Daga Fathiya Bayusuf
Khanga ko Leso wani nau'in yadi ne shimfiɗaɗɗe da aka yi shi da auduga, kuma yana fitowa cikin launuka daban-daban da karin magana iri-iri cikin harshen Swahili rubuce a ƙasansa ɗauke da saƙonnin zamantakewa daban daban.
Ya zarce sutura kawai; wani nau'i ne na fasaha da ke nuni da al'adu da ƙawa, musamman tsakanin matan yankin Gabashin Afirka mai maƙwabtaka da teku.
Galibi suna zuwa ne a falle biyu, mata na ɗaura leso ɗin a ƙugunta yayin da take rufe kanta da falle na biyun - abin da ke samar da wata sifar al'ada da daraja ko a gida ko lokacin bukukuwa daban daban.
A wajen mata, leso na nuni da wani matsayi na girmamawa da nuna ƙauna daga mazajensu.
Tara suturar leso dayawa na nufin hakan ya zarce batun kyautata ado kaɗai, batu ne na bayyana so da ƙauna a cikin aure. "Suturar Leso daidai take da kayan ƙawa a wajen matar Swahili.
Duk lokacin da ta saka ta, ta kai wani matsayi na muhimmanci da ado. Ta wuce matsayin kayan tarihi da magabatanmu suka saka, musamman a salon Kisutu, wanda ya shahara a lokacin bukukuwa kamar aure ko bukukuwan al'ada," in ji misis Amira Msellem, wata mai bincike da ta ƙware a fannin ɗabi'u da al'adun Swahili a Mombasa.
Tushen ƙarni na 19th
An yi imanin cewa tarihin leso ya fara ne tun ƙarni na 19th, musamman a tsibiran Zanzibar, da Pemba da kuma Mombasa.
Tsawon lokaci, ya shahara tsakanin al'ummomin yankunan, abin da ya yi sanadiyar fitowarsu da ado masu alamomi dabam dabam.
Adon farko farko na dauke da adon fari da baƙi da ke nuni da launin wani tsutsu da aka fi sani da Kanga. A nan ne sunan "Khanga" ya shahara da kuma samun karɓuwa tsakanin mutane.
"Khanga na farko farko suna da adon fari da baƙi ne kaɗai, babu wani wani rubutu. Amma da tafiya ta tafi, sai aka inganta su da nau'o'in ado iri iri," Imran Abdul Haq, wani mai zanen adon leso a shagon Abdullah ya bayyana.
Tsawon shekaru, salon leso ya bunƙasa sannu a hankali, ya ƙunshi fasahar amfani da launuka da furanni da kuma hotunan abubuwan ban sha'awa kamar tsirrai da dabbobi.
A farkon ƙarni na 21, an ƙara rubutun Swahili, da karin magana da kuma maganganun hikima a jikin leso, abin da aka yi imanin ƙoƙarin ne na wani fitaccen ɗan kasuwa, Kaderdina Haji Isaack, wanda kuma aka sani da Abdulla, wanda ya kawo kasuwancin leso a Mombasa.
Imran Abdul Haq, mai yin zanen leso a Shagon Abdullah ya bayyana yadda kakansa ya yi nasara wajen bambanta hajojinsa, kuma ya ƙirƙiri wani daban da ake kira "Mali ya Abdulla".
"Mzee Abdulla shi ne ya ƙara rubutun Swahili a cikin zanen da ake yi wa leso kuma mutanen Mombasa sun so shi. Matan Swahili sai suka fara aika wa da saƙo ta hanyar rubuce rubuce a kan Suturar Khanga da suke sakawa.
Sakamakon haka, mun faɗaɗa kasuwancinsa daga Khanga zuwa wani makeken kanti da ke sayar da kayayyakin Afrika kamar kaniki, da vikoi, da vintege da saura," ina ji Imran.
Da farko, rubutun da ke kan leso, duk da a harshen Swahili ne, amma a harufan Larabci aka rubuta, sannan daga baya aka rubuta a harshen Romanci lokacin da karɓuwar Khanga ta yaɗu daga al'ummomi masu maƙwabtaka da teku i zuwa faɗin Gabashin Afirka.
Sai dai akwai banbanci tsakanin leso ɗan Kenya da ɗan Tanzania, Imran ya jaddada.
"An san Khanga ɗinmu na Mombasa da faɗi da nauyi da kuma ingancinsu, abin da ya sa mutane dayawa suke son su." Suturar Khanga ba kayan ado ba ne kaɗai, ta zamo wani cikakken ɓangare na al'adar Swahili kuma ana amfani da su a matsayin hanyar sadarwa.
Rubuce rubucen da ake a kansu suna nuni da ƙauna, godiya har ma suna isar da saƙon rashin jituwa.
"Matan Swahili sun fi son yin amfani da leso su isar da saƙo. Idan suka sayi wani yadin leso, suna zaɓan rubuce rubucen ne gwargwadon saƙon da suke son isarwa. Alal misali, Khanga da mata masu ɗanyen jego ke sakawa kan ƙunshi saƙon taya murna kamar "Maraba da zuwa Baƙo ko Na Gode Baba da Kika Rene Ni," a cewa Amira.
Amira ta ce, a baya can, ana amfani da leso wajen nuni da balagar ƴaƴa mata.
"Suturun leso suna zama kadara ga mata saboda ya zamo al'ada mata su mallaki suturun leso dayawa. Mata na mallakar leso a matsayin wata hanyar yin tanadi don magance matsalolin kuɗi ta hanyar sayar da su.
"Har ila yau, an yi amfani da leso wajen sadarwa tsakanin ma'aurata saboda wasu matan wani lokaci suna samun matsalar yin magana kai tsaye da mazajensu. Saboda da haka, matar za ta ninke leso ta hanyoyi dadama domin isar da saƙo ga mijinta. Ana amfani da wasu leso a bukukuwan aure, ko murnar ɗaukar juna biyu ko bukukuwan kaciya ko ma jana'iza. Mata har ila yau, suna amfani da leso su goyi yara ko kuma lokacin ibada.
"Leso na da matuƙar muhimmanci a wajen mace; kuma ma sutura ce ta mutunci kuma ana yawan amfani da ita wajen ibada, da hidimomin gida ko ma goya yara. Leso muhimmin ɓangaren rayuwar mutane masu amfani da harshen Swahili ne tun daga haihuwa har mutuwa."
"Idan mace ta haihu,wajibi ne ta sanya leso na tsawon kwanaki 40. Haka kuma ana amfani da su wajen renon yara ko ma maɗaukin jarirai da ake ɗaurewa a ƙasan gado.
Duk da sauye sauyen lokaci,leso na ci gaba da zama muhimmiyar sutura da ke nuna tsattson Afrika. Khanga na wannan zamanin ana ɗinka su a matsayin kayan gargajiya, a yi amfani da su a matsayin yadikan ado a bukukuwan aure da sauran bukukuwa na al'ada.
Har ila yau, an sanya leso a jerin kayan ado na duniya da ake yayi. Wasu mata sun riƙe gargajiyar saka leso a matsayin wata hanyar adana al'adunsu. yanzu ina amfani da leso a gida saboda wani ɓangare ne na asalina na matar Afrika.
Ina sayen su bisa la'akari da saƙon da nake son isarwa, don bayarwa a matsayin kyauta a bukukuwa dadama, kamar bukin tunawa da zagayowar ranar haihuwa, da aure ko ma kyauta ga iyayena," Kavira Neema, wata ƴar ƙasar Congo mazauniyar Mombasa ta ce.
"Zan shawarci ƴan'uwana mata kan kar su dena saka suturar leso, domin saka leso jinjina ce da kuma martaba gadonmu," Neema ta kammala.