Daga Mehmet Cem Oğultürk
Zaɓen shugaban ƙasa na Donald Trump na farko ya shammaci duniya, kuma manufofinsa na ƙasashen waje ya yi tasiri a kan ƙasashen fiye da adadin aminan Amurka mafi kusa.
Amma duk da haka, iya wa'adin mulkinsa kacokan har ma yanzu, Afrika - wacce yawanci ake yi wa kallon nahiyar da za ta samu ɗaukaka nan gaba kuma wani ƙunshi ne mai tarin alhairai - yana wahala zancenta ya taso a ra'ayoyin jama'a ko agendojin da suka shafi manufofi.
A wa'adin mulkinsa na farko, manufofin ƙasashen wajen Trump kan Afrika sun kasance a birkice kuma ba su da wata takamammiyar alƙibla.
Yayin da sake zaɓarsa ke ƙaratowa, abin tambaya a nan shi ne: Wace rawa Afrika za ta taka a wa'adin mulkin Afrika mai zuwa, kuma yaya hakan zai yi tasiri kan daidaiton muradun nahiyar da na Afrika?
Hange ta yin amfani da China
Lokacin da Trump ya tsaya takara da farko, ya yi wasu maganganu game da Afrika, abin da ya nuna gajeren hange kan matsayinsa game da nahiyar. Da aka zaɓe shi, hankalinsa ya koma kan tsaro musamman yaƙi da ta'addaci a wasu ƙasashen Afirka da aka zaɓa.
Hakan ya ƙarfafa zaɓin Trump game da muradun tsaro na gajeren zango, a maimakon gano dimbin buƙatun Afrika, da suka haɗa da bunƙasar tattalin arziƙi da agajin jin ƙai.
Babban abu a kallon da Trump ke yi wa Afrika ita ce China. Da yake yi wa Afrika kallo ta ma'aunin hamayyarsa ta cinikayya da China, Trump ya saka ido sosai kan dangantakar kasuwancin Afrika da Beijing.
Amma, a maimakon ya samar da wani kyakkyawan zaɓi ga ƙasashen Afrika, sai matakansa (galibi kan gogayya da China) suka taƙaita tasirin Amurka sannan suka jawo sukar cewa ya raina baiwar da Afrika ke da ita.
Aƙidar 'Amurka ce gaba da komai'
Matsayin Trump kan "Amurka ce gaba da komai" shi ma ya kawo tarnaƙi kan dangantakar tattalin arziƙi da Afrika. Dokar Bunƙasa Afrika Da Samar Da Damammaki (AGOA), wani shiri da aka ƙaddamar zamanin tsohon shugaban ƙasa Barack Obama domin bunƙasa harkar fitar da kayayyakin Afrika, ya fuskanci halin ko-in-kula a wajen gwamnatin Trump.
Trump bai nuna sha'awa sosai ba a ƙulla sabuwar yarjejeniyar cinikayyar da ƙasashen Afrika, abin da ke nuni da cewa faɗaɗa dangantakar tattalin arziƙi tsakanin Amurka da Afrika ba shi da muhimmanci. Wannan mataki ya kawo tarnaƙi ga damarmakin bunƙasa ga duka ɓangarorin biyu.
Da ya muhimmantar da muradun cikin gida, hakan na nufin Trump ya bai wa wasu manyan ƙasashen duniya dama, musamman China, su karfafa dangantakarsu.
Da ba ta yi amfani da damar abubuwan da take da su a matsayinta na wata babbar mai zuba jari ba, Amurka ta kuskure damar bunƙasa matsayinta ta fuskar tattalin arziƙi a faɗin nahiyar.
Dangantaka ta fuskar soji
Yayin da gwamnatin Trump ta dankwafar da dangantakar tattalin arziƙi da Afrika, ta ci gaba da dangantaka ta fuskar soji, musamman a yankunan da ke fama da ta'addaci, kamar Sahel da Somalia.
Amurka ta tallafa wa matakan yaƙi da ta'addaci, tana jaddada matsayinta a matsayin jigo a wajen yaƙar ƙungiyoyi da dama da suka haɗa da Al Shabab a Somalia, da ƙawayen Daesh a yankin Sahel da kuma Boko Haram a Najeriya, galibi ta hanyar kai farmaki ta sama, bayar da horo da musayen bayanan sirri da dakarun gida da na yanki.
Matakin mayar da hankali kacokan kan tsaro na Trump bai magance manyan matsalolin Afrika na zamantakewa da tattalin arziƙi ba, abin da ke zamar da shi masalaha ta ƙaramin lokaci a maimakon ta dindindin.
Yanzu, matakin Trump na mayar da hankali kan tsaro kacokan bai magance manyan matsalolin Afrika na zamantakewa da tattalin arziƙi ba, yana zamar da shi masalaha ta ƙaramin lokaci a maimakon ta dindindin.
Aiwatar da mataki na biyun da aka ambata da ya rage rashin zaman lafiya da tsattsauran ra'ayi tun daga tushesu,ya amfani tsaron Amurka.
Sannan kuma da ya samar da damarmakin tattalin arziƙi da za su ƙarfafa dangantakar Amurka da Afrika ta fuskar cinikayya da diflomasiyya na tsawon lokaci.
Sabon Yaƙin Cacar Baka Ne?
A baya bayan nan, Afrika ta jawo hankalin manyan ƙasashen duniya daidai gwargwado, inda China da Rasha suka yi gagarumin yunƙuri.
Yayin da gwamnatin Trump ke nuna damuwa da tasirin China da ke ƙaruwa, ba ta samar da wani gwaggwaɓan zaɓi ba. Ta hanyar zuba jari a fannin samar da kayayyakin more rayuwa a Afrika da kuma ƙawance ta fuskar kuɗi, China ta kafa kanta sosai, yayin da Rasha ta faɗaɗa tasirinta ta hanyar ƙulla yarjejeniyoyi ta fuskar soji.
Idan aka kwatanta, gwamnatin Trump ba ta da wata tsararriyar dabara ta mayar da martani kan waɗannan matakan, abin da yake kassara matsayin Amurka a nahiyar na lokaci mai tsawo.
Tare da aƙidar "Amurka kafin komai", manufofin Trump sun kasa karya lagon tasirin China da Rasha a Afirka, abin da ya zamar da nahiyar wani muhimmin fage a siyasar duniya. Rashin taɓuka kataɓus ɗin Trump zai iya sa wa a bar Amurka a baya.
Rawar da Afirka za ta taka nan gaba
Bayan sake zaɓar Trump, akwai buƙatar samar da gwaggwaɓar manufar ƙasashen waje ta Amurka a kan Afrika. Afrika, bisa la'akari da yawan matasanta da ɗimbin albarkatunta da kuma tattalin arziƙinta mai bunƙasa, ta shirya taka ƙarin muhimmiyar rawa a fagen kasuwar duniya.
Kafin Amurka ta zama tana da tasiri, ya kamata gwamnatin Trump ta ɗauki Afrika a matsayin muhimmiyar ƙawa, ta hanyar daidaita muradun tsaro tare da na zuba jari a shirye shiryen tattalin arziƙi, siyasa da zamantakewa.
Domin tabbatar da tasirinta, yakamata gwamnatin Trump ta yi amfani da shirye shirye kamar AGOA, da ƙulla alaƙar cinikayya da kuma karfafa zuba jari a shirye shiryen raya Afirka.
Bai kamata ƙawancen sojin Amurka ya mayar da hankali kacokan kan yaƙi da ta'addaci ba kaɗai, ya kamata ya mayar da hankali kan abubuwan da ke jawo tashin hankali da kuma goyon bayan masalahar siyasa mai ɗorewa.
Rashin tabbas tattare da manufofin Trump ya rage tasirin Amurka, yayin da ƙasashe irin su China da Rasha sun yi amfani da wannan giɓin.
A yanayi na ƙaruwar gogayya a duniya, kar Amurka ta yarda ta kau da kanta kan muhimmancin Afrika.
Idan aka yi gaba, ya kamata Trump ya nemi gwaggwaɓar manufa mai ɗorewa game da Afrika.
Idan ta nuna ta san muhimmancin Afrika a fagen siyasar duniya kuma ta karfafa dangantaka, Amurka za ta iya farfaɗo a matsayin ƙawa abar dogaro kuma ƙasa mai tasirin gaske a nahiyar.
A yanayi na ƙaruwar gogayya a duniya, kar Amurka ta yarda ta kau da kanta kan muhimmancin Afrika.
Ƙulla ƙawancen diflomasiyya da na tattalin arziƙi da kuma na soji tare da ƙasashen Afrika yana da muhimmanci wajen Amurka ta samu ƙarfin faɗa-a-ji da kuma ci gaba da damawa da ita a wannan muhimmin yankin.
Marubucin, Mehmet Cem Oğultürk a halin yanzu shi ne daraktan Cibiyar Gabatar Da Buƙata Da Bincike Ta Afrika a Jami'ar Aydin ta Istanbul kuma shugaban sashen kimiyyar Siyasa da Dangantakar ƙasa da ƙasa. Ya kammala karatu a makarantar soja ta Turkiyya a shekarar 1993. Shi ne shugaban Ofishin Hulɗa Da Jama'a kuma muƙaddashin kwamanda lokacin kafa cibiyar horas da sojoji a Somalia ta TURKSOM a shekarun 2016-2017. Fannin ilimi da ya fi mayar da hankali a kai ya ƙunshi Tsaron da Ƙasa da kuma Dangantakar Ƙasahen Transatlantic,tare da mayar da hankali kan yankunan Afrika da Balkan.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba dole ne su zama daidai da ra'ayi, da hange da fahimtar manufofin editan TRT Afrika ba.