Daga Firmain Eric Mbadinga
Da yammacin wata rana a cikin ƙarshen mako na watan Fabrairu, wani al'amari mai faranta rai ya samu ƙasashe uku maƙwabtan juna a yankin Yammacin Afirka, waɗanda suke ga rikicin siyasa da zamantakewa da juyin mulki ya jawo musu tun daga shekarar 2021.
Ƙungiyar ECOWAS ta yankin ta yanke shawarar ɗage takunkuman tattalin arziki da ta ƙaƙaba wa Mali da Nijar da Guinea ba tare da ɓata lokaci ba, lamarin da ya zama hanyar warware rikicin da ya aka dinga ganin zai damalmala dangantakar da ke tsakanin ƙasashen yankin.
Wannan lamari mai yiwuwa ya sa Mali da Nijar da Burkina Faso da suka ayyana a ranar 28 ga watan Janairu cewa za su fice daga ƙungiyar ECOWAS, janyewa daga daukar matakin yin hakan.
A yanzu, yanayin da jama'a ke ciki kawai ya fayyace martaninsu kan abin da ya faru a ƙarshen makon a wajen taron ECOWAS da aka yi a Abuja, babban birnin Nijeriya, ranar 24 ga watan Fabrairun.
Baya ga sake buɗe kan iyakoki da bai wa jirage damar yin shawagi a sararin samaniyar Nijar, ECOWAS ta kuma ɗage takunkumin da ta sanya na ɗaukar ƙwararrun ma'aikata daga Mali da za su yi aiki a cibiyoyin ECOWAS.
Sai dai har yanzu tasirin matakan ba su gama gushewa ba, amma abin da ya fito fili shi ne cewa ƴan ƙasar Mali da Nijar da Guinea suna da kyakkyawan fata, saboda sun samu sauƙi daga sake buɗe kan iyakokin da ɗage takunkuman tattalin arzikin, musamman waɗanda suke shafar rayuwar al'umma.
Wani mamallakin otel a birnin Yamai na Nijar, Issifou Issa, ya ce yana fatan ganin haske bayan duhun da ya mamaye ko ina, amma duk da haka ya kasa mantawa da ɓacin ran da ya shiga a baya.
Yana daga cikin masu ganin cewa, wajen daukar matakan yaƙi da gwamnatin mulkin soja, kamata ya yi a bai wa al'ummar ƙasar kulawa ta musamman.
“Waɗanda suka yanke shawarar ɗage takunkumin ba su yi hakan da nufin faranta wa al’ummar Nijar rai ba. Sun yi hakan ne don sanin cewa matakin da ƙasashe ukun ke son ɗauka na ficewa daga ECOWAS zai yi mummunan tasiri.
"Ban sani ba, wataƙila matakan ba su dace da zatonsu ba, musamman ganin yadda duk da hakan al'ummar Nijar sun rayu," ya shaida wa TRT Afrika.
Issa, wanda kuɗin shigar da yake samu daga harkar otek ɗinsa ya yi ƙasa sosai tun bayan saka takunkuman, yana fatan a yanzu al'amura su sauya ya ga alheri.
Karya alkadarin takunkuman
Juyin mulkin da ya bai wa Kanal Assimi damar mulkar Mali ya faru ne a watan mayun 2021. ECOWAS ta sanya wa ƙasarsa takunkumai a ranar 30 ga watan Mayu, lamarin da ya dinga ƙara tsauri a hankali.
A ranar 7 ga watan Nuwamban shekarar ne, ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba takunkuman hana tafiye-tafiye da dakatar da Mali daga hada-hadar kadarori da kuɗaɗenta gwamnatin mulkin sojin.
Daga cikin sauran matakan, tun daga watan Janairun 2022, ECOWAS ta rufe iyakokin ƙasa da sama tsakanin Mali da ƙasashen da ke da alaƙa da ƙungiyar. Har ila yau, ta dakatar da hada-hadar kasuwanci da ƙasar Mali, sai dai waɗanda suka shafi kayayyakin kiwon lafiya da kayayyakin masarufi.
Kasar Guinea dai na fuskantar takunkumi tun kwanaki 22 bayan juyin mulkin da aka yi ranar 5 ga watan Satumban shekarar 2021. Daga cikin matakan da ƙungiyar ta ECOWAS ta ɗauka, ta dakatar da kadarorin mambobin gwamnatin mulkin sojan kasar tare da hana zirga-zirga.
An hana duk wata hada-hadar kuɗi da ke goyon bayan Guinea daga cibiyoyin hada-hadar kudi na ECOWAS.
Nijar ce ta baya-bayan nan da ta shiga sahun ƙasashen da ke fama da rikicin juyin mulki da aka hamɓarar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin shugaban ƙasar Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin shekarar da ta gabata, sannan kungiyar ECOWAS ta sanya wa gwamnatin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani takunkumai.
Kungiyar ta ƙasashen Yammacin Afrika ta kuma dakatar da hada-hadar kasuwanci da samar da wutar lantarki daga maƙwabciyarta Nijeriya bayan juyin mulkin.
A dukkan kasashen uku, shirin ɗage takunkumin na da nasaba da mayar da mulkin farar hula. An kuma buƙaci gwamnatin mulkin Nijar da ta saki tsohon shugaban kasar Bazoum da iyalansa lafiya.
Ba zato ba tsammani
Ana dai kallon ɗage takunkumin ba zato ba tsammani da aka yi a ranar 24 ga watan Fabrairu a tamkar ɗauke wani girgije da ya baƙanta tare da jefa rayuwar miliyoyin mutane cikin tasku a dukkan kasashen uku.
"Zan iya cewa babban bala'i ne a ɓangarenmu. Idan aka rufe kan iyakokin ƙasa, kusan filayen ba za a iya amfani da filayen tashi da saukar jiragen sama ba. Kusan dukkan otel-otel ba sa iya aiki. Wannan takunkumin na nufin bashin albashi na watanni da kuɗin wutar lantarki," in ji Issa mai otal.
"Tasirin hakan yana da yawa. Waɗanda suka yanke shawarar makomarmu ba za su iya tunanin irin wahalhalun da mutanen Nijar suka sha ba."
Cherif Mohamed Abdallah Haidara, shugaban kungiyar GOHA International da ke wakiltar masu gudanar da harkokin tattalin arzikin Afirka, ya ce harkokin kasuwanci a dukkan ƙasashen ukun da ke fuskantar takunkumi na lokuta daban-daban yanzu suna cikin "tashin hankali na bayan abin da ya faru".
"Ina tabbatar muku da cewa waɗannan takunkuman sun sa rayuwa ta yi mana wahala, wanda ya janyo hasarar kuɗaɗe masu yawa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Mohamed Abdallah Haidara bai iya farin ciki da ɗage takunkuman ba, ko da yake ba shi da tabbacin tasirinsu zai gushe a nan kusa.
"Hanyoyin sun ƙarfafa ci gaban kasuwar baƙar fata, wanda ya sa farashi ya hauhawa, musamman a sufurin kan iyaka," in ji shi.
A cikin yanayin jin daɗi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya, wanda a halin yanzu yake shugabantar ECOWAS, ya bayyana a wurin taron cewa, ya kamata ƙungiyar ƙasashen yankin ta sake duba yadda za ta tunkari ko ƙarfafa komawa kan tsarin mulki a Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma Guinea.
Romaric Badoussi, masani kan ƙungiyar ECOWAS, yana kallon abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a matsayin wata zazzafar jayayya tsakanin ɓangarorin biyu, wato ECOWAS da kuma gwamnatocin mulkin soja na Mali da Guinea da Nijar.
"Ta wasu hanyoyi, hakan na nuni da sassauci daga ƙungiyar. Labari mai daɗin shi ne za mu iya sa ran yanayin zamantakewa da tattalin arzikin al'ummar Nijar zai inganta," in ji masanin ɗan ƙasar Benin.
Shugaban sashen nazarin tattalin arziki na jami’ar tarayya ta Kashere da ke jihar Gombe ta Nijeriya, Isa Abdullahi, ya ce baya ga inganta tattalin arzikin da ake samu, ya kamata wannan matakin na ECOWAS ya kawo tsari da kwanciyar hankali ga sauran ƙasashe mambobin ƙungiyar a halin da ake ciki na tawaye, har ma da rashin yarda.
"Tasirin wannan manufa shi ne, akwai yiwuwar ƙasashen da ke son ficewa daga ECOWAS za su dawo. Kuma ina ganin hakan ma yana ƙara ƙarfafa gwiwa ga sauran ƙasashe mambobin."
Abdullahi ya yi hasashen cewa fita daga ECOWAS da ƙasashen da aka ɗage wa takunkumin suka so yi na iya janyo hauhawar farashin kayayyaki da kashi 50 cikin 100.
Shi kuwa Kabiru Adamu, wani mai sharhi kan harkokin tsaro a Nijeriya da yankin Sahel yana ganin "komawa zuwa turbar da ta dace" shi ne mafi kyawun abin da ƙungiyar ECOWAS ta yi.
"Ina ganin ma'anar farko ko muhimmancin sanarwar ita ce, ECOWAS na fatan cewa waɗannan mambobin da ke barazanar ficewa za su koma kan teburin tattaunawa, kuma wataƙila za a fara tattaunawa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.