Trump na jawabi a wajen taron 'Spirit of America'.. (Photo: AFP)

Daga John Mac Ghlionn

Kamata ya yi a ce taken Donald Trump na "Fifita Amurka" ya zama mai kawo sauyi - ya zama alkawarin bayar da fifiko ga rayukan Amurkawa, albarkatun kasarsu, da dukkan fifiko sama da komai. Amma, kamar yadda nade-nadensa na baya-bayan nan suka nuna, wannan take nasa karya ce da abin kunya.

Marco Rubio, Mike Huckabee, da Tulsi Gabbard, duk manyan magoya bayan Isra'ila, sun zama manyan masu taka rawa wajen juya akalar gwamnatin. Kamar yadda a baya-bayan nan TRT World ta yi nuni. Zabin ministoci da Trump ya yi ya karkata ga manyan magoya bayan Yahudawan da ke son kafa kasar Isra'ila, masu jiji da kai, da kuma goyon bayan ta'addanci.

A Gabas ta Tsakiya, ba "Fifita Amurka" ba ne, "Fifita Isra'ila" ne.

Huckabee ne cikakken misalin irin wannan akida. Tsohon gwamna, wanda zai zama jakadan Amurka a Isra'ila nan da wani dan lokaci, ya bayyana ƙarara cewar 'za a warware rikicin ta hanyar kafa kasa daya', inda ya yi watsi da wata kalma ta 'Falasdinu', yana watsi da wanzuwarsu da asalinsu.

Wadannan kalami ba a boye suke ba - suna bayyana zukatan da ke goyon bayan Isra'ila sama da komai, suna kebe diplomasiyya mai ma'ana da duk wani yunkuri na samun daidaito.

Rubio, wanda aka sani da tsagwaron zalunci, da Gabbard da aka sani da nuna adawa da masu shiga tsakani, na nuni da wannan matsala.

Ya nesanta sosai da alkawarin da ya yi na zai kawo karshen yaki. Trump na kara rura wutar yakin ne, yana kusantar wadanda suke yi wa yake-yaken da ba su da karshe kallon a matsayin wata dama, ba wai matsala ba.

Yaudara ce da ke cin kanta saboda an yarda da alkawarin. Trump ya yi yakin neman zabe a matsayin mai kutse, wanda zai iya kawo karshen ayyukan kasar a kasashen waje da suke tsotse albarkatu da kudaden Amurka tsawon shekaru.

Maimakon kawo sauyi, sai gwamnatinsa ta zama kamar wani rubutaccen labari da aka sake rubutawa. Yake-yaken da suka ki karewa, cikakken goyon baya ga Isra'ila, da manufofin kasashen waje da suka bar Amurkawa na mamakin wanda ya amfana da maganar "Fifita Amurka".

Marubuci Tom Woods ne ya bayyana wannan abu daidai.

"Ko ma wa ka zaba," in ji shi, "a karshe za ka samu John Mc Cain," tare da nadin da Trump ya yi na baya-bayan nan, an ga yadda wannan son zuciya ya fito karara.

Sanatan jam'iyyar Republican kuma mai kiran kansa dan kishin kasa, marigayi John MacCain ne mai goyon bayan yaki. Ya dinga yawan kira da a dauki matakan soji, daga Iraki zuwa Afganistan zuwa Libya, yana yawan goyon bayan manufofi da ke azurta 'yan kwangilar makamai inda ake barin Amurkawa da biyan kudade da asarar rayuka.

McCain ya zama misalin tsarin da ke wanzuwa da yaƙe-yaƙe, ko ma a karkashin wacce gwamnati ce.

Kwashe kainuwa ko ninkaya a cikinta?

Game da Ukraine, Trump ya yi alkawarin kawo karshen yakin - babban alkawari daga mutumin da tarihinsa ya bayyana shi da wanda ayyukansa suka saɓa da maganganunsa.

Alakarsa ta kusa da Larry Fink, shugaban BlackRock, na sanya shakku game da wannan alkawari.

Fink ba mai iya amfani da karfin gwamnati kawai ba ne, shi ne ya mallaki kamfanin gudanarwa mafi girma a duniya, yana juya tiriliyoyin daloli da kuma yin babban tasiri a kasuwannin duniya da gwamnatoci.

A hanyoyi da dama, shi ne misalin "kainuwa" wanda Trump ya taba alkawarin kwashe wa. Amma kuma, makusantan juna ne sosai, suna ninkaya tare don cimma manufofin bai daya.

Alakar na da muhimmanci. Sosai fa.

Ukraine na ci gaba da kasancewa a cikin rikici, BlackRocks na ci gaba da samun ribar kasuwanci. Kamfanin ya samu wkangilolin taimaka wa wajen 'sake gina" Ukraine, damar da ke da alaka da yakin da ake yi.

Tasirinta ya kai zuwa ga sama da na tattalin arziki; BlackRock na da karfin fada a ji a yanke hukunci a gwa,mnatin Kyiv, ciki har da watsi da tsarin tsara birane - matakin da ya bude kofar tatsar tsarin da dama na cikin tsananin bukata.

Ukraine ta zama marar karfi wajen ikon kasnacewa kasa, kuma ta zama babbar dama ga masu son samun kudade.

Babu riba a batun samar da zaman lafiya, gaskiyar da BlackRock ke amfana, babban kamfanin da ya janyo karyewar kudade a 2008, amma a yanzu shi ke neman tatsar Ukraine.

Wannan yanayi da ake ciki na kara munana idan kuka yi duba ga zuzzurfar alakar masana'antun sojin Amurka da BlackRock.

Wata kungiyar bin diddigin ayyukan kamfanoni ta ce kamfanin na barazana ga Dimokuradiyya. BlackRock na rike da biliyoyin daloli na zuba jari da suke samar da kayan tsaro a manyan kamfanoni irin su Lockeed Martin, Raytheon, da Boeing.

Wadannan kamfanoni na ta gwagwarmaya kan yake-yaken da ake ci gaba da yi.

Kowanne makami mai linzami da aka harba, duk tankar da aka yi yaki da ita, kudi ne ke shiga aljihunsu - kuma BlackRock na samun riba saboda kasancewar sa daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki.

Amma kuma masu bayar da haraji a Amurka ne ke biyan kudaden yake-yaken da ba su da niyyar zuwa karshe.

Alaka ta kusa da Fink da Trump ke da ita na bayyana batutuwa masu cin karo da juna.

Mutumin da ya dinga yawo yana nuna adawa ga masu yaki a duniya amma yana da alaka ta kusa da daya daga cikin manyan masu karfin fada a ji wannan bangare.

A dukkan kalaman da ya dinga yi kan yakin Ukraine, tasirin BlackRock - da ma na Fink - na sanya shakku kan niyyarsa.

Adawa da yaki ko adawa da gaskiya?

Dole ne a kalli duk wadannan da mahanga mai fadi. Trump ya dade da bayyana kansa a matsayin dan takara mai adawa da yaki, wanda zai kawo karshen shigar Amurka yake-yake.

Tsawon shekaru yana jingina kansa ga wannan, amma wannan ma babbar karya ce. Ikirarin da ya yi na cewa zangon farko da ya yi a mulki "shugabanci ne marar ta'addanci da yaki", suk karya ce.

Duk da wannan wasan kwaikwayo da yin jawabi ga jama'a a koyaushe, Trump bai dawo da dakarun Amurka gida ba, bai kuma kawo karshen yake-yaken da Amurka ta shiga ba.

Asali ma dai, ya dinga kara rura wutar rikicin ne. A karkashin gwamnatinsa, aka kara yawan dakaru, aka zurfafa dogaro kan 'yan kwangila, wanda ke kara ingiza wutar rikicin da ya yi alkawarin kawo karshe.

Yaki da jiragen sama, wanda ya tabarbare a lokacin gwamnatin baya, ya sake rikice wa zuwa yanayi mara misaltuwa.

Kamar yadda mahukunta suka bayyana, tsaffin dokokin Amfani da Sojoji na 2001 da 2002 na Amurka - da suka share dokokin da suka ingiza yake-yake tsawon shekaru - sun zama masu aiki a karkashin mulkin Trump.

Mafi muni ma, an kara fadada amfani da su, aka bayar da damar Amurka ta shiga yake-yake sosai.

A lokaci guda, Trump ya yi shugabanci na shekaru hudu yana kara yawan kasafin kudin Pentagon, yana zuba biliyoyin daloli a masana'antun tsaro, wanda yake nuna adawa da su.

Kamar yadda aka gani, mutanen da Trump ya zaba a baya-bayan nan ba abin mamaki ba ne. Tarihinsa ya nuna yadda yake kara rura wutar yaki, maimakon kawo karshen sa.

Alkawarin 'Fifita Amurka" kawai wani mafarki ne na rashin tabbas. Wadanda suka yi nasara a yau ba Amurkawa ba ne, ba kuma mutanen da yake-yake suka fatattaka ba ne.

Isra'ila ce kasar da ta fi kowacce amfana da manufofin kasashen waje na wannan gwamnati - kasar da muradunta suka samu fifiko sama da na Amurkawan da Trump ya ce yana hidimtawa.

A dukkan alkawarurrukan da ya yi na kawo karshen yake-yake, Trump ya zama wani marar muhimmanci a ayyukan da suke yi. Jama'ar Amurka - da rayukan da ake ta rasa wa a Falasdin da Ukraine - ba wani abu ba ne illa dabarun tsirurutar mutane a tsakanin kungiyarsu da ke son cin riba.

Marubuci, John Mac Ghlionn, mai bincike ne kuma mai nazari. An buga ayyukansa a jaridu irin su Newsweek, New Yokr Post, Yahoo Finance da Sydney Morning Herald.

Togaciya: Ra'ayoyin da aka bayyana a nan na marubucin ne, kuma ba sa wakiltar ra'ayi, komahangar editocin TRT Afrika.

TRT Afrika