɗar diflomasiyya da ƙasashen yankin.
A halin da ake ciki, goyon bayan da ƙasashen duniya ke bai wa Falasɗinawa na ƙaruwa kamar yadda hakan ke bayyana a ƙudurorin Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya ke nunawa tun ranar 7 ga watan Oktoba shekarar da ta gabata.
A watan Mayu, ƙasashe mambobi 143 sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da a ƙara ƴancin Falasɗinu a MDD yayin da ƙasashe tara ne kaɗai da suka haɗa da Micronesia, Palau, Nauru, and Papua New Guinea - suka kaɗa ƙuri'ar adawa da hakan (wato suka goyi bayan Isra'ila). Wannan sauyin ya nuna matsayin isra'ila ta fuskar diflomasiyya a idon duniya.
Mutuncin Isra'ila na zubewa
Faɗaɗa yaƙin da firaministan isra'ila Benjamin Netanyahu ke yi ya zubar da mutuncin ƙasarsa sosai. Wannan matsaya za ta iya yiwuwa ita ce mafi ƙanƙanta a tarihin ƙasar na shekaru 76.
Muhimman al'amurra guda biyu sun nuna hakan: Na farko, mai shigar da ƙara na Kotun Aikata Manyan Laifuka Ta Duniya ya shigar da ƙarar Netanyahu da Ministan Tsaro Yoav Gallant bisa zargin aikata "laifukan yaƙi da kuma laifuka kan cin zarafin bil adama."
Na biyu, babbar kotun MDD, Kotun Duniya, ta fahimci akwai yiwuwar abubuwan da Isra'ila ke aikatawa su iya zama aikata kisan kiyashin. Wannan lamari na ci gaba da wakana.
Isra'ila har ila yau na fuskantar mummunan rasa goyon bayan jama'a, har ma a cikin ƙasashen manyan ƙawayenta.
Wata ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta YouGov da The Economist da aka gudanar daga 21 zuwa 23 na watan Janairu 2024 ta nuna cewa rabin waɗanda suka zaɓi shugaban Amurka Joe Biden a zaɓen Amurka na shekarar 2020 sun yi imanin cewa Isra'ila na "aikata kisan kiyashin kan fararen hular Falasɗinawa."
Wannan binciken, wanda ya ƙunshi Amurkawa 1,664, ya bayyana wani babban sauyi kan tunanin jama'a game da mummunan abin da isra'ila ke aikatawa.
Neman tsira
Wani muhimmin abu na ƙarshe shi ne adadin ƴan isra'ila da ke ficewa daga ƙasar ya ƙaru da kashi 285 biyo bayan 7 ga watan Oktoba.
Bugu da ƙari, kusan kashi ɗaya cikin huɗu na Isra'ilawa suna duba yiwuwar barin ƙasar a cikin shekarar da ta gabata saboda bazuwar yaƙin ta fuskoki da dama, a cewar nazarin Kantar da kuma ƙafar yaɗa labarai jama'a kan.
Abin mamaki, isra'ila na zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suka kasance mafi hatsari ga al'ummarsu - saɓanin hangen da waɗanda suka assasa ƙasar suke da shi lokacin da suke kafa ta.
Duk kalubalen isra'ila na tattalin arziƙi da diflomasiyya da zamantakewa da ma na Shari'a, wataƙila su ƙaru a cikin yaƙin da ke bazuwa kuma mara iyaka da Netanyahu ke jagoranta.
Haka galibi abubuwa ke ƙarewa idan neman tsirar siyasar mutum ɗaya tilo ya zama yana sama da komai.
Dr. Emir Hadžikadunić a halin yanzu mataimakin farfesa ne a makarantar kimiyyar da fasaha ta jami'ar Sareyevo, Bosnia Herzegovina. Har wa yau, farfesa mai kai ziyara ne kuma fitaccen jami'i a wasu jami'o'i da dama a Bosnia Herzegovina da Turkiyya da kuma Malaysia. Dr. Hadžikadunić a baya bayan nan ya kasance jakadan Bosnia a Iran da Malaysia kuma ya wallafa muƙaloli da dama ga kafofin yaɗa labarai da kuma takardun ilmi.
Togaciya: Ra'ayoyi da marubucin ya bayyana ba dole ya zo daidai da ra'ayi fahimta da kuma manufofin editan TRT Afrika ba.