Daga Pauline Odhiambo
A lokacin da Yvans Conde da ke Nairobi ya fara daukar matakin farko na zama telan zamani, ba ya iya sayen yadika sababbi don dinka kaya.
Karin maganar nan da ake cewa "Idan ba ki da gashin wance kar ki ce za ki yi kitson wance" ya zama mai hana matashin da ya zaku ya nuna bajintarsa; a saboda haka sai ya zabi hanya mai sauki da yake da ita.
Conde ya shaida wa TRT Afirka cewa "Ina daukar tsaffin zannuwan mahafiyata da 'yar uwata don gwada ko hikimata za ta yi aiki. Sake dinka su a hankali ya zama wani bangare na sana'ar dinkina."
A matsayin mai dinka kayan da za su iya dorewa, tunani da hangen nesan matashin dan shekara 28 bai samu cikas daga daukar matakin mayar da hankali ga kananan yadika a masana'antar da ake gasar kashe kudi a kanta.
Irin kayan da yake samarwa na da kyau da kayatarwa, suna kama da adon jikin dawisu sarkin ado.
A lokacin da Conde ya so saka wa kayansa suna, sai ya zabi "Tausi", wanda ke nufin dawisu a yaren Swahili na Gabashin Afirka.
Wannan na zuwa ne bayan shekaru da yawa a lokacin da ya samu labari daga kakarsa cewa sunan danginsa na "Conde" na nufin 'gashin dawisu" a yaren kasar Uganda.
"Tausi Conde" ya zama kamar maimaici, amma Conde kawai ya fi zama mai kamanta kayansa.
Tun bayan assasa wannan suna a 2017, Tausi Conde ya zama sunan da ake tunawa idan ana son ingantattun tufafi, wand aake wa kallon dawisu da kyawun dabi'a.
"Ina son mutane su sanya tufafin da na ke samarwa kawai don su ji dadi kuma su yi fice kamar dawisu," in ji shi.
Tufafi da ba sa illata muhalli
A yayin da amfani da sunan Conde ga kayan da yake samarwa ya yi daidai da sunan dangi da yake amfani da shi, bayan da abubuwa suka bude ya zama ba shi da kalubalen kudi, bai ajje sunan na Conde ba, ya ci gaba da amfani da shi.
"A yanzu ina sayen sabbin yadika, amma na zabi na dinga amfani da tsofaffi. Ina jin cewar abinda na ke yi na da amfani ga muhalli," Conde ya shaida wa TRT Afirka.
Wani shafi mai sunan 'State of Matter Apparel' da ke fafutukar ganin an samar da tufafi mai dorewa, kashi 95 na tufafi da ake zubarwa na iya koma wa sabo ko a gyara shi. Hakikanin gaskiya, kashi 15 na kayan sawar da ake zubarwa ne ake sake sabunta su.
Ana saka kananan tufafi kasa da sau biyar, ana ajje su na kwanaki 35, suna kuma samar da iskar carbon da kashi 400 a shekara sama da manyan riguna da ake saka su sau 50 kuma a tsawon shekara a ci gaba da amfani da su.
Conde ya ce kasancewar sa mai son kare muhalli, ya sake ba shi karfin gwiwar bin dokokin masana'antar dinka kayayyaki, wanda ake hasashen zai kai darajar dala biliyan $8.3 nan da 2025.
Dogayen riguna
Conde ya zama jagora wajen samar da tufafi ga Maisha da ke akrkashin Nisria, Maisha na nufin "rayuwa" a yaren Swahili.
"Daukar kayan da aka zubar a bola a mayar da su wani abu mai amfani, na da dadi matuka, saboda hakan na samar da rayuwa ga abinda ya tsufa," in ji Conde, wanda ke jagorantar masu tsara tufafi 10, teloli da dlibai.
"Duba da yanayin da ake ciki, muna samar da tufafi daga barguna, labulaye, ko wasu yadika da aka yi amfani da su da suke da amfani da yanayn da ake ciki."
An tsara sabon rukunin kayayyaki na Hayat na Conde, da manufar tallafawa jama'ar Gaza da Isra'ila ke yaka.
"Hayat na nufin rayuwa a Larabci, kuma kayan da aka samar a karkashin hakan na nuna muhimmancin sabunta kayayyali da haskaka kyawun rubutun larabci irin na Falasdin," in Conde.
Kayan na kuma girmama daya daga cikin wadanda suka kafa Maisha, wani dan asalin Falasdin da ya rasu ba da jimawa ba.
Abin koyi ga mutane da dama
Mafi yawan daliban da ke tare da tawagar Conde sun fito ne daga wannan yankin, daga ciki akwai 'ya'yan marasa abin hannu.
"Ana koyawa daliban tsara wa da zana salon tufafi, sanna ana dora su a kan hanyar koyon dinki," in sji shi.
Maisha mallakin Nisria kuma na taimaka wa jama'ar yankin ta hanyar bayar da abinci ga kananan cikin su da ke makarantu.
Conde ya ce tun daga makaranta ya samo kwadayin tallafa wa yara kanana da matasa, yana mai tina wa da lokacin da ya yi takara a gasar dinkin dalibai a Kenya.
"Na karanta tsara tufafi a Jami'ar Kenyatta kafin na dan tsaya don fara aiki da koyon dinki a aikace," in ji Conde yayin tattaunawa da TRT Afirka.
"Baje-kolin kayayyakina a wajen bukukuwan nuna tufafi da daban-daban a taimaka min wajen jan hankulan mutane."
Shwararsa ga masu sha'awar tsara tufafi da dinka su da ke taso wa ita ce da su amince da amfanin hadin kai. "Kar ku ji tsoron hotun su yi muku yawa, ku yi zane da kirkirar nau'ika daban-daban, ba za ku kashe kudi sosai ba wajen yin hakan, wanda zai ba ku damar tattara salon kayayyaki da yawa." in ji shi.
"Kawai ka zabi abu guda ka kware a kai, sannan ka mayar da hankali wajen gina hajarka. Daga baya kudi zai zo."