Daga Patrick Wanjohi da Tsitsi Chakonza
Wani rahoton baya-bayan nan da Bankin Ci gaban Ƙasashen Afirka AFDB ya fitar ya nuna cewa ƙasashen Afirka 11 na daga cikin ƙasashen duniya 20 mafi saurin haɓaka.
A kan haka, labari ne mai daɗi ga ɓangaren kuɗi na nahiyar. Sai dai kuma akwai cikas ta wani ɓangare.
Akwai ƙasashen Afirka da dama waɗanda aka bari a baya ta fuskar ƙwarewa, waɗanda jerin abubuwa ne da suka haɗa da sadarwa da kuma ƙirƙirar ababen da za su magance wasu matsaloli.
Irin wannan ƙwarewar ana son ta a kamfanoni da ke faɗin duniya waɗanda kamar makulli ne na kawo ci gaba.
Wani zai iya dukan ƙirji ya ce manajojin kuɗi a Afirka a tarihi sun samu horo na ɓangarori da dama waɗanda suka haɗa da kula da kasafi da hasashen kuɗin shiga da duba bayanai.
Haka kuma akwai giɓi a abin da muke kira ɓangaren ƙwarewa mai matuƙar amfani, waɗanda ba a cika damuwa da su ba kuma suna da tasiri sosai wajen cimma manufofin kuɗi na ƙasashe.
Muna magana ne game da ingantacciyar hanyar sadarwa, jagoranci, da gudanarwar dabaru, waɗanda za su iya taimaka wa ƙasashe magance matsalolin cikin gida da na waje na tattalin arziƙinsu kamar rashin daidaito a kasuwannin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa, matsalar bashi, da rikice-rikicen siyasa na zamantakewa.
Gidauniyar Africa Capacity Building, wadda hukuma ce ta musamman da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Tarayyar Afirka, ta ƙaddamar da wani shiri mai ma'ana da sabbin dabarun haɓaka jagoranci na shekaru huɗu mai suna Haɓaka Jagoranci da Gudanarwa a Gudanar da Kuɗin Jama'a yayin taron shekara-shekara na AfDB na baya-bayan nan a Nairobi, Kenya.
"Bincike ya nuna cewa daya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da gazawa wurin gyrare-gyare - magance matsalolin tattalin arziki / zamantakewa ba tare da kula da yanayin wutar lantarki da ke shafar su ba a kasashe masu tasowa shi ne rashin kula da al'adu da ingancin gudanarwa," in ji babban sakataren gidauniyar, Mamadou Biteye, kamar yadda ya bayyana a lokacin da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin.
Shirin na da nufin horar da manyan jami'ai a ma'aikatun kudi da harkokin kudi na gwamnati kan tsarin shugabanci nagari da ingantattun hanyoyin jagoranci.
Kasashe shida - Cote d'Ivoire, Ghana, Kenya, Nijeriya, Senegal, da Zimbabwe - an zaɓe su don yin gwaji.
A matsayin wani ɓangare na shirin, dole ne jami'an da ke da alaƙa da ƙungiyoyin kula da kuɗin jama'a su samu ƙwarewa wadda za ta samar da ingantattun ayyuka da sauƙi ga jama'a.
Cinikayya maras shinge
Nahiyar Afirka na neman cimma babban buri na hadakar kasuwa guda daya ga ƙasashe 55 ta hanyar tsarin cinikayyar Afirka maras shinge na African Continental Free Trade Area.
An kiyasta tsarin zai iya haɓaka kasuwancin tsakanin nahiyoyi da kashi 52.3% ta hanyar kawar da harajin shigo da kaya. Hakan na iya haifar da habakar tattalin arzikin Afirka zuwa dala tiriliyan 29 nan da shekarar 2050.
Kwararrun harkokin kudi na gwamnati za su iya zama kan gaba a fafutukar cimma burin da aka sa a gaba da zarar shirin raya kasa ya samar musu da dabarun da ake bukata don samun bunkasar AfCFTA ta hanyar inganta shugabanci da rikon amana, ingantacciyar hanyar sarrafa albarkatu, karfafa karfin cibiyoyi, kara kwarin gwiwar masu zuba jari, da kuma sauƙaƙa haɗin gwiwar yanki.
Kula da bashin Afirka
Ƙasashen Afirka da dama har yanzu na ci gaba da ƙoƙarin farfaɗowa daga irin illar da annobar korona ta yi, haka kuma matsalar bashi na daga cikin matsalolin da ke damun ƙasashen.
Duk da haka, irin ƙwarewar da aka samu daga shirin horarwa, kamar haɓaka tunani mai muhimmanci, yin shawarwari da kuma isar da saƙo, tattalin arzikin Afirka zai iya cin gajiyar jagoranci mai kyau wajen sarrafa bashi yadda ya kamata, tattaunawa game da abubuwa kamar kudaden ruwa da lokacin biyan bashi, da kuma kawar da cin hanci da rashawa. .
Babban burin da ake da shi shi ne bai wa bangaren hada-hadar kudi na nahiyar damar cimma buri na ajandar 2063 da bai wa kasashen Afirka damar da suke bukata wajen ciyar da ‘yan kasarsu gaba da kuma samar da irin nahiyar Afirkar da suke so da kuma ta cancanta.
Marubutan ƙwararru ne daga Gidauniyar Africa Capacity Building wadda hukuma ce ta musamman da ke ƙarƙashin Ƙungiyar Tarayyar Afirka
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi ko dolokin aikin jarida na TRT Afrika ba.