Daga Amanda Gelender
An raine ni tare da matuƙar shauƙin son al'adun Yahudanci. A matsayina ta farar fatar Bayahudiya jinsin Ashkenazi daga garin California mai ƙarancin Yahudawa sosai, an koya mini na dinga alfahari da asalina da al'ummata ta gada daga iyaye da kakanni.
A wajen ibadar Yahudawa da nake halarta, ina jin daɗin kaɗe-kaɗe, da nazarin littafin Attaurah, da yi wa jama'a hidima, da addu'a da kuma abinci. Ina lulluɓe da ni'ima.
A duniyata, nuna ƙauna da koyon wani abu game da Isra'ila wani ɓangare ne na jin mutum shi cikakken Bayahude ne. An koyar da ni cewa bayan kisan ƙare dangin Holocaust, Yahudawa na buƙatar wani wuri da za su tsira.
Saboda haka, cikin karamci sai aka miƙa wa Yahudawa halattaccen matsuguninsu na asali: Isra'ila, sahara fayau, babu mutane babu albarkatu. Kirarin da muka koya shi ne: "Ƙasa mara jama'a ta jama'a marasa ƙasa".
Shafe tahirin Falasdinawa da ake yi yana tsorata ni matuƙa.
Wannan ita ce irin aƙidar kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa da aka cusa a tunanin matasan Yahudawan Amurka bayan yaƙin duniya na biyu: Isra'ila ƙasa ce da babu ruwanta kuma mai daraja da take da matuƙar muhimmanci mutanenmu su ba ta kariya.
Domin sama wa matasan Yahudawa wata hanyar da za su bayar da gudunmawa wajen cim ma burin shirin kama-wuri-zauna, shirin na kafawa da kare ƙasar Yahudawa ya sa mun ji kamar muna bayar da gudummawa ce wajen bunƙasa ƙasar Yahudawa mai tatata.
Alal misali, magabatana sun koyar da ni cewa Isra'ila fayau take kuma cikin matuƙar buƙatar albarkatu da sai mun bayar da gudunmawar sulalla a matsayin sadakar tzedakah domin taimakawa a shuka bishiyoyi a Isra'ila.
Babu tattaunawa, musamman, game da tuge bishiyoyin Zaitun na Falasdinawa.
Gudunmawarmu ga biyayyarmu ga Isra'ila a bayyane take tsawon lokacin tasowarmu a matsayin Yahudawa. Alal misali, " tafiye-tafiyen birthright trips."
Waɗannan wasu tafiye-tafiyen yawon buɗe-ido na farfaganda ne, waɗanda gwamnati da masu zaman kansu ke ɗaukar nauyi, domin duk wani Bayahude a duniya ya ziyarci "ƙasarmu ta asali" ta Isra'ila.
Ana ɗaukar nauyin Yahudawa a tafiyar ta tsawon kwana goma kyauta zuwa Isra'ila, inda ake ƙarfafa Yahudawa su gana da abokanai da kuma waɗanda za su aura yayin da suke more alfarmomin ƙasa mai nuna wariyar launin fata.
Ƙungiyoyi suna ɗaukar nauyin hutun cin-amarci na Yahudawa ma'aurata a Isra'ila, da fatan za su yi ƙaura zuwa Isra'ila, su zauna da iyalinsu a matsayin ƴan kama-wuri-zauna a Isra'ila.
A matsayinmu na Yahudawa, mun fahimci cewa, komawa da zama Falasɗinu da aka mamaye wani kyakkyawan aikin sake haɗewa da asalin gadonmu na Yahudanci ne, kuma haƙƙinmu ne.
Wannan wankin ƙwaƙwalwar, haɗi da amfanin da Isra'ila ke bai wa Yahudawa ƴan kama-wuri-zauna, ya ƙarfafa ƙaurar ƴan kama-wuri-zauna sama da rabin miliyan zuwa West Bank, matsugunan da haramtattu ne a ƙarƙashin dokokin duniya.
Tabbas bai zama da mamaki ba, cewa tasirin aƙidar kafawa da kare ƙasar Yahudawa ba ta taƙaita ga wani ɓangare na al'ummar Yahudawa ba kaɗai: Aƙidar kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa abu ne da ya zama ruwan dare a kowane wurin ibadar Yahudawa da kuma cibiyoyin raya al'adun Yahudawa a faɗin duniya.
Wurin ibadar Yahudawa ɗaya tilo da na sani da yake da aƙidar adawa da kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa yana Chicago ne.
A wurin ibadar Yahudawa da na halarta lokacin ina tasowa, bukukuwan hutun Yahudawa na dauri kamar Passover ana cakuɗa su da sabbin bukukuwa kamar ranar samun ƴancin kai na Isra'ila wanda daga bisani na fahimci ya siffantu da Nakba.
Duk da Yahudanci a matsayin addini da al'ada ya shafe dubun-dubatar shekaru, amma a ƴan shekaru 75 aƙidar kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa ta yi nasarar jaddada asalin jinin Isra'ilaci a kowanne ɓangaren rayuwar Yahudawa ƴan Amurka.
Wannan aƙida ta kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa batu ne da babu wanda ya isa ya tanka a kansa a al'ummar da Yahudawa ne masu gagarumin rinjaye. Babu wata dama ta yin adawa da aƙidar kafawa da kare ƙasar Yahudawa.
Haƙiƙanin aƙidar kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa ba ta bayyana mini ba sai da na fara zuwa kwaleji kuma wani ɗan'uwa Bayahude ya yi mini bayani game da haƙiƙanin halin da ake ciki a Falasdinu. Kafin wannan lokacin, na yarda da duk abin da al'ummata ta koyar da ni:
Cewa Falasdinu a kowane irin nau'i mai aƙidar ƙyamar Yahudawa ce kuma ta kasance barazana. Har ila yau, duk wanda ya soki Isra'ila bai fahimci yaya ake ji idan aka musguna wa mutum a matsayin Bayahude ba.
Wannan shi ne karon farko da na ji Bayahude ya ba ni labari dalla-dalla kuma tsakani da Allah game da Isra'ila, na kaɗu kuma na ji kunya cewa ya ɗauke ni iya tsawon wannan lokacin kafin na gano gaskiya.
Wasu ma da dama sun fara fahimta su ma. Biyo bayan hare-haren kisan kiyashi na baya bayan nan a Gaza, kama-karyar da Isra'ila ke yi, ya yi ƙamarin da ƙasashen yamma ba za su kau da kai a kai ba.
Duk da yunƙurin da ake kan yi na yin tarnaƙi da hana ruwa gudu. Muryoyin Falasdinawa sun kutso waje kuma zalincin Isra'ila ya bayyana a idon duniya, ƙarara a gabanmu kowa ya gani.
Yahudawa na sauraron muryoyin Falasdinawa fiye da yadda suka taɓa ji a baya, suna matuƙar nuna yarda da aminci ga jajirtattun ƴan jarida da ke filin daga kamar Bisan Owda, suna duba kafofin sada zumunta don ganin sabbin labarai da take wallafawa game da tsaron lafiyarta.
Hatta masu aƙidar kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa tsawon rayuwarsu sun fara ɗiga alamar tambaya game da manufofin Isra'ila bayan sun shaida irin wannan mummunan tashin hankali, suna fahimtar cewa kashe dubban ƙananan yara a gidaje, da makarantu, da asibitoci da dalolin masu biyan haraji na Amurka ba zai kai ga samun tsirar Yahudawa ba.
Yayin da duk waɗannan al'amurra masu cike da tarihi ke faruwa, Yahudawa da yawa suna farkawa daga tsananin shagaltuwarsu da aƙidar kafawa da kare ƙasar Yahudawa.
Su yarda da abin da ke faruwa a yankin Falasdinawa da aka mamaye zai iya haddasa wani tunani mai zurfi game da tarbiyyar Yahudanci da aka raine su a kanta.
A matsayinmu na ƙananan yara, shugabannin addininmu, da iyalai da al'ummomi da kuma magabata, waɗanda suka ɓoye batun kisan ƙare dangi don su halasta kafuwar ƙasar Yahudawa, sun sharara mana ƙarya.
Masu adawa da aƙidar kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa kamar ni ana ɓata mana suna, a yi mana barazana, sannan masu son ci gaba da shirga ƙaryar da ita ce Isra'ila, suna katse mana hanzari.
Sun zarge mu da tsanar ƴan'uwanmu Yahudawa abin da shi ne kai tsaye kishiyar matsayarmu. A kyawawan ɗabi'u na Yahudawa kamar Tikkum Olam ("a gyara duniya").
A wajena, hakan, har ila yau, yana daga cikin kyawawan dabi'un Yahudawa da na tashi da su: fitowa fili ka soki rashin adalci ko da kuwa ba haka mafiya rinjaye ke so ba.
Ina alhinin mutuwar ruhin sanin ya kamata na addinin Yahudanci, wanda ya nashe, sannan ya zama kishin ƙasa mai cike da tashin hankali na aƙidar kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa.
Bugu da ƙari, ina jajanta wa kowane Bafalasdine, wanda ya mutu ƙarƙashin fakewa da kare Yahudawa.
A matsayinmu na yahudawa masu sukar lamirin aƙidar kafawa da kare ƙasar Yahudawa, muna kira ga magabatanmu waɗanda suka san tashin hankali kisan kiyashin, da makaman sojoji da kuma muzanta bil adama, da su ƙi amincewa da wannan kisan kiyashin.
Batu zaman lafiyar Yahudawa shi ne zaman lafiyar kowa na ɗamfare ne da ƴantacciya kuma sakakkiyar ƙasar Falasdinu.
Mawallafiyar, Amanda Galender Bayahudiyar Amurka ce da ke adawa da aƙidar kafawa da kuma kare ƙasar Yahudawa da ke zaune a Netherlands. Ɗaya ce daga cikin ƴaƴan ƙungiyar da ke goyon bayan Falasdinawa tun 2006.
Hattara Dai: Ra'ayoyin da mawallafiyar ta bayyana ba dole ba ne ya dace da ra'ayoyi hange da kuma manufofin tace labarai na TRT AFRIKA.