Ranar 6 ga Satumban 2024 wani sojan Isra'ila gwanin harbi ya kashe Aysenur Ezgi Eygi a yankin Gaɓar Yamma da aka mamaye. Ba'amurkiya r'yar asalin Turkiyya tana da shekaru 26, kuma 'yar gwagarmaya ce da ta bar gadon yaƙi don kafa daidaito da 'yancin Falasɗinu da kafa adalci a duniya. (Hoto daga Saif Sharabati).

Na fara haɗuwa da Aysenur Ezgi Eygi ne a Mayun da ya gabata a wani sansanin ɗalibai masu zanga-zanga a Amurka. Mun tsaya a can don nuna goyon baya ga Falasɗinu kan kisan ƙare dangin da Isra'ila take yi a Gaza, muna Jami'ar Washington. A lokacin, Ayse ɗaya ce cikin masu jagorancin fafutukar ɗaliban.

Matashiyar Ba'amurkiya 'yar asalin Turkiyya ta tsayu kan kafa adalci ga Falasɗinawa, da gwagwarmaya a jami'a tsawon rayuwarta.

Yayin da rayuwa ta haɗa mu wajen fafutukar neman 'yancin Falasɗinawa, Ayse da na sani jaruma ce, mai kirki da juriya. Matar mai shekaru 26 tana da sakin fuska, da tarin abokai, kuma tana da fara'a da haba-haba.

Ayse kullum a shirye take ta taimaki mutane da duba damuwar abokanta don jin yadda suke, sannan ko suna buƙatar taimako kan wani abu, ko da kuwa tana cikin aiki.

Daidaito tsakanin al'umma

Cikin sanannun halayenta, ina tuna ƙarfin halin Ayse. Tana da faran-faran kuma tana ƙoƙarin sanya mutane farin ciki. Amma tana da halin mayar da hankali idan aka zo batun gwagwarmaya.

Ranar 6 ga Satumban 2024 wani sojan Isra'ila gwanin harbi ya kashe Aysenur Ezgi Eygi a yankin Gaɓar Yamma da aka mamaye. (Hoto daga Saif Sharabati).

Kyawawan halayenta sun haɗa da ba da lokaci wajen haɗa taruka. Ayse tana ƙaunar Falasɗinawa matuƙa, kuma ta taka babban matsayi wajen shirya zaman dirshan a jami'a, inda ta haɗa gwiwa da ɗalibai da jagororin jami'a.

Ta cim ma wannan nasara yayin da take karatu a matsayin ɗaliba, inda ta yi aiki tuƙuru wajen samun kyakkyawan sakamako inda a ƙarshe ta kammala Jami'ar University of Washington.

Ayse mace ce da ta yi imani da adalci yana nufin yaƙi don ɗaukaka batun Falasɗinawa, da kuma yaƙi don kawo daidaito ga kowa.

Rayuwarta a matsayin matashiya 'yar gwagwarmaya, mai himma kan abin ta yi imani da shi, ta kasance mai tafiye-tafiye a ƙasashen duniya. A 'yan shekarun baya, ta je Myanmar don duba kisan ƙare dangin da aka yi wa al'ummar Rohingya a Kudu maso gabashin Asiya.

A Amurka, a garin Seattle, wanda nan ne garinta tun bayan barin garin Antalya na Turkiyya tana ƙarama, Ayse ta kasance cikin harkokin neman adalci game da launin fata, inda ta shiga fafutukar kamfe ɗin Black Lives Matter (BLM), da sauransu.

Ranar 6 ga Satumban 2024 wani sojan Isra'ila gwanin harbi ne ya kashe Aysenur Ezgi Eygi a yankin Gaɓar Yamma da aka mamaye. (Hoto daga Saif Sharabati).

Ayse tana da matuƙar dattaku; saboda kullum tana abun daga zuciyarta kuma da nuna soyayya, ko a wane hali. Ina tuna yadda Ayse take son rayuwa cikin annashuwa do kishin karatu do yankin Gaɓar Yamma da aka mamaye.

Ziyarar Gaɓar Yamma

Ayse tana da matuƙar karsashin zuwa can, don ganewa idonta zahiri rayuwar da Falasɗinawa ke ciki bayan fuskantar mamayar sojojin Isra'ila tun 1967 a Gaɓar Yamma da kuma kisan kiyashin da ya biyo baya.

Tun da Isra'ila ta tsananta kai hari kan Falasɗinawa a Oktoban bara, sojojinta suk kashe sama da mutum 41,000, yawancinsu mata da yara. Yayain da take Gaɓar Yamma, Isra'ila zuwa yanzu ta kashe kusan mutane 700 nkuma ta jikkata sama da mutum 5,700.

A wannan yanayi, lokacin mu'amalarmu tare, Ayse ta sanar da ni yadda mahaifinta da wasu malaman jami'a suka nuna tosor kan kasancewarta a can.

Amma tana da ƙwarin gwiwa da ƙarfin hali. Ayse tana son zuwa Gaɓar Yamma don nuna goyon baya ga Falasɗinawa kan mamayar da aka musu. Ta je ganin yadda suke rayuwa suma ta ci gaba da turo saƙonni ga duniya - wani labari da ake yawan saka wa takunkumi.

Ayse na sane da haɗarin, amma tana son zuwa don ta nuna cewa tana tare da al'ummar Falasɗinawa da ake wa kisan kiyashi a Gaza yayin da duniya ke zura ido.

Dalilin da ya sa ta je tare da sauran masu fafutukar kawo zaman lafiya daga ƙungiyar the International Solidarity Movement (ISM) shi ne don ci gaba da aika saƙonnin nuna gaskiyar lamarin da mamayar Isra'ila da zaluncinta ga duniya.

Wayata ta ƙarshe da Ayse ta kasance 'yan awanni kafin a kashe ta. Ina tare da ita kan waya tsawon sama da awa biyu.

A wannan lokaci, na ji Ayse tana magana kan batun daga zuciyarta. Ta gaya min yadda mamayar ta ƙazanta da yadda rayuwa take da wahalar, kamar yadda iyalai Falasɗinawa kamar nawa suke fama. An kama ni a can a baya, jami'an farin kaya sun kama ɗan uwana. Mahaifina ma an kama shi har ma aka harbe shi a ƙafa a baya.

Rayuwa cikin mamaya

A faɗin Gaɓar Yamma da aka mamaye har zuwa masallaci mai tsarki na Jerusalem, da tafiya cikin shigayen bincike, za ka ji kamar kana rayuwa tsakiyar haɗari da wariya.

Falasɗinawa da dama suna shan harbi da kisa ba don sun yi komai ba. Abokaina Falasɗinawa sun sha wahalar wannan, yayin da aka zagaye su da shingayen bincike, da barazana ga gidajensu da hana su ko baƙinsu shiga ko fita daga al'ummar. Da yawa suna kuma fuskantar rashin adalci na jiran awanni.

yayain ganawarmu a waya, Ayse ta ba ni labarin da ta ji daga mazaunan wajen da wahalhalun da mamayar ta haifar garesu.

Mun kuma zanta kan mu'amalarta a Jerusalem da yadda sojojin Isra'ila suka ƙi barin ta shiga Masallacin Qudus mai tarihi.

Kuma ta fuskanci matsanancin yanayin mamaya wanda a kullum Falasɗinawa suke fama da shi. Ta gaya min game da yadda Isra'ila ta karɓe fasfo ɗinta a kan iyaka, inda suka sa ta jira tsawon lokaci inda suka mata tambayoyi game da tafiyarta kafin daga bisani suka bar ta ta wuce.

Babban batun da ta tattauna kai shi ne wahalhalun al'ummar da ke ƙarkashin mamaya, duk da zamanta a can na 'yan kwanaki ne.

Gado

Kafin mutuwarta mai firgici, Ayse ta yi shirin haɗuwa da dangina a birnin Hebron bayan 'yan kwanaki, amma hakan bai faru ba.

Za mu tuna da Ayse, wadda ta rayu don kafa adalci da 'yantar da Falasɗinawa har zuwa rasuwarta. ba za mu manta da ita ba. Duniya ba za ta taɓa mantawa da ita ba, kuma za mu ci gaba da yaƙin kawo ƙarshen mamaya.

Za mu ci gaba kan tafarkin da ta bari don ɗaukaka saƙonta na adalci da daidaito har sai duniya ta samu kyakkyawan sauyi.

Gadon da Ayse ta bari shi ne haɗa kan jama'a. Don tunawa da ita, masu haɗa taruka da ƙungiyoyin fafutukar kafa adalci za su yi aike tare don kawo sauyi ko da hakan ya zama mai wahala, kasancewar Ayse ta san da wahalar amma ta zaɓi bin tafarkin.

TRT Afrika