Lokaci ne kawai zai tabbatar da komai.
A wannan makon an gudanar da wasu manyan taruka a duniya - daya a Kazakhistan, sai daya a Washington DC, kuma kasashe biyu kawaye suka ɗaura sabuwar dambar ƙalubalantar Ƙasashen Yamma a watanni da shekaru masu zuwa.
A wajen taron farko, shugaban kasashen mambobin Kungiyar Hadin Kan Shanghai a Astana, China da Rasha sun sha alwashin karfafa alakarsu ta tattalin arziki, siyasa da tsaro a yayin da suke mu'amula da ƙawayensu na Eurosia.
A wajen taro na biyu kuma, mambobin Kawancen NATO na ganawa a Washington a makon nan don karfafa alakar tsaro da kasashen Asiya, suna fatan kalubalantar China da Rasha da ke ƙara haɓaka a duniya.
A shekarar 2001 aka samar da Kungiyar SCO tsakanin China, Rasha da Ƙasashen Tsakiyar Asiya don yaki da ta'addanci da inganta tsaro.
Yau, kungiyar ta kara da kasashen Indiaya da Pakistan da Iran da Belarus. A yayin da alakar kasashen Choina da Rasha da Yammacin Duniya ke kara tsamari, kasashen biyu kawaye na son sake farfado da Kungiyar SCO don kalubalantar Ƙasashen Yamma.
A jawabinsa ga SCO, Shugaba Vladimir Putin ya yi kira da a samar da "sabon tsayayyen tsarin tsaro da cigaba" a Eurasia, ya kuma soki Ƙasashen Yamma bisa yada manufofin biyan bukatun Turai da Turai da Atlantika.
Rasha na kallon SCO a matsayin babbar lemar da za ta yi amfani da ita wajen kawar da sukar Yammacin Duniya saboda yakin Ukraine, ta kuma yi gargadi da kar a ga sojojin Amurka a yankin a nan gaba.
China ma na da irin wannan ra'ayi na tirjiya. Tana daukar SCO a matsayin wata kafa sabuwa ta kalubalantar mamayar Yammacin Duniya a tsarin kasa da kasa, kuma ta soki mamayar da Amurka ta yi a tattalin arzikin duniya a yau.
Shin yunkurin China da Rasha na karfafa alakar tattalin arziki da siyasa da tsaro zai yi nasara?
Bukata iri guda
Akwai fata mai kyau sosai a fannin tattalin arziki.
Tuni China da Rasha suka fara tattaunawar yadda za su dinga kasuwanci da kudadensu a tsakanin kasashen SCO.
Sabbin hanyoyin biyan kudi ne a kan gaba na batutuwan da suka tattauna a wajen babban taron na bana, inda aka matsa kan China ta samar da sabon tsarin biyan kudade na SCO, wanda zai baiwa kudinta daraja sama da dalar Amurka.
Kasashen Tsakiyar Asiya za su iya goyon bayan tattaunawar saboda mafi yawan kamfanoninsu na karkashin takunkumin China.
A farkon shekarar nan, Ma'aikatar Baitilmalin Amurka ta saka takunkumai ga kamfanonin da ke kasashen Kyrgyzstan da Kazakhistan, inda suka bi sahun na Rasha, wanda hakan ya tirsasa su kan dole ne su ajiye amfani da dalar Amurka don sayen kayayyaki daga kasashen SCO.
Daduwar kasuwancin Rasha da kasahen SCO na kara matsa lambar daina amfani da dala. Kasuwanci tsakanin Moscow da SCO ya karu zuwa dala biliyan 333 a shekarar da ta gabata, kuma sama da kashi 90 na kasuwancin Rasha da kasashen SCO ana yin sa ne da kudadensu.
Wannan na da muhimmanci saboda Rasha da China na son samun karfin fada a ji ta fuskar tattalin arziki a Tsakiyar Asiya, kuma suna kallon kaurace wa dalar Amurka a matsayin babbar hanyar habaka kawunansu a karkashin SCO.
Misali, China ta bi sahun karfin tattalin arzikin Rasha inda ta zuba jarin biliyoyin kudi a Tsakiyar Asiya ta karkashin aikin BRI na gina hanyoyi. Manufar ita ce a fadada amfani da kudin China a wajen gudanar da wadannan manyan ayyukan.
Duk da wannan fata nagari da ake da shi, akwai iyaka ga burin habakar tattalin arzikin China da Rasha.
Ku kalli Indiya, duk da ta yarda da fadada amfani da kudadensu wajen kasuwanci da China don magance matsalolin dalar Amurka, tana yi wa BRI na China kallon abu da ya saba wa darajar 'yancinta.
Wadannan 'yan matsaloli ne suka hana duakacin mambobin SCO amincewa da ayyukan hadewar juna na China.
New Delhi kuma na da 'yar damuwar kar ta zama maƙiyiyar Yammacin duniya. Ta nuna sha'awa mai iyaka ga tsarin biyan kudi sabo da Rasha ta goyi bayansa kacokan a tsakanin SCO, kuma ta ci gaba da yin taka tsan-tsan idan aka zo batun neman mafita ta daban.
Rashin halartar Firaminista Narendra Modi a wajen taron na bana ya bayyana karara cewar akwai yiwuwar Indiya ta nesanta kanta da SCO.
Ana kuma bayyana ra'ayin cewar Indiya ba ta wani amfana daga adawar da China da Rasha ke yi ga Yammacin Duniya.
New Delhi na iya ci gaba da biyan manyan bukatunta - samun mai, biyan kudade da nata kudin, karancin fuskantar takunkumi - ba tare da ta goyin bayan China da Rasha ba, kuma ba tare da yin adawa ga Yammacin duniya ba.
Fifiko mabambanta
China da Rasha sun karkafara alakar tsaro a tsakanin kasashen SCO, duk da cewar kowa na da nasa bukatun mabambanta.
A wajen kungiyar da sun kai yawan kashi 40 na jama'ar duniya, ya zama dole a amince da kalubalen tsaro da kasashen ke fuskanta kuma za a magance shi ta hanyar bai daya.
Batun tsaro ga Moscow kusan ya ta'allaka ne ga yakin Ukraine. Putin na kallon SCO a matsayin wani budadden bigire da za a iya amfani da shi don nuna tirjiya ga Ƙasashen Yamma, ya kuma bukaci lallai Ƙasashen na Yamma su amince da ka'idojin da ya sanya don tattaunawa.
Yadda ba a kalli batun Ukraine na kawo cikas din yiwuwar raunin kungiyar kan matsalar kalubalen tsaro. Taron bai yi magana ta hadin gwiwa game da yaki a Ukraine ba, kuma kasashe irin su Kazakhistan da India na da damuwa kan yakin da Rasha ke yi.
A wajen kungiyar da sun kai yawan kashi 40 na jama'ar duniya, da kuma rike da daya bisa hudu na tattalin arzikin duniyar, ya zama dole a amince da kalubalen tsaro da kasashen ke fuskanta kuma za a magance shi ta hanyar bai daya.
Yaki da ta'addanci batu ne da ake tattaunawa. Daduwar hare-haren ta'addanci daga Afganistan na sanya fargaba ta kai tsaye ga Pakistan, kasashe Tsakiyar Asiya da wasu kasashen yankin.
Amma batun bai samu hadin kai ba, a yayinda China da Rasha suka bayar da fifiko ga kalubalantar mamayar Amurka kawai.
A watan Yunin shekarar da ta gabata, Tajikistan ta yi kira ga daukar karin matakai don yakar 'yan ta'adda da ke kai hare-hare a kan iyakokinta, inda Pakistan kuma ta sake yin kira da a dauki kwararan matakan daina amfani da kasar Afganistan wajen kaiwa wasu kasashen hare-hare.
Amma bambancin kallon barazanar da kowa ke fuskanta na zama wani kalubale ga kokarin SCO na daukar matakin tsaro na bai daya.
Shugaban Kasar China Xi Jinping ya kauce wa suka na kai tsaye ga Taliban a wannan watan, ko ya soki yadda ta gaza magance yadda ake kai hare-hare ta kan iyakokinta.
Hakan na zuwa ne saboda yadda China ke da manufar iki tare da Taliban a Afganistan, tana son su kyautata alakarsu, ita kuma ta ba ta taimakon yakar kungiyar Tahrik Taliban Pakistan (TTP).
Matakin na zuwa ne a lokacin da Beijing ke shugabantar kwamitin Yaki da Ta'addanci na SCO.
An fahimci cewar kokarin China da Rasha na habaka alakar tsaro, tattalin arziki da siyasa tare da SCO na kunshe da rikitattun alkawura.
Habakar zuba jari da amfani da kudadensu a tsakaninsu ne manyan abubuwan da za su habaka kasashen Eurasia, amma bambancin fifikon sha'anin tsaro ne babban kalubalen da suke fuskanta a tsakaninsu.