Daga Dennis Amachree
Za a iya cewa garkuwa da mutane ta samo asali ne tun zamanin mulkin mallaka, inda sarakunan suke aikawa a sato musu mutanen wasu garuruwa ko kuma a kama gurbatattun cikinsu domin a sayar da su, su zama bayi.
A shekarar 2006, lokacin ina aiki a Nijeriya a wani kamfanin man fetur da iskar gas a yankin Neja Delta, na hadu da 'yan bindigar yankin, inda na je domin tattaunawa a kan fansar wani Bature da suka yi garkuwa da shi.
Yanzu matsalar ta yi kamari, inda ta hade da tabarbarewar tattalin arziki da rashin adalcin da suka yi wa kasar katutu.
Yanayin tsaiko da juyin mulki ya rika kawo wa dimokuradiyyar kasar, da Yakin Basasar wata 30 da aka gwabza, sun taimaka wajen yawaitar makamai a kasar.
Tabarbarewar tattalin arzikin kasar ta hai har wadanda suka kammala digiri da dama da ba su samu aikin ba, ana yaudararsu cikin sauki su dauki makamai. Wannan ya sa harkokin ta'addanci suke yawaita.
Talauci da rashin aikin yi da bambancin da ke tsakanin masu kudi da talakawa ya taimaka wajen ingiza wasu su fara garkuwa da mutane domin samun kudi.
Ratar da ke tsakanin masu kudi da talakawa a Nijeriya tana da fadi sosai, inda wasu 'yan kalilan ne da iyalansu suke juya arzikin kasar, wanda hakan ya sa ake harin masu arziki da iyalansu, a yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa mai yawan gaske.
Abubuwan da ke jawo matsalar
Wata matsalar da ke addabar mutanen kasar da ma masana bangaren tsaro ita ce raunin bangaren tsaro da shari'ar kasar.
Rashin katabus na jami'an tsaron da tafiyar hawainiyar bangaren shari'a sun taimaka wajen hana magance matsalar ta garkuwa da mutane.
Rashin kamawa tare da hukunta masu garkuwar ne yake kara karfafa gwiwar masu sha'awar "sana'ar" abin mamaki, yanzu garkuwa da mutane ta zama ruwan dare, inda wani lokacin a kan kama yaran masu kudi da suka kitsa garkuwa da kansu domin a karba kudin fansa daga wajen iyayensu ko 'yan uwansu.
Matsalar ta ta'azzara ne saboda karuwar matsalolin da suke jawo ta. Daya daga cikin matsalolin ita ce cin hanci.
Saboda yawaitar talauci da rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa, yanzu garkuwa da mutane ta zama hanyar samun kudi
Bibiya da kula shiga da fitar mutane
Tunanin samun kudin fansa yana cikin karfin gwiwar da suke samu, musamman a kasar, wadda hanyoyin samun kudi suka takaita ga mafi yawan 'yan kasar.
Yawaitar kananan makamai a Nijeriya, wanda bai rasa nasaba da rashin ingantattun boda a kasar, da yake-yake a yankunan da suke makwabtaka da kasar, sun taimaka wajen yawaitar harkallar.
Kungiyoyi kamar su Boko Haram a yankin Arewa mason Gabas da kungiyoyin 'yan bindiga da dama na yankin Neja Delta da kuma 'yan bindiga na yanzu suna amfani da garkuwa da mutane domin samun kudaden shiga domin gudanar da harkokinsu.
Yanzu kuma 'yan bindiga da ke yankin Arewa maso Yamma sun gano akwai ma'adinai a karkashin inda suke zaune, sannan suna amfani da wadanda suke garkuwa da su a matsayin leburorinsu wajen hako ma'adinai.
An yi sakwa-sakwa da tsare-tsaren shugabancin unguwanni wadanda a da da su ake amfani wajen kula da shiga da fitar mutane. Sakacin nan ya taimaka wajen rashin kula da shiga da fitar mutane da kula da masu aikata laifi.
Yanzu sarakunan gargajiya ba su da karfi. Yadda ake samun makudan kudaden a garkuwa da mutane ya sa wasu bata-garin suke tururuwar komawa harkallar, inda suke ganin za su kudance cikin kankanin lokaci.
Rikice-rikicen da ke wakana a yankuna da dama na Arewa sun kara yawan wadanda aka raba da muhallansu. Wadannan mutanen sun fi fuskantar barazanar sacewa cikin sauri.
Tattara bayanan sirri
Boko Haram suna daukar 'yan gudun hijira aiki ta bayan fage. A cikin birane kuma, ci gaban da ake samu da fadadar biranen sun sa mutane na ta kara shigowa, wanda hakan ya sa sa ido a kan mutane ya yi karanci, wanda hakan ya sa masu garkuwar ke samun saukin bacewa cikin mutane.
Wadannan matsalolin, ko dai ga daidaikun mutane ko al'umma baki daya, sun taimaka wajen yawaitar garkuwa da mutane a Nijeriya. Magance matsalolin kuma suna bukatar bin hanyoyi da dama, ciki har da karfafa jami'an tsaro.
Hanyoyin sun kunshi karfafa tattara bayanan sirri. Sai dai kuma rashin kayayyakin aikin tattara bayanan sirri , yana kawo tsaiko ga aikin jami'an tsaron wajen bibiya tare da kama masu garkuwar cikin sauri.
Rage harkokin masu garkuwar nan na bukatar hadin gwiwa ne tsakanin gwamnati da al'umma, da inganta tattalin arzikin kasar da kuma neman hadin kan kasashen waje.
An sha yin alkawura a shekarun baya cewa za a inganta aikin dan sandar Nijeriya, inda har wasu masana suke ganin akwai bukatar kafa 'yan sanda na jihohi. Amma da alama kawai zakin baki ne.
Karfafa gwiwar mutane suna shiga harkokin tsaron yankunansu yana da matukar muhimmanci, domin duk wani rashin daidai da aka aikata a yankin ba zai boyu ba. Haka kuma za a samu saukin wayar da kan mutane hanyoyin kare kansu.
Idan aka inganta tare da karfafa ayyukan 'yan sanda da sauran jami'an tsaron wajen yaki da matsalar garkuwa da mutane, za a samu sauki sosai a matsalar.
Dokoki masu tsauri
Dokokin za su kunshi bayar da horo mai inganci, kara yawan jami'an tsaron da inganta hanyoyin tattara bayanan sirri da kuma amfani da fasahar zamani. A bangaren gwamnati kuwa, akwai aiki babba.
Niyyar aiwatar da aikin da gaskiya tana da muhimmanci, sannan ya kamata a yi yaki da cin hanci a tsakanin jami'an tsaro da bangaren shari'a na kasar idan ana so a yaki da matsalar garkuwa da mutane.
Haka kuma yana cikin aikin gwamnati ta samar da hanyoyin tallafa wa mutane domin rage ratar da ke tsakanin masu kudi da talakawa.
Haka kuma akwai bukatar a samar da hanyoyin tallafa wa iyalai da 'yan uwan wadanda abin ya shafa, wanda hakan zai sa su ba jami'an tsaron hadin kai domin gudanar da bincike.
Ba za mu magance asalin matsalar laifuffuka ta hanyar samar da aikin yi ba kadai, musamman ga matasa.
Samar da hanyoyin tallafa wa marasa karfi zai taimaka wajen rage sha'awar samun kudi ta hanyar garkuwa da mutane.
Sannan za a karfafa wannan tsare-tsaren ne idan aka tanadi hukunci mai tsauri a kan masu garkuwa da mutane da sauran laifuffuka masu kama da ita.
Matsala mai wahalar sha'ani
Dole a sauya tunanin matasa na cewa ana samun kudi a harkar garkuwa da mutane. Na dade ina cewa akwai bukatar a kafa bangarorin tsaro na musamman masu yaki da garkuwa da mutane kamar Special Weapons and Tactics wait SWAT, sannan a samar musu da kayan aiki sannan a ba su horo na musamman.
A karshe, hadin gwiwar kasashen waje musamman kasashe makwabta da kungiyoyin duniya domin magance garkuwa da mutane a tsakanin kasashe makwabta yana da matukar muhimmanci a yaki da matsalar.
Matsalar garkuwa da mutane tana da wahalar sha'ani, sannan dadaddiyar al'ada ce da take da tarihi.
Matsalar ta kara nuna matsalolin da Nijeriya ke fuskantar a matsayinta na kasa mai tasowa.
Idan aka dabbaka wadannan shawarwari, sannan aka samu tsari mai kyau, za a rage kaifin harkallar sosai a kasar.
Matsalar tana bukatar dagiya da hadin kan kowane bangare, ciki har da gwamnati da jami'an tsaro da al'umma da kasashen duniya.
Marubucin, Dennis Amachree, tsohon darakta ne a Hukumar DSS da ya yi ritaya, kuma masanin tsaro.
Togaciya: Ra'ayin marubucin ba dole ba ne ya yi daidai da ra'ayi da dokokin aikin jarida na TRT Afirka.