An yi yunkuri da dama wajen sake dawo da waɗannan injinan na saƙa tufafi zuwa hayyacinsu: Hoto/Reuters

By Abdulwasiu Hassan

Ga wata tambaya cikin sauri: Mene ne alaƙar tufafin da aka samarwa a Nijeriya da tasowar ƙasashen Yammacin Afirka a matsayin cibiyar kwallon kafa?

Magoya bayan wasanni da suke iya riƙe bayanai, za su tuna cewar zakaran dan wasan Nijeriya da aka taɓa yi mai jefa kwallo a raga, marigayi Rashidi Yekini, ya fara kwallon ƙafa a ƙungiyar United Nigeria Textiles FC da ke garin Kaduna na arewacin ƙasar a shekarar 1982.

Wannan kuma lokaci ne da masana'antu da kamfanoni masu zaman kansu da dama suke daukar nauyin kwallon kafa a cikin kasar, suna bayar da gudunmowa ga habakar harkokin wasanni a kasar da a koyaushe take da masu basira, amma ba ta da hanyoyin habaka su.

Wani abin ban mamaki shi ne yadda bunkasar masana'antun tufafi na Nijeriya suka zo a daidai da Shuhurar kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya ta Suoer Eagles a gasar kasa da kasa ciki har da lashe gasar cin kofin kasashen Afrka a 1994 da gasar kwallon kafa ta Olympics a 1996.

Rashidi Yekini ne ya ci kwallon kafa ga Nijeriya ta farko a gasar cin kofin duniya: Hoto/Reuters

A wannan zamanin, kamfanonin samar da tufafi a kasar sun fuskanci barazana, suka dinga rushe wa daya bayan daya.

Wani nazari ya bayyana cewa a tsakanin 1994 da 2005, kusan kashi 64 na kamfanonin samar da tufafi da ke Nijeriya sun durkushe, abin da ya mayar da adadin daga 125 zuwa 45 a shakaru 11 kawai.

Ya zuwa 2022, akwai kamfanonin samar da tufafi kasa da 20 da ke aiki a Nijeriya. A 1995, akwai irin wadannan kafanonin guda 175 da suke aiki kuma suke da dubban ma'aikata.

"Idan aka kalli samar da ayyuka, adadin ayyukan da masana'antar ta samar ya zaftare daga 137,000 a 1996 zuwa 24,000 a 2008. A shekarar 2022, akwai kasa da mutane 20,000 da ke aiki a masana'antun samar da tufafi a Nijeriya," in ji Folorunsho Daniyan, shugaban Kungiyar Masu Samar da Tufafi a Nijeriya (NTMA).

Manyan dalilan da suka janyo durkushewar

Hamma Kwajaffa, darakta janar a NTMA, ya alakanta durkushewar masaƙu na Nijeriya ga karyewar Naira a 1980. Masu masana'antun tufafi da suka ci bashi a kasashen waje ne suka sha wahala wajen biyan basussukan.

Kwantenoni dauke a auduga cikin kura a wasu masana'antun samar da tufafi da aka rufe: Hoto/Reuters

"Biyan basussuka na ci gaba da zama matsala saboda yadda kuɗin kasashen waje ke kara hauhawa," ya fada wa TRT Afirka.

"Daga Naira Naira 3 da ake iya sayen dalar Amurka $1 a 1985, farashin ya tashi zuwa Naira 30. Yanayin da ya sanya da wahala a iya tsira."

Karyewar farashin kudin Naira ne ya sanya masu samar da tufafin ba sa iya gogayya da kayan da ake sayo wa daga kasashen waje da rahusa, wadanda suka samu karbuwa a kasar.

"'Yanci da budadden kasuwanci yajanyo sayo kaya da ma yin fasa kaurin su daga kasashen waje zuwa Nijeriya, kuma farashinsu kasa da na wadsnda ake samarwa a cikin gida. Wann an ne dalilin da a hankali ya janyo durkushewar baki daya." in ji Kwajaffa.

Amma Abubakar Musa Bunza, malami a sashen Injiniyancin zana tufafi da samar da shi a Jami'ar Ahmadu Bello ta Zaria, na kallon matsalar ta faffadar mahanga.

Ya alakanta matsalar rushewar masana'antar ga matsaloli daban-daban irin su lantarki, cin hanci da rashawa, da rikici tsakanin kungiyoyin kwadago da ma'aikata.

Bunza ya yi amanna da cewar masana'antun na cikin gida kuma na shan wahala wajen samun ingantattun kayayyaki, rashin wata hukuma da za ta dinga sanya idanu kan bangaren, da kuma yadda gwamnatocin da ke biyo baya ba sa iya magance matsalolin.

Gazawar matakan farfadowa

Wannan masana'anta na ta faduwa warwas a tsawon lokaci duk da yunkurin tallafawa daga gwamnatoci.

Masana'antar tufafi ta Nijeriya da ta shahara a baya, har yanzu na ta kokarin farfadowa: Hoto/Reuters

A 'yan shekarun nan, gwamnatin tsohon Shugaban Kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ta bayar da bashi da ya kai Naira biliyan 60 don farfado masana'antn samar da tufafi. Haka ma gwamnatin Muhammadu Buhari ta samar da Nair biliyan 294, amma babu wani sauyi da aka samu.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a baya-bayan nan ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na hada kai da Kwamitin Bayar da Shawarwari Kan Auduga na Kasa da Kasa (ICAC) don farfado da masana'antun, inza za a samar da ayyuka ga mutum miliyn 1.4 a kowacce shekara.

"Gwamnatin Tinubu za ta yi kyakkawan kokari don tabbatar da ƙasar ta amfana da dimbin arzikin audugar da take da shi, ciki har da tabbatar da cewa Nijeria ta sake zama mambar ICAC," in ji shi.

A yayin da Shettima bai bayar da dogon bayani kan yadda za su samu kudade don aiwatar da wannan shiri na farfado da masana'antun ba, Ministar Kasuwanci da Zuba Jari Doris Uzoka-Anite ta ce Nijeriya ta samo dala biliyan $3.5 don zuba jari a wannan fanni.

Kira ga sabon salo

Ba kowa ne ya gamsu da wadannan kalamai na gwamnatin tarayya ba, saboda yadda aka ga irin wannan yunkuri a baya.

Manazarta na ra'ayin cewar akwai bukatar sauya salo da dabarun farfado da kamfanonin samar da tufafi na Nijeriya: Hoto/Reuters

"Matukar ba a magance tushen dimbin matsalin da ake fuskanta ba, duk wani yunkuri da za a yi ba zai yi naara ba," Bunza ya shaida wa TRT Afirka.

"Mafitar da ake bukata ta hada da makamashin lantarki mai sauki kuma mai dorewa, da daidaitacciyar manufar shigowa da fitar da kayayyaki da za ta bayar da fifiko ga masana'antun samar da tufafinmu, da kuma yin binciken masana na jami'o'i."

Malamin jami'ar ya kuma bayar da shawarar samar da Cibiyar Binciken Samar da Tufafi.

Darakta Janar na NTMA Kwajaffa ya yi amanna cewa Nijeriya na bukatar daukar layi daga kasashe masu taso wa da masana'antunsu na samar da tufafi suke aiki.

Illar kudin da aka karya drajarsa

Tun bayan rugu-rugun da Naira ta yi a 2023, kudin ya rasa darajarsa da sama da rabi wadda a lokacin ta ke Naira 700 kan dala $1, inda a yanzu ta ke Naira 1,600.

"Idan muka karya darajar Naira, zai kasance mun zama kasar da sai dai ta sayo komai daga waje. Hakan zai sanya mu zama ba ma gogayya, kuma ba za mu iya fitar da kayayyaki ba," Kwajajjafa ya jaddadawa TRT Afirka.

Bunza ya yi nuni da cewar karya drajar kudi na da illa ga shigo da sinadarai da kayayyakin da za a yi amfani da su don samar da wasu kayan a cikin gida.

Hajiya Aisha Mohammed da ke da shago a Abuja, ta bayyana cewar buƙatar tufafi ta ragu sosai, saboda tsadar shigo da tufafin daga kasashen waje.

"Kayan da a baya ake iya saya, a yanzu sun zama 'Na nuna isa"", ta fada wa TRT Afirka.

Wasu masu nazari na fadin cewar masana'antun samar da tufafi na cikin gida na bukatar sauya manufarsu, su nemi yadda za su sayar da tufafinsu a kasashen waje, ba wai a Nijeriya kadi ba.

TRT Afrika