Gamayyar hotuna na nuna Mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris a bangaren hagu a ranar 7 ga Agustan 2024, da dan takarar shugaban kas ana jam'iyyar Republican tsohon shugaban kasa DOnald Trump a ranar 31 ga Yulin 2024. / Photo: Others

Yadda manufofin shugaban ƙasar Amurka Joe Biden suka ɓata ran masu jefa ƙuri'a na Amurka ya sake fitowa ƙarara a wannan makon ta hanyar zanga-zangar magoya bayan Falasɗinawa a wajen otel ɗin da Kamala Harris take a Chicago, inda aka gudanar da Babban Taron Ƙasa na jam'iyyar Democratic na 2024.

Zanga-zangar na nuni da cewa a wajen gama-garin Ba'amurke mai kaɗa ƙuri'a, manufofin ƙasashen waje abu ne mai muhimmanci a zaɓen Nuwamban 2024 mai zuwa.

Idan aka zo batun alaƙar ƙasa da ƙasa, Harris ta daidaita kanta don zama mai ƙalubalantar tsohon shugbn ƙasar Donald Trump, abokin hamayyarta na jam'iyyar Republican. Amma shin tana da wani bambanci da shi? Bari mu kalli wannan batu:

Aƙidun Harris

A matsayinta na mataimakiya ga Biden, ana tsammanin Harris za ta ci gaba da bin sahun wannan gwamnati a fannin manufofin ƙasashen ƙetare.

Ziyarce-ziyarcen da ta yi a baya zuwa ƙasashe 121 tare da ganawa da shugabanni 150 alamu ne na yadda ta yi amanna da amfani da hanyoyin haɗin kai wajen ɗabbaƙa manufofin ƙasa da ƙasa. Wannan na nufin mayar da hankali ga ƙulla babbar alaƙa tsakanin arewacin Amurka da Turai; ƙarfafa NATO; ƙara ƙarfin ƙawancen India da Pacific inda ASEAN da India ke taka babbar rawa; da kuma ci gaba da kallon China a matsayin babbar abokiyar hamayya a fannin tattalin arziki.

A ɗaya gefen kuma, manufar Donald Trump ta 'America First' (Amurka ce a farko) na nufin yana da tantama game da ƙawancen Amurka irin na NAFTA da NATO. Sannan yana yi wa Rasha kallon tausasawa game da yaƙin da take yi a Ukraine.

Bambanta da juna game da Ukraine da Rasha

Babban bamancin manufofin ƙasashen waje tsakanin Kamala Harris da Donald Trump shi ne batun Rasha.

Harris na kallon Shugaba Vladimir Putin a matsayin abokin gaba saboda yadda ya afka wa Ukraine da yaƙi, kuma ta fito ƙarara ta nuna tana goyon bayan Kiev. Wakilcin da ta samu a taron Zaman Lafiya a watan Yuni a Ukraine da alƙawarin da ta yi na samar da tsaro a Ukraine da 'yanci a wajen Babban taron Tsaro na Munich a watan Fabrairu, na nuni da za ta ci gaba da aiki da manufofin gwamnatin Biden na goyon bayan Ukraine don ƙalubalantar Rasha.

Idan hakan ta ci gaba da tabbata, kuma Harris ta ci gaba ga goyon bayan Kiev ta hanyar aika makamai da goyon bayan diflomasiyya, to babu wata ƙofar neman Rasha da ta zauna a teburin sulhu, wanda hakan zai ƙara rura wutar rikicin.

Wannan ya saɓa kai-tsaye da yadda Trump yake kallon rikicin Rasha da Ukraine. Trump na nuna ƙawance da Putin saboda tarihinsa na ƙaunar shugabanni masu ƙarfin faɗa-a-ji da kuma buƙatar ƙarfafa kasuwanci da Rasha wanda ya fara tun 1987.

Trump ya bayyana cew aidan aka zaɓe shi, zai yi aiki don kawo ƙarshen yaƙin sannan ya kawo ƙarshen ɗaukar nauyin Ukraine da Amurka ke yi a yaƙin. Amma dai wani abu da ke a ayar tambaya shi ne yadda zai ja hankalin shugaban Rasha Vladimir Putin da na Ukraine Vladimir Zelensky su zauna a teburin sulhu.

Amma matakin da Harris ta ɗauka na ci gaba da goyon bayan Ukraine wanda hakan zai hana sulhu da Rasha, zai kuma sanya a ci gaba da yaƙin.

Gabas ta Tsakiya

Harris da Trump na bayar da goyon baya iri guda ga Isra'ila, amma kowa akwai hanyar da yake bayyana irin nasa goyon bayan.

Harris ta zaɓi kalamai masu taushi kan Falasɗinawa don kawar da ɓacin ran da 'yan Democratic suke da shi saboda goyon bayan da Biden ya nuna ga Isra'ila. Amma ba za a yarda cewar wannan abu na nufin za a dakatar da ba wa Isra'ila makamai ba.

Duk da kalamanta na buƙatar kawo ƙarshen wahalar da Falasɗinawa ke sha bayan ganawa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a Washington a watan da ya gabata, Harris ba ta goyi bayan takunkumin daina bai wa Tel Aviv makamai ba.

Duk da ta bayyana tana goyon bayan warware rikicin ta hanyar kafa ƙasashe biyu, tana fuskantar suka daga magoya bayan Falasɗinawa da masu jefa ƙuri'a na Amurka da ba su gamsu da cewar manufar Amurka kan Isra'ila za ta sauya ba.

Za a iya hasashen manufofin Trump game da Isra'ila. Yadda ba ya ƙaunar masu goyon bayan Falasɗinu da ke zanga-zanga da goyon bayan da yake bai wa Isra'ila sun bayyana a matakin da ya dauka a 2017 na mayar da ofishin jakadancin Amurka a Isra'ila zuwa Birnin Ƙudus daga Tel Aviv.

Sai dai kuma, a yadda ake gwabza yaƙi a Ukraine, Trump ya yi kira da a warware rikicin, kuma ya yi amanna da cewar yana da iko kan Netanyahu sama da Biden saboda shi yana goyon bayan mamayar yankunan Falasɗinawa ba bisa ƙa'ida ba, amince wa da Ƙudus a matsayin babban birnin Isra'ila kuma samar da Yarjejeniyar Abraham da ta baiwa Isra'ila damar sasantawa da wasu ƙasashen Musulmai a yankin.

Sannan kuma, ana tsammanin aika dakaru a dama zuwa Gabas ta Tsakiya idan Harris ta ci gaba da mulki, inda tun bayan kisan gilla ga shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Iran aka aika da manyan jiragen yaƙin ruwan Amurka zuwa tekunan Bahar Maliya da Bahar Rum a Gabas ta Tsakiya. Idan a ƙarƙashin Trump ne za a samu aika sojojin da ma yin kisan gilla ga manyan mutane kamar wanda aka gani ga Kassim Suleymani, shugaban dakarun sojin juyin juya hali na Iran.

A bayyane take ƙarara, goyon bayan Harris a baya ga shirin Amurka na yarjejeniyar Nukiliya da Ian a 2015, ba ya nufin gwamnatinta za ta ki taimaka wa wajen kare Isra'ila idan rikici ya rincaɓe tsakanin kawarta da Iran da sauran waɗanda ke wakiltar ta.

A daya ɓangaren kuma, Trump ne ya cire Amurka daga yarjejeniyar JCPOA a lokacin mulkinsa na farko, kuma tabbas zai kawo wa Isra'ila ɗauki idan Iran ta kai mata hari.

China ta zama kandagarki

Ana tantamar ko manufar Trump ga Rasha ta zama kakkausa da ƙalubalanta. Daga cikin aƙidun Trump akwa ƙoƙarin raunata kasuwancin China da kuma ƙara haraji zuwa kashi 60 na kayan da ake shigarwa Amurka daga China.

Idan aka zabi Harris, duniya za ta iya tsammanin manufofin Amurka a ƙasashen waje su ci gaba kamar yadda suke a yau. Shugabancin Trump kuma zai kawo rashin tabbas, ɗaukar matakin mutum guda da mulkin jama'a.

A baya Harris ta taɓa sukar Trump da cewar ya illata tattalin arzikin Amurka a lokacin tana aiki a matsayin Ministar Shari'a. Amma a matsayinta na Atoni Janar, ta amince da dokar da ke goyon bayan kare hakkokin ɗan'adam a Hong Kong, inda ta kuma yi kira ga Taiwan da ta kare kanta, matakan da China ta yi wa kallon ƙalubale ga ƙarfin mulkinta.

A saboda haka, akwai yiwuwar alaƙar Amurka da China ba ta wani inganta ba a ƙarƙashin Harris, saboda Hong Kong da Taiwan ba batu ne na wasa ba a wajen China. Sannan mu'amala da Beijing a ƙarƙashin mulkin Harris ba ya nuna gogayya tsakanin manyan tattalin arzikin duniya guda biyu zai kawo ƙarshe.

Alaƙar tattalin arzikin Amurka da China na iya ci gaba da fuskantar rikici a yayin da Beijing ke ci gaba da kasancewa a Tekun Kudancin China da wasu wuraren.

Idan aka zabi Harris, duniya za ta iya tsammanin manufofin Amurka a kasashen waje su ci gaba kamar yadda suke a yau. Duk da dukkan 'yan takarar na da ra'ayi kusan irin guda game da Isra'ila da China, shugabancin Trump kuma zai kawo rashin tabbas, daukar matakin mutum guda da mulkin jama'a.

A wajen Harris, za a ga mu'amala da ƙasashen duniya sosai, za kuma a iya hasashen mai zai je ya komo. Amma kuma salon manufar ƙasar kan Isra'ila, Iran da China ba za ta sauya ba.

TRT Afrika