Burkina Faso, Mali da Nijar sun balle daga ECOWAS a watan Janairun 2025. / Hoto: AFP

Daga Mubarak Aliyu

A ranar 29 ga Janairu, 2025, Mali, Burkina Faso da Nijar - da a yanzu suka hade karkashin Kawancen Kasashen Sahel (AES) - suka sanar a hukumance sun fice daga Kungiyar Rayar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), wanda hakan ya zama babban sauyi a fagen siyasar yankin.

Wannan ballewa ta ba zata na bayyana al'amarin da ya fi na rikicin diflomasiyya girma, na bayyana tsananin damuwa game da kawancen tsaro da dogaron tattalin arziki, da 'yancin kan siyasa.

Sai dai kuma, akwai kalubalen da ke tafe a yayin da dukkan bangarorin ke duba mai zai je ya komo.

Daga makomar 'yancin juya kudade a yankin zuwa alakar kasuwanci da kawancen tsaro mai rauni, tasirin ballewar AES na iya sauya fasalin makomar hadewar Yammacin Afirka.

Tambaya kan kudin CFA

Neman wani sabon tsari zuwa 'yancin juya kudade na iya zama mai muhimmanci ga zaman lafiyar AES da ECOWAS.

Karfin fada a jin Faransa kan harkokin tattalin arzikin Yammacin Afirka na fitowa karara a yadda take kla d akudin CFA - kudin da kasashen Afirka rainon Faransa da dama suke amfani da shi a yankin.

Faransa na yin karfa-karfa kn harkokin kudi a kasashen da ta yi wa mulkin mallaka tare da juya manyan bankunan kasashen.

Ana bukatar Babban Bankin Kasashen Yammacin Afirka (BCEAO) da Babban Bankin Tsakiyar Afirka (BEAC) da su saka kashi 50 na kudaden ajiyarsu a kasashen waje a Baitulmalin Faransa.

Wannan shiri ya bawa Faransa cikakkiyar damar yin yadda ta ga dama kan sha'anin juya kudaden da irin ribar da suke samarwa.

Tun da an ayyana CFA ta zama Euro, karfin darajar kudin ya sanya kai kaya zuwa kasashen yake da arha, kuma babu gogayya wajen fitar da kaya zuwa waje daga kasashen.

Tsarin ya sanya kasashen ECOWAS da AES zama masu kai kaya d ake da rahusa zuwa masana'antun Faransa, wanda ke kara girman dogaro kan kasar, sannan ana rage karfin kananan masana'antunsu.

A baya, ECOWAS ta yi yunkurin samar da kudi na bai daya da ake kira Eco ga kasashen Yammacin Afirka.

Sai dai kuma, an dinga dage lokacin kaddamar da Eco din tun bayan bayar da shawarar samar da shi kusan shekaru 30 da suka wuce, kusan saboda rashin daidaiton tattalin arziki, takaddamar siyasa, da matsin lamba daga kasashen waje.

Duba da yadda nuna adawa ga Faransa ya zama dalilin da shugabannin AES ke dogaro da shi, tambayar da ta rage ita ce ta yaya wadannan kasashe uku (Mali, Burkina Faso da Nijar) za su samar da mafitar tattalin arziki da za ta kori CFA?

Matsalolin yankunan

Samun damar zuwa ga gabar tekuwata damuwa ce ga kasashen AES - tun da Burkina Fasi. Mali da Nijar kasashe ne da ba su da iyaka da teku, dukkan su ukun sun dogara kan makotansu da ke da iyakar tekun daon samun damar isa ga ruwan.

Wannan dogaro kan wata kasa na sanya su zama masu rauni wajen daukar matakan siyasa da tattalin arziki, wanda zai iya kawo matsala a hanyoyin kasuwanci kuma hakan ka iya janyo tsaikon kaiwa da komowar kayayyaki.

Bayan ficewar su daga ECOWAS a hukumance, kasashen biyu sun shiga tattaunawar bayan ballewa don tabbatar da tsarin ci gaba da kulla alakar kasuwanci da kawance.

Duk da cewa ECOWAS ta baiwa kasashen uku damar wucin gadi ta yin kasuwanci ba tare da tsangwama ba da 'ya'yanta, har yanzu ba a gama tantance yadda a nan gaba bangarorin za su dinga mu'amala ba.

Hadin kan samar da tsaro

Hadin kan tsaro a yankin Sahel da Tafkin Chadi ya shiga halin rashin tabbas duba ga yadda tsaron yankin ya dogaro kan Dakarun Hadon Gwiwa na Kasa da Kasa (MNJTF).

MNJTF da aka kafa don yaki da Boko Haram a Gabar Tafkin Chadi, dakarun na karkashin jagorancin Nijeriya da Nijar, Chadi, Kamaru da wani dan adadi daga Benin.

A yayin da Chadi da Kamaru ke wakiltar Tsakiyar Afirka, ECOWAS ta taka rawa sosai wajen tallafa wa MNJTF wajen yaki da ta'addanci a kan iyakokinta.

Sai dai kuma, rikicin diflomasiyya tsakanin Nijeriya da Nijar bayan juyin mulkin Nijar a watan Yulin 2023, ya janyo an kulla yarjejeniyar ayyukan tsaro a tsakanin kasashen AES.

Tun wannan lokacin, Nijar ta ja da baya wajen bayar d agudunmowa a ayyukan MNJTF, wanda ke bayyana matsawa daga yunkurin da Nijeriya ke yi.

Duk da cewa ayyukan baya bayan nan tsakanin shugabannin sojin kasashen biyu na nuni da yiwuwar sake hada kai, kuma rawar da ECOWAS ke taka wa wajen dawo da zaman lafiya a yankin Sahel da Tafkin Chadi na kan daidaituwa.

Hangen nesa da neman mafita

Duk da tshin tashinar da ke akwai sakamakon rarrabuwar ECOWAS, habakar hadin kan diflomasiyya na bayyana makoma ga wannan yanki.

A Taro Kashi na 5 na Taron Gwamnonin Jihohin Gabar Tafkin Chadi da ake yi kwanan nan a Maiduguri, Nijeriya, an jaddada niyyar karfafa MNJTF don yaki da Boko Haram, ISWAP da sauran barazononin tsaro a matakin yanki da kasa da kasa.

A gajere da matsakaicin zango, akwai yiwuwar mu ga kasashen AES su fita daga masu amfani da kudin CFA, don tabbatar da rabuwa da 'yar mulkin danniya Faransa baki daya.

Ga ECOWAS, duk da cewa kudin Eco bai yi nasarar wanzuwa ba, shi ne dai hanya mafi saukin yiwuwar samun mafita ga zaman lafiyar siyasa, cin gashin kan sarrafa kudade da hadewar ayyukan tattalin arziki.

Yadda ECOWAS ke dabbaka manufofinta na kasashen waje kan Faransa abin dubawa ne, a yayin da ake ta warware yarjejeniyar ayyukan soji tsakanin Faransa da kasashe mambobin ECOWAS din.

Dole ne kungiyar ta rungumi tsari na bai daya da zai tabbatar da kubuta daga kangin faransa don su samu 'yancin ayyukan tattalin arziki da tsaro.

Dole ne wannan manufar ta kasashen waje ta zama mai cikakken iko da kuma samun hadin kai, saboda dukkan biyun na da muhimmanci wajen kare yiwuwar afkuwar rikici a tsakanin mambobin ECOWAS.

Mubarak Aliyu mai nazari kan siyasa, kuma marubuci ne da ke mayar da hankali kan Yammacin Afirka da yankin Sahel. Batutuan da yake tabo wa sun shfi shugabanci da cigaba mai tafiya da kowanne bangare.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.

TRT Afrika