Daga Airlin Pérez Carrascal
A tsakanin 1534 da1850, kimanin mutane miliyan 12 ne aka yi garkuwa da su a Afirka, aka muzanta su sannan aka kai su 'Sabuwar Duniya" da ake kira Amurka, wadda 'yan mulkin mallaka na Yammacin Duniya suka kafa don tabbatar da ci-gaban masana'antu da tsarin jari hujja a Turai.
Kafin wannan lokaci, Turawan mulkin mallaka sun fara aikata kisan kiyashi a nahiyar Amurka tare da jama'ar yankunan, suna karar da jama'arsu masu yawa.
Kisan gilla da dama, tursasa aikin karfi da gudun hijira sun zama halastaccen abu ta hanyar assasa bambanci matsayin kabila-launin fata -- da manufar mallakar kadarori daga hannun bakaken fata da jama'ar asalin yankin.
An yi hakan ne da manufar tuhumar matsayinsu na 'yan'adam, a mayar da su wasu injinan aiki d araba su da al'adu da asalinsu.
Irin wannan abu na ci gaba da faruwa tsawon shekaru sama da saba'in a Falasdinu, yayin da Isra'ila ke aikata kisan kiyashi ga Falasdinawa.
A tarihin Falasdinu, Isra'ila na aiwatar da manufar mamaya ta iyakoki da siyasa, da kuma dabbaka tsarin mulkin mallaka da cin zarafin dan adam, tare da kwace kasa da gonakin gadon kaka da kakanni, sannan suna amfani da karfin tattalin arziki, soji da siyasar danniya wajen ci gaba da cimma wannan manufa tasu.
Hadin kan adawa da 'yan mulkin danniya
Akwai alaka ta kai tsaye da kuma cin karo da juna tsakanin jama'ar asalin Afirka da ke Colombia a Latin Amurka da Caribbean da kuma jama'ar Falasdinawa.
Saboda wannan tarihi, dole gwagwarmayarmu ta neman 'yanci ta gina goyon baya mai karfi ga duk wasu jama'a da ake zalunta a fadin duniya.
Dukkan jama'ar sun nuna tirjiya ga mamayar 'yan aksar waje, sun yi gwagwarmayar tabbatar da 'yancin kan su, tare da bin tsarin hakkin kare kai sau da kafa.
Dadin dadawa, dukkan su tarihi ya nuna sun kalubalanci bayanan karya da mamaya na 'Gwagwarmayar yaki da tayar da zaune tsaye da ta'addanci" -- da manyan kasashen duniya na Amurka da Isra'ila ke yi, don karfafa kasuwancin makamai, mayar da kare kai ya zama ta'addanci, da kuma halasta kisan kiyashi, kai harin bama-bamai da karar da kabilu.
'Yan mamaya da danniya a Falasdin da Colombia sun kwace yankunan da ba nasu ba, suna kuma bayyana duk wanda ya nuna musu yatsa a matsayin makiyi mai in zagon kasa da aikinsu na mulkin mallaka da jari hujja.
Gwagwarmaya cikin hadin kai
Colombia na da 'yan asalin Afirka sama da miliyan 4.7. Goyon baya tsakanin 'yan asalin Afirka da ke Colombia da gwagwarmayar Falasdinawa na tunatar da kwakwale dubunnan bakar fata da aka kashe a Colombia ta hanyar sabon mulkin mallaka.
Wannan goyon baya na tunatarwa da nuna tirjiya ga rawar da gwamnatin Isra'ila da Amurka ke takawa a bala'o'in da muke fuskanta, musamman a 1980 bayan zuwan tsarin tsaronsu a Colombia.
Wannan sabon fasali na tsaro ya samu goyon bayan gwamnatocin masu tsaurin ra'ayi don kare manufarsu ta murkushe abokan adawa, da dukkan ayyukan adawar siyasa a kasar, wadanda suke da dangantaka a alakar Colombia da Isra'ila.
An dabbaka wadannan manufofi a yayin bayar da horo ga sojojin Colombia da dakarun Isra'ila ke yi.
Wannan alaka ta kuma bude kofar murkushe jam'iyyun siyasa irin su PU, sannan aka dinga haramta ayyukan kungiyoyin bakaken fata da ke Colombia, da kuma dabbaka alaka ta kai tsaye tsakanin kamfanonin tsaro na Isra'ila.
Rahotanni sun bayyana cewa sama da kashi 51 na kisan kai da aka yi a yayin rikicin da gwamnati ta sanya idanun afkuwarsa, an bayyana sojoji ne suka aikata su, kuma sun kashe shugabannin jama'a, malaman makaranta, da mambobin kungiyoyin fafutuka.
Gwamnatin Shugaba Alvaro Uribe Velez ta yi karin haske kan manufar tsarin "Tsaron Dimokuradiyya" karkashin tallafi da goyon bayan Isra'ila, wanda hakan ke nufin su ma su goyi bayan ci gaba da kasancewar jama'ar falasdinu karkashin zalunci da tauye hakkoki.
Ya kuma bayyana yadda a wasu yankunan, inda ake da bakaken fata da yawa 'yan asalin Afirka, irin su Uraba, Choco da wasu yankunan Caribbean, ayyukan sojin kasar da mayakan da Isra'ila ke goya wa baya suka zamto masu kwace gonaki da dazukan jama'ar Colombia don samar da kwakwar Afirka da suaran kayan marmari don amfanin masu hannu da shuni na kasar.
Irin wannan abu ne dai yake afkuwa a Isra'ila/Falasdinu, inda 'yan kama guri zauna na isra'ila ke kwace gonakin Falasdinawa na wadin Jordan, don su shuka kayan amfanin da za su ci, su fitar da wasu kasashen waje.
Dukkan 'yan asalin Afirka da ke Colombia da 'yan asalin kasar Falasdinu na fuskanta zaluncin tsarin mulkin danniya da mallaka.
Bakin ciki da hawayen bangarori daban-daban na cudanya da juna. Saboda haka, idan hawaye da zalunci suka tsallaka iyaka, to tirjiya ma za ta tsallaka zuwa wjaen iyaka.
Dole ne jama'ar Colombia 'yan asalin Afirka su ci gaba da kalubalantar kisan kiyashin da ake yi wa Falasdinawa, su kuma ci gaba da neman hakkokin bakaken fatar da aka yi wa kisan kiyashi a Colombia.
Marubucin wannan makala Airlin Pérez Carrascal, mamban Kungiyar Gwagwarmayar 'Yan Asalin Afirka a Colombia ne, kuma farfesa mai bincike da ya mayar da hankali kan yaki da mulkin mallaka da gwagwarmayar jama'a.
Togaciya: Ra'ayin da marubucin ya bayyana ba lallai ya zama sun yi daidai da ra'ayi ko manufofin dab'i na TRT Afirka ba.