Daga Abdulwasiu Hassan
Garba Yusuf Maitama Kura yana cikin annashuwa saboda damina ta yi kyau. Yana farin ciki a bana saboda amfanin gonar da ya samu wanda ya ajiye ne daga noman rani.
Garba wani manomi ne da ke zaune a wajen Kano a arewacin Nijeriya, kuma ya san irin tasirin da kayan aiki ke yi a gonakin da ake yin noman rani wanda kuma hakan ne babban abin da ke taimakawa wajen samun amfani mai kyau.
"Na samu buhun shinkafa 67 a gona hekta daya da na noma, wato shinkafar da ba a gyara ba, kuma na sayar a kan naira 27,000 zuwa 33,000 kan kowane buhu," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Ba kamar galibin manoman Nijeriya ba, Garba yana noman rani kuma hakan yana ba shi gagarumar riba lokacin da amfanin gonarsa ya isa kasuwa.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake samun hauhawar farashin kayan abinci, wanda ya yi tashin da ba a taba ganin irinsa ba a cikin shekara kusan 20, kamar yadda alkaluman Hukumar Kididdiga ta Kasar (NBS) suka bayyana.
'Yan Nijeriya da dama ba sa iya ciyar da iyalinsu yadda ya kamata. Damuwarsu ita ce farashin kayan ya ki saukowa duk da cewa ana tunkarar karshen damina, a daidai lokacin da sabon amfanin gona yake isa kasuwa wanda hakan ke taimakawa wajen sauko da farashi.
Tsoron kada a ci gaba da tashin kayan abincin ya sa gwamnatin Nijeriya ayyana dokar ta-baci inda ta fito da wasu tsare-tsare – na nan-take da na matsakaicin lokaci da kuma na dogon lokaci don magance matsalar.
A tsarin matsakaicin lokaci, gwamnati ta shirya kashe kudin da aka tara daga cire tallafin fetur wajen aikin gona don kawo gyara ga fannin, kamar yadda Minista Dele Alake wanda tsohon mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu ne ya bayyana.
Hadarin karancin abinci
Galibi ana noma a Nijeriya daga lokaci zuwa lokaci, kuma an fi yin aikin gona ne a lokacin damina.
Kashi 90 cikin 100 na aikin gonar da ake yi a kasar ya dogara ne da damina, kamar yadda Bankin Ci-gaban Afirka ya bayyana ta hannun shirin Country Food and Agriculture Delivery Compact.
Alkaluman sun nuna cewa kaso 10 cikin 100 na manoman Nijeriya ne suke noman rani kuma su ne nauyin ciyar da kasar da ta fi kowace yawan jama'a ya rataya a wuyansu bayan damina ta tafi.
"Shugaban kasa ya ce ba za mu lamunci aikin noma na lokaci zuwa lokaci ba. Ba za mu lamunci karancin abinci ba," kamar yadda Alake ya bayyana yayin ayyana dokar ta-bacin.
Ana bayar da shawarar sanya duka wasu muhimman abubuwa a jerin kayan da Majalisar Tsaro ta Kasar (National Security Council) za ta sanya ido a kansu.
Alake ya kuma bukaci hadin gwiwa tsakanin Ma'aikatar Aikin Gona da Ma'aikatar Albarkatun Ruwa don tabbatar da wadatuwar kasar noman da za a rika yin noma a duk tsawon shekara.
Ruwan da ba a amfani da shi
Nijeriya tana da yalwataccen ruwa da za a iya noma da shi a gaba daya kasar, ciki har da manyan koguna 12 wadanda suke da wadataccen ruwa da za iya aikin noman rani a kasar noman da ta kai girman hekta miliyan 3.14.
A zahiri karamin bangare daga cikin makeken filin kasar noman kasar ne aka yi masa tsarin aikin noman rani.
"Kamar yadda majiyoyi da dama suka bayyana, filin kasar noman hekta 400,000 ne aka yi masa tsarin aikin noman rani a Nijeriya," in ji Farfesa Abba Aminu, babban darakta aikin gona a hukumar kula da kogunan Hadejia da Jama'are.
Ko da yake wasu suna ganin adadin bai kai haka ba, inda suke cewa kasar da aka yi wa tsarin noman rani ba ta wuce hekta 100,000 idan aka kwatanta da hekta miliyan uku da ake bukata.
Masana sun ce hekta miliyan shida na kasar noma ake amfani da shi cikin hekta miliyan 30 na kasar noma mai albarka da kasar take da shi. Ko da duka kasar noman za a mata tsarin aikin noman rani, sauran kasar noman ma za ta bukaci tsarin aikin noman rani.
"Rashin kasuwanni da farashi mai kyau, da matsalolin ajiye kayan da kayan aiki na zamani su ne manyan kalubalen noman rani a baya," in ji Farfesa Abba.
Halin da tattalin arziki kasar yake ciki ya dace a samar da yanayi da zai dace da kasuwanci wanda zai taimaka wajen samar da tsarin aikin noman ranin ga manoman da ba sa yinsa.
"Babban kalubalen shi ne tsadar noman rani, musamman ga manoman da ke amfani da injin ban ruwa mai amfani da man fetur. Saboda yadda farashin litar man fetur ya yi sama sosai, tsadar aikin noman rani zai karu sosai," in ji Farfesa Abba.
Yayin da yawancin manoma da suke son yin noman rani suke cikin tsaka mai wuya saboda da tarin kalubale, su kuma wadanda suke tsarin noman rani a kasar sun yi azaman tunkarar wucewar damina.
Abubuwan da suke so su cimma zuwa gaba
Ana fara damina ne daga watan Mayu zuwa Satumbar a arewacin Nijeriya, wato yankin da ke samar da galibin abincin da kasar take amfani da shi.
Yayin da damina take shirin tafiya cikin 'yan makonni masu zuwa, masu aikin noman rani kamar Garba suna shiryawa lokacin tsuka da kuma tsara abin da suke son cimma.
"Dabarata ita ce na mayar da hankali kan alkama saboda za ka iya ajiye ta har tsawon watanni. Sauran abubuwan da ake shukawa lokacin rani kuwa suna saurin lalacewa," in ji Garba.
"Da yardar Allah ba zan shuka kasa da hekta uku zuwa biyar na alkama ba. Zan iya samun buhu 30 na alkama daga kowace hekta."
Idan ana so yawancin manoma su fara noman rani da kuma bunkasa samar da abinci, to matakin farko shi ne sai an zuba jari a harkar noman rani.
"Dole sai an kirkiro sabbin dabarun noman rani, ta hanyar samar da injin ban ruwa mai aiki da hasken rana da sauransu," in ji Farfesa Abba.
Har sai wannan ya tabbata, wanda idan ba haka ba to mutane kalilan kamar Garba ne kawai za su ci gaba da aikin noman rani.