Daga David Schultz
Galibin lokaci ana bayyana aikin jarida da cewa rubuta daftarin tarihi na farko. Amma fashin baƙi kan kimiyyar siyasa shi ne daftarin na biyu. Yayin da muke tunani game da nasarar da Donald Trump ya samu da kuma kaye da Kamala Harris ta sha a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024, tambayar ita ce, mene ne ya faru, kuma me ya sa ya faru?
Akwai dalilai na dogon zango da suke bayyana tashin Trump da aƙidar Trump, da kuma batutuwa masu gajeren zango da suke sauya yanayin masu zaɓe a Amurka.
Masana kimiyyar siyasa irin su Walter Dean Burnham sun yi magana game da muhimman zaɓuɓɓuka da sake ƙulla ƙawance a siyasar Amurka.
A wasu lokuta a tarihin Amurka, zaɓuɓɓuka suna da matuƙar muhimmanci da tantancewa har suna iya kawo cikas ga daidaiton siyasa.
Suna haifar da sabbin ƙawance da sauyin ra'ayin zaɓe tsakanin masu zaɓe. A Amurka, ƙasar ta sheda bayyana a hankali na abin da tun da farko a 1930 ake kira sabuwar yarjejeniya, ƙawancen jam'iyyar Demokarats da ya ƙunshi kungiyoyin mutane masu ƙaramin ƙarfi da mutane marasa rinjaye da mabiya darikar katolika da yahudawa da kuma manoma.
Sake ƙulla ƙawance a siyasance
Cewa an sake ƙulla ƙawancen ne a shekarun 1960 da 1970, aka sauya ta bayan Dokar Ƴancin Farar Hula ta shekarar 1964, da Dokar Ƴancin Yin Zaɓe ta shekarar 1965, Hukuncin Kotun Ƙoli ta Roe v. da ta saka baki kan batun ƴancin kafa jam'iyyar marasa rinjaye da zubar da ciki.
A nan aka fara tushen aƙidar Trump, da farko da Richard Nixon a 1968 da kuma Ronald Reagan a 1980 suka tsaya takara da ke adawa da juyin juya halin al'ada na shekarun 1960s.
Sun rarrashi fararen fata masu matsakaicin hali da ma'aikata da aka manta da su, waɗanda suke ganin sauye sauyen da ke faruwa a cikin al'umma ya tarkata su a gefe.
Bugu da ƙari, lokacin shekarun 1970s da 1980s tattalin arziƙin Amurka, wanda aka kafa shi kan masana'antu da aikin ƙwadago ya samu matsala.
Guraben aikin masana'antu fiye da miliyan 37 sun salwanta, wasu saboda ɗebo ma'aikata daga wasu wuraren wasu kuma saboda fasahar zamani.
Ma'aikata, marasa shedar kammala makaranta ta digiri, waɗanda a baya sun samu bunƙasar arziƙi da wadata yanzu kwatsam sai suke yi wa kansu kallon sune masu asara a tsarin tattalin arziƙin da cikin hanzari ke zama wanda ya dogara da fasaha da yi wa wasu hidima.
Jam'iyyar Demokarats ƙarƙashin Shugabannin ƙasa Bill Clinton da kuma daga baya Barack Obama ba su tattauna da waɗannan mutanen ba.
Sun zaɓi su gina jam'iyyar Demokarats kan ƴan boko, waɗanda suke da hali, ba su cika damuwa da kuɗaɗen jingina ba sun fi mayar da hankali kan abubuwa kamar siyasar asali.
Obama ya sauya taken yaƙin neman zaɓensa na fata da sauyi zuwa tallafin masu bayar da gudummawa, samar da kuɗin tallafawa miliyan 10 ga Wall Street.
Tasowar Trump
Trump ya ce jam'iyyar Democrats ba ta damu da fararen fata talakawa ba, haka ma jam'iyyar Republican.
Trump ya yi jawabi game da fargaba da zaƙuwar tattalin arziƙin Amurkawa da yawa da suke ganin an yi watsi da su.
E, ana kallon saƙonsa a matsayin na ƙyamar jinsi da wariyar launin fata, amma ya yi tasiri kan Amurkawa da dama yayin da ya shi kuma ya daidaita kansa a matsayin wani zaɓi a fagen siyasa.
Banbancin tsakanin jinsi wani bangare ne da ya kassara Hilary Clinton a 2016, amma tana da nata gazawar a siyasance, daga ƙarshe ta gudanar da yaƙin neman zaɓe cike da kurakurai da saƙo da dabaru marasa inganci.
Nuna banbanci a tattalin arziƙin Amurka da yake ta ginuwa tsawon shekaru 50 ya ci gaba. Mutane da dama sun lura cewa a shekaru huɗu da suka gabata farashin madara da burodi da ƙwai da sauran kayayyakin masarufi ya tashi, kuma suna fafutika.
Trump ya sha kaye ne a 2020 wataƙila saboda yadda ya tafiyar da annobar da kuma buƙatar daidaiton siyasa.
Democrats sun sake bayar da goyon bayan ƙawancen siyasarsu da ke disashewa ga shugaban ƙasa Joe Biden kuma da ƙyar suka kayar da Trump. Amma an sauya ƙuri'u 43,000 a tsakanin jihohin da ba ɗan takarar da ke iya alwashin nasa ne na Arizona, Georgia da kuma Wisconsin, da Trump ya sake lashe zaɓen.
Lokacin da muka zo shekarar 2024, gazawar Biden da jam'iyyar Demokarats sun bayyana. Biden shugaban ƙasa ne mai rauni saboda shekarunsa da kuma raunin tunaninsa da yake a bayyane.
Bugu da ƙari, nuna banbanci a tattalin arziƙin Amurka da yake ta ginuwa tsawon shekaru 50 ya ci gaba. Mutane da dama sun lura cewa a shekaru huɗu da suka gabata farashin madara da burodi da ƙwai da sauran kayayyakin masarufi ya tashi, kuma suna fafutika.
A halin da ake ciki, motsa batutuwa masu nasaba da wariyar launin fata da yawan jama'a da tsattsauran ra'ayi kan gwagwarmayar siyasa tsakanin kabilu mabanbanta da kuma kambaben kafofin watsa labarai da kuma warwatsa bayanai sun karfafa waɗannan batutuwan.
Yayin da gazawar Biden ta bayyana ƙarara kuma Harris ta maye gurbinsa, ba ta iya magance manyan matsalolin da shi da jam'iyyar Demokarat suka saka mata a gaba ba.
Ko shakka babu, ita ƴar takara da ba ta dace ba ne kuma ɗauke da saƙo da dabaru da ba su dace ba, amma fa babu ɗan takarar jam'iyar Demokarat da zai lashe zaɓen nan.
Babu dabara mai kyau
A karan kanta, ba ta da wani takamaiman dalilin da take son zama shugaban ƙasa ban da cewa Trump sheɗani ne.
Ita da jam'iyar Demokarat sun dogara sosai a kan ƴancin zubar da ciki da batutuwa masu nasaba da haihuwa a matsayin batutuwan tattaunawa kuma ta gudanar da yaƙin neman zaɓe da ya ta'allaka kan manyan ƴan boko.
Wataƙila ƙyamar mata da ƙyamar jinsi za a iya cewa ya ɗan taka rawa wajen rashin nasara da ta yi, amma abubuwa da dama sun faru.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa Amurka ta koma hannun masu tsattsauran ra'ayi. Hatta mata, duk da suna nuna damuwa game da zubar da ciki, sun ƙaurace mata saboda matsalolin tattalin arziƙi.
Yaƙin neman zaɓen Trump da ya fi mayar da hankali kan maza ko shakka babu ya taimaka masa wajen jawo maza masu zaɓe zuwa bangarensa, amma kuma yana jaddada cewa saƙonsa ya shafi duka jinsi game da mutane nawa ne har yanzu ba a lissafi da su.
Duk da Harris ba ta fito fili ta bayyana ƙarara ita ƴar takara mace ce mai gaurayen tsatso, amma abin da ya fi fitowa fili a yaƙin neman zaɓenta shi ne asalinta wanda ke tattare da saƙon yawan jama'a.
Sai dai yawan jama'a ba ƙaddara ba ce. Muhimman al'amuran tattalin arziƙi da kuma ji ba a damawa da mutum, manyan abubuwa ne da ke nuna inda hankalin mutane ya fi karkata wajen zaɓe.
Abin da sakamakon wannan zaɓen ya nuna ba watsi da masu zaɓe na gajeren zango ba ne, face na dogon zango ne.
Jam'iyyar Demokarats ta rasa talakawa, har da matasa masu zaɓe da mata da yawa waɗanda suka ci gaba da damuwa game da matsayin tattalin arziƙinsu.
Kawo yanzu babu tabbas ko Republican za su iya riƙe wannan ɓangaren na daga masu zaɓe, ya danganta da yadda Trump ya magance matsalolinsu a shekaru masu zuwa.
Amma sai lokacin da jam'iyyar Demokarat za su koyi yadda za su yi magana da waɗannan mutane - sannan su roƙe su - za su ci gaba da yin asara, wataƙila ba dayawa ba, amma duk da hakan dai za su yi rashin nasara.
Marubucin David Schultz farfesan kimiyyar Siyasa da Nazarin Shari'a da kuma Nazarin Muhalli a jami'ar Saint Paul, Minnesota. Shi ne mawallafin litattafai fiye da 45 da kuma muƙaloli 200.
Togaciya: Ra'ayoyin da aka bayyana a nan na marubucin ne, kuma ba sa wakiltar ra'ayi, komahangar editocin TRT Afrika.