An ga masu zanga-zanga na kacalcala hoton tsohuwar Firaminista Sheikh Hasina a lokacin da suke murnar murabus din ta a ranar 5 ga watan Agustan 2024. / Hoto: Reuters

A yayin da ake ci gaba da matsa lamba kan India da ta mika tsohuwar Firaministar Bangladesh Sheikh hasina ga kasar, ana ganin New Delhi ba ta da hurumin kin amsa bukatar Dhaka.

Sheikh Hasina ta yi amfani da dakarun kasa wajen kashe a kalla 'yan kasar Bangladesh 1,000 da suke zanga-zangar neman a kawo gyare-gyare da sauya fasalin rabon ayyuka da mukaman gwamnati. Nan da ana ka hambarar da Firaministar da ta gudu zuwa India.

A gida, ana zargin ta da aikata manyan laifuka da dama na keta hakkokin dan adam, ciki har da kisan kai, a yayin mulkinta na shekaru 15.

Ta musanta dukkan zarge-zargen. A watan da ya gabata, gwamnatin Bangladsh ta aika da bukata a hukumance ga India kan ta tiso keyar Hasina zuwa gida, a yayin da dubban mutane ke zanga-zanga a kan tituna don neman gurfanar da ita a gaban kotu.

Kuma a makon da ya gabata, Bangladesh ta kara kokarin ganin an dawo da Hasina inda aka soke fasfonta gaba daya.

A nata bangaren, India ba ta ce komai ba game da wannan mataki.

Kazalika, ana kuma zargin ta da jagorantar boren jami'an tsaro a 2009, domin smaun damar ci gaba da kasancewa a kan mulki.

Binciken da Kwamitin Bangladesh Mai Zaman Kansa ke ci gaba da yi, wanda aka kafa don sake bincikar kisan mummuken da aka yi a 2009 saboda lalata shaidar da ake da ita a lokacin mulkin Hasina, na nuni da hannun Hasina a lamarin.

Tare da yadda ake ci gaba da tattara hujjoji, Kwamitin na NIC ya bayyana rawar da Hasina ta taka na shirya tuggun da ya janyo mutuwar sama da mutane 70, mafi yawan su jami'an sojin Bangladesh.

A yayin da a yanzu Kwamitin ke neman da a dawo da ita gida daga India, kin amsa wannan bukata daga New Delhi na iya zama kuskure da ya haura tsananin zarge-zargen ko jerin manyan laifukan da Hasina ta aikata kan jama'ar Bagladesh.

Boren Sojoji

Kisan da aka yi jama'a da dama na BDR 2009 misali ne na boren sojoji a rundunar sojin kasa ta Bangladesh inda jami'an tsaron musamman da ke tsaron kan iyakokin kasar, suka yi wa manyansu tawaye.

Rikicin ya yi sanadiyyar mika biyayyar dubunnan sojoji ga masu biren, inda suka karbe makamai tare da kashe manyan sojoji da fararen hula.

Domin gano musabbabin rikicin, gwamnatin Hasina ta kaddamar da bincike kan kisan kuma BDR sun yi bore ne saboda rashin kyawun yanayin aiki rashin albashi mai kyau da yi musu kallon makaskanta idan aka kwatanta da sauran jami'an soji.

Sai dai kuma, har ya zuwa yau, iyalan wadanda kisan na 2009 ya rutsa da su ba su gamsu ba, kuma sun bukaci da a sake gudanar da bincike kan lamarin.

Wannan ne ya sanya Kwamitin Binciken Kasa Mai Zaman Kansa ya bukaci da a dawo da Hasina zuwa gida Bangladesh daga India, bayan gana wa da wdanda lamarin ya rutsa da makusantansu da Kwamitin ya yi.

Matakin da India ta dauka na ci gaba da bayar da kariya ga Hasina wani babban cikas ne ga aiki da gaskiya. Hakan zai haifar da sakamako ga New Delhi.

Dambarwar diplomasiyya

Tun da jima wa India ke ta kokarin rike kambinta na juya akalar Bangladesh, kuma Hasina babbar kawa ce ga New Delhi tsawon shekaru da suke yakar 'yan hamayyarsu China da Pakistan.

Bayan kifar da gwamnatinta, India ta fuskanci tangarda wajen ci gaba da samun karfin juya sabuwar gwamnatin da ke adawa da Hasina, da kuma yadda take ci gaba da rike da tsohuwar Firaministar a kasarta.

Ko ba jima ko dade, New Delhi za su fahimci cewa ba za a taba kulla alaka mai dadi bayan juyin juya halin Bangladesh matukar dai Hasina na zaune a kasarsu.

Domin gwamnatin Firaminista Narendra Modi ta samu damar kulla alaka da gwamnatin rikon kwarya ta Dakha, dole ne a dauki matakan tabbatar da karfin gwiwa, in ji Jon Danilowicz, wani jami'in diplomasiyyar Amurka da ya yi murabus wanda ya taba aiki a Bangladesh.

Da yake magana da TRT World, ya ce "Bukatar mahukuntan Bangladesh na bayyana irin dambarwar diplomasiyyar da India ke ciki bayan ta baiwa Sheikh Hasina mafaka. Ko ma dai bukatar ta shafi kisan rayuka na BDR, zargin cin hanci da almubazzaranci, ko hannu a mutuwa da batan mutane, a bayyane take karara cewa gwamnatin rikon kwarya ta Bangladesh da jama'ar kasar na son ganin Hasina ta girbin abinda ta shuka na aikata manyan laifuka a loakcin da take kan mulki.

Ko ba jima ko dade, New Delhi za su fahimci cewa ba za a taba kulla alaka mai dadi bayan juyin juya halin Bangladesh matukar dai Hasina na zaune a kasarsu. "

Wannan ya hada da girmama yarjejeniyar mayarwa da juna masu laifi tsakanin kasashen biyu wadda Bangladesh ta sanya hannu a kai a 2013, tare da kuma yi wa yarjejeniyar kwaskwarima a 2016 don hanzarta musayar 'yan tawayen siyasa.

Tanadin yarjejeniyar shi ne, bangarorin biyu za su mayarwa da juna mutanen da aka samu da laifin aikata muggan laifuka irin su almundahanar kudad ko kokarin aikata wa, ingizawa ko hannu a ayyukan da za a iya mayar da mutum kasarsa.

Wannan abu zai yi aiki kan Hasina, a yayin da take fuskantar zarge-zargen kisan kai, murkushe mutane a lamarij BDR na 2009, kirkirar rikici a cikin rundunar soji ta hanyar baiwa jami'an 'paramilitary' su kashe fararen hula da manyan jami'an soji.

Haka kuma, kwaskwarimar da aka yi wa sashe na 10 karamin sashe na 3 na yarjejeniyar mayarwa da juna masu laifi, ya bayyana za a iya kama Hasina idan kotu a Bangladesh ta bayar da umarnin hakan ba tare da duba ga hujjojin da aka gabatar ba.

Sakamakon haka, India ba ta iya dorar da karfin fada a ji a Bangladesh ba, muddin dai ta ci gaba da rike Hasina. Sakamakon hakan zai tawayar da India wadda ke fuskantar adawa daga Chin da Pakistan.

Saniyar ware a tsakanin kasashe

Kuma India na kan hatsarin zama saniyar ware a matakin kasa da kasa, saboda ci gaba bayar da mafaka ga wadda ake tuhuma da aikata muggan laifuka na keta hakkokin dan adam, kamar yadda Babban Mai Gabatar da Kara na Kotun Kasa da Kasa da ke Bangladesh ya bayyana, wanda ya bayyana murkushe jama'a na 2024 a matsayin dalilin da ya sanya za a gurfanar da Hasina a gaban kotu.

Mutane sun yi murnar murabus din Firaminista Sheikh Hasina a Dhaka, Bangladesh, a ranar 5 ga watan Agustan 2024 (REUTERS/Mohammad Ponir Hossain).

Tuntuni Dhaka suka tunkari Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa don gurfanar da Hasina, kuma sun shigar da karar da ke gaban kotun.

Wasu kwararru na gargadin cewa Bangladesh na iya kara wa gaba don neman hakki. Dr. Akalvya Anand, mataimakin farfesa a Tsangayar Shari'a a Jami'ar New Delhi, ya fada wa TRT World cewa "Idan India ta ki sauke nauyin da ke kanta, Bangladesh na iya kai maganar gaban Kotun Kasa da Kasa (ICJ).

A wannan gaba, dokokin a bayyane suke, kuma India ba ta da wata madogara da yawa. Zai zama ko dai ta bi doka ko kuma a shigar da kara, kamar yadda aka yanke hukunci a shari'in baya a IJC."

Saboda, sakamakon siyasa, diplomasiyya, alaka da kasashe da dama da Bangladesh na iya zama mai nauyi ga India ta ci gaba da bayar da mafaka ga Hasina.

A lokacin da ake tuhumar tsohuwar Firaministar Bangladesh da aikata muggan laifuka a kasarta da ma kashe rayuka, mafita kawai ita ce India ta tosa keyarta zuwa Bangladesh.

Marubuci: Hamzah Rifaat, Ya yi digiri a fannin Nazarin Zaman Lafiya da Rikici a Islamabad, Pakistan da Harkokin Duniya da KWarewar Diplomasiyya a Cibiyar Horaswar Diplomasiyya ta Colombo, Sri Lanka. Hamzah Babban Jami'in 'South Asian Voices' ne a Cibiyar Stimpson da ke Washington DC a 2016.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.

TRT World