Matasa sun shiga cikin zanga-zanagar mamaye wani titi da ke gaban ginin jami'ar Sciences Po a birnin Paris na Faransa don nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a Gaza a ranar 26,2024./ Hoto: Reuters

Gomman mutane waɗanda ke da alaka da ƙungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Faransa wato Action des Forces Operationnelles (AFO) ne za su fuskanci shari'ar ta'addanci bisa zarginsu da aikata laifukan cin zarafin musulmai nan ba da daɗewa, ciki har da haɗa baki wurin kashe musulmai masu wa'azi 200.

Shari'ar wadda aka ba da umarnin gabatar da ita amma ba a sanya rana ba, za ta mayar da hankali ne kan tuhumar hare-hare da aka shirya kaiwa a tsakanin shekarar 2017 zuwa 2018, na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar tashe-tashen hankula na ƙyamar musulunci a Faransa tun bayan kaddamar da hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza a watan Oktoban shekarar 2023.

Duk da cewa wannan ƙaramin mataki ne zuwa ga hanya mai ƙyau, sai dai shari'ar da aka kwashe tsawon lokaci ba za ta iya tunkarar babbar matsalar ba juriyar da ƙasar ta yi kan karuwar tashe-tashen hankula na ƙyamar musulmai a Faransa.

Matakan ƙasar kan ƙungiyoyi masu kyamar musulunci da kuma yadda take tunkarar batun 'yancin musulmai tamkar haske da duhu ne.

A takaice dai shari'a kan ƙungiyar AFO ya sake fito da waɗannan batutuwa biyu a fili, tare da fallasa rawar da gwamnatin Faransa ke takawa wajen ba da gudummawarta a tashe-tashen hankula kan ƙyamar musulmai a watannin da suka wuce.

Nesa da yin adalci

A cewar masu gabatar da ƙara, AFO ta yi shirin kashe malamai masu wa'azi su 200 tare da kai wasu hare-hare na gurneti kan al'ummar musulmai, inda ta yi niyyar kaddamar da harbi daga nesa na ta'addanci kan wani masallaci a Clichy-la-Garenne da ke Paris tare da amfani da mambobinta mata wajen zuba guba a cikin abincin halal a manyan kantuna.

Amma saboda ba a kai ga aiwatar da shirin ba, sai aka sanya ayyukan a matsayin ''laifi'' wanda ya kai ga ayyana hukunci na ɗan ƙaramin lokaci- idan akwai kenan.

Akwai sarƙarkiya a cikin wannan mataki, musamman a irin yanayin rashin tabbas na siyasa da ake ciki, sake matsayin ƙungiyoyin na iya tasiri wajen ƙara wa sauran ƙungiyoyi daga "Barjols" da ke adawa da addinin musulunci waɗanda ke shirin fuskantar shari'a karfi.

Mambobin ƙungiyar sun danganta ayyukan ta'addanci da addinin musulunci a baya kana sun nuna aniyyarsu ta kona Musulmai.

A yanzu haka dai 'yan ƙungiyar na shirin fuskantar shari'a a wata mai zuwa, kuma idan har za a bayyana yunƙurin harin ƙare-dangi na AFO a matsayin laifi, kazalika ita ma Barjols na iya kaucewa fuskantar hukunci ta irin wannan hanyar.

Al'ummar Musulmai Faransawa da ke fuskantar barazana ba ta cancanci a yi mata haka ba, la'akari da irin karuwar tashe-tashen hankula na ƙyamar musulmai da aka yi ta fama da su a shekarar bara, ƙasar na buƙatar tabbatar da cewa ta kare 'yanci musulmai daga tashe-tashen hankula na masu tsassauran ra'ayi.

Alal misali, Majalisar Musulman Faransa ta samu wasiƙu 42 na barazana, sannan an lalata gamman masallatai tun bayan soma kai hare-haren Isra'ila a Gaza a watan Oktoba.

An kai hari kan wata ƙungiyar al'adu ta Franco- Turkish a Loiret da ƙungiyar harkokin addinin Musulunci ta Turkiyya (DITIB) a shekarar bara a kuɗancin Faransa.

A cewar hukumar yaki da wariyar launin fata ta Majalisar Turai, tun daga watan Oktoban bara ake ta samun rahotanni na nuna ƙyamar addinin Musulunci, sannan a lokuta da dama ana alakanta musumai da ke sanye da alamomin addini da ta'addanci da tsatsauran ra’ayi.

Addinin Musulunci da ƙasar

Faransa ƙasa ce mai ɗauke da al'ummar Musulmai mutum miliyan shida wato kusan kashi 7 zuwa 10 na al'ummarta. Jami'ai da dama a ƙasar sun jima suna ganin al'ummar a matsayin barazana ga Faransa.

Tuni dai ƙasar ta kafa dokar da ta kyamace sanya hijabi na addinin Musulunci, inda ta faɗaɗa sa ido kan masallatai, tare da tsaurara matakan da gwamnati ke ɗauka kan ƙungiyoyi al'umma.

Al'amura sun ƙara tabarbarewa tun watan Oktoba.

Gabanin gasar Olympics ta 2024 a birnin Paris, masu suka sun bayyana cewa Faransa ta yi amfani da batun tsaro a matsayin fakewa wajen murƙushe al'ummar musulmai a ƙasar.

An yi amfani da wani tsarin sa ido da kuma dakile hare-haren kan musulmai tare da bai wa mahukuntan Faransa damar kawar da ''kowace irin manufa'' da aka sanya a cikin jerin ayyuka na tsassauran ra'ayi da ta'addanci (FSPRT) a ƙasar ƙarkashin ministan harkokin cikin gida na Faransa Gérald Darmanin.

A wata ganawar baya bayan nan da ya yi da ministar gwamnatin Jamus Nancy Faeser, Daemanin ya kuma yi alkawarin haɗa gwiwa da Berlin don dakile '' "tsassauran ra'ayin addinin Islama'', yayin da shugaban masu ra'ayin rikau ta jam'iyyar National Rally ta ƙasa, Jordan Bardella ya yi alƙwarin samar da daftarin doka da za ta taimaka wajen rufe masallatai tare da korar malamai masu wa'azi waɗanda ƙasar ta kallonsu a matsayin ''tsageru''.

Yana da muhimmaci a lura cewa matakan da ake ɗauka kan musulmai da ake ganinsu a matsayin barazana ba ta buƙatar wata shaida na mai laifi.

A takaice dai, 'yan ƙungiyar AFO da ke fuskantar shari'a na iya ƙarewa da hukunci masu sauƙi , za a iya yi waɗanda ake zargi shari'a kan ''laifin makirci na ta'addanci'' kan musulmai, amma a kotun da ba ta da hurumin yanke hukunci kan ta'addanci, hakan na nufin za su fuskanci hukunci na gajeran lokaci, kana ba za a yi musu shari'a a gaban alkali ba.

Don haka, zan yi wuya a iya samar wa musulmai kariya ba domin shi kan shi wannan sashi da ke da matsayi mai girma a al'umma ya gaza hukunta wannan al'umma balle sauran mutane.

Shin Faransa tana iya koƙarinta?

Kuskure ne a mayar da shari'ar AFO a matsayin wani yunƙuri na adalci ta hanyar gurfanar da masu aikata laifuka, hakiƙanin gaskiya, hakan yana bayyana tsarin wanda har yanzu ke jan ƙafa wajen ayyana ƙungiyar a matsayin na ta'addanci duk da yunkurin kisan gilla da aka shirya aiwatarwa, amma banda al'ummar Musulmai na Faransa wadanda ke amfani da ‘yancinsu na yin zanga-zangar lumana.

Tun da samun 'yancin musulmai ba shi da yawa a cikin tsarin gwamnati, hukunta masu tsassauran ra'ayi zai yi matukar wahala.

Mutane da dama sun halarci zanga-zangar neman tsagaita buɗe wuta a Gaza, tare da neman a kawo karshen hare-hare ta sama da raba jama'a da matsugunansu da karfi a birnin Paris na Faransa, Nuwamba 4, 2023/  Hoto: (Reuters/Claudia Greco).

Idan aka yi duba kan jawaban ƙasar kan yakin da Isra'ila ke yi da Gaza, za a ga yanda Paris ta ƙara kaimi wajen kama Musulmai ba bisa ka'ida ba musamman waɗanda suka nuna goyon bayansu ga Falasdinawa, inda suke take musu 'yancinsu na gudanar da taro cikin lumana tare da bayyana kamen da suke yi a matsayin wani mataki na yaki da ta'addanci.

Mussamam ake amfani da dokar wajen aiwatar da irin waɗannan matakan ''yaƙar ta'addanci'' na Faransa don amfani muradun masu tsassauran ra'ayi.

Hakan dai ya samo asali ne daga manyan masu fada a ji daga bangaren masu ra'ayin rikau, karƙashin jagorancin Marine Le Pen, wadanda ke kallon hakan a matsayin wata dama ta ƙara sanya takunkumin da bai dace ba a kan musulmai tare da ƙarfafa labarinsu na abin da ake kira "barazanar Musulunci."

Ko dai ta hanyar hana sanya hijabi a makarantun gwamnati, ko hana rufe fuska ko sanya abaya, gwamnatin Faransa ta taimaka wajen ci gaba da nuna wariya da ƙyama ga mata musulmai

Wadannan matakai na nuna ƙyama sun sa masu tsassauran ra'ayi sun yawan maganganun kan ƙyamar Musulunci, tare da kara nuna wariyar launin fata ga matan musulmai.

Sai idan har an magance matsalar masu nuna wariya da ƙyamar addini Musulunci, akwai yiwuwar Musulmai a Faransa su iya ci gaba da fuskantar tsattsauran ra’ayi.

An fahimci makircin ƙungiyar AFO na ƙyamar musulmai a cikin al'ummar da ke da tsananin rashin haƙuri ga Musulman Faransa.

Har yanzu babu wani takamamman dalilin da zai sa Faransa ta shigar da ƙara tun daga 2018, amma ta nuna ƙarancin kulawa ga karuwar tashe-tashen hankula na kyamar musulmai a cikin 'yan watannin nan.

A ƙarshe dai, zai ɗauki fiye da shari'ar ta'addanci ga Faransa ta iya sauya haƙikanin gaskiyar da ke faruwa a ƙasa tare da samar da yanayin daidaito ga Musulmai miliyan shida.

TRT World