Shugaba Bola Tinubu ya sha alwashin farfado da tattalin arzikin Nijeriya./Hoto: Getty Images

Daga Mazhun Idris

An cika kwana 100 da rantsar da Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya, wanda ya karbi mulki bayan nasarar zaben, inda ya dauki alkawuran kawo kyakkyawan sauyi a kasar.

Ranar 29 ga watan Mayu ne Shugaba Tinubu ya haye karagar mulkin kasar da take kan gaba a karfin tattalin arziki da yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Ya kama aiki ne a lokacin da kasar ke fama da hauhawar farashi, da rashin aikin-yi da matsalar tsaro.

Abubuwa da yawa sun farun a ciki da wajen Nijeriya tun bayan da Shugaba Tinubu ya dare karagar mulki.

Bayan watanni uku na gwamnatin ra'ayoyin masu sharhi ya bambanta kan nasarorinta.

Cire tallafin man fetur

Babban batun da ya mamaye kwanakin 100 na gwamnatin Tinubu shi ne abubuwan da suka biyo bayan janye tallafin man fetur a kasar, wanda ya haifar da tashin farashin mai a fadin kasar. Gabanin nan talafin mai ne ya taiamaka wajen sassauta farashi mai ga 'yan kasar.

Tun a lokacin yakin neman zabe Bola Tinubu ya jaddada kudurinsa na ririta arzikin kasar. Wannan ne ya sa bai bata lokaci ba bayan shan rantsuwar kama aiki, Tinubu ya sanar da cire tallafin mai gabakidayansa, tare da sauyi a kasuwar canjin kudin.

Babban batun da ya mamaye kwanakin 100 na gwamnatin Tinubu shi ne abubuwan da suka biyo bayan janye tallafin man fetur a kasar:Photo/Facebook/Bola Ahmed Tinubu

Sama da watanni uku bayan nan, ra'ayoyi sun bambanta game da ko shugaban ya yi gaggawar zartan da wannan mataki.

Kabir Ringim, wani injiniya mai karantarwa a Kwalejin Fasaha ta Binyaminu Usman da ke Hadejia a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar, ya ce akwai gyara kan yadda gwamnatin Tinubu ta soma aiki.

Malam Kabir ya bayyana cewa duk da dai cire tallafin mataki ne da ya kamata, amma bai dace gwamnati ta yi gaggawar aiwatar da matakin ba, wanda ya jefa talakawan kasar cikin matukar wahala.

Ya gaya wa TRT Afrika cewa, "Mun yarda cewa akwai matsaloli a yadda ake gudanar da tallafin mai, kamar masu sayen man da araha su kai shi kasashe makwabta don cin riba. Amma idan gwamnatocin baya sun gaza hana satar, ita wannan gwamnatin ai da ta gwada wata dabarar. Ta yaya za ka yanke kanka don kana ciwon kai."

Rage radadin

Yayin da jama'a ke fama da tasirin cire tallafin na mai, gwamnatin Tinubu ta fitar da jerin shiryue-shirye da za su rage radadin cire tallafin da ke shafar mutanen kasar.

Shirin jinkan ya kunshi samar da hatsi daga rumunan gwamnatin tarayya don rabata talakawa a farashi mai rangwame. Sai dai shirin raba tsabar kudi ga matalautan mutane bai samu karbuwa ba, inda aka janye shirin.

A ranar 17 ga watan Agusta, gwamnati ta sanar da fitar da Naira biliyan biyar (kusan dalar Amurka miliyan $6.5) ga jihohin 36. Kudaden za a sayo motocin safa masu dauka fasina, sai kuma sauran kudin a rabawa mutane abinci.

Tijjani Muhammad Musa, wani babban dan jarida a birnin Kano, yana ganin ana bukatar karin tallafa wa talakawa, sakamakon "girman tasirin farashin kayayyaki wanda 'yan kasa suke fama da shi saboda tashin farashin mai".

Ya ce, "An ganin shugaba Tinubu a matsayin jajirtaccen jagora, saboda tarihin mulkinsa na shekaru takwas a matsayin gwamnan jihar Legas.

"Amma yunwar da wahalar da al'umma ke fama da ita suna fara kawar mana da kyakkyawan fatan da muke da shi."

Shugaba Tinubu ya yi suna wajen a matsayin gogaggen dan siyasa wanda ya san yadda ake gina hada tawagar da za ta yi aiki cikin nasara.

"Amma bai tsaya jiran kaddamar da kwamitin tattalin arziki ba, kafin y sanar da janye kulawa kan kudin kasar na Naira, a kasuwar canjin kudi.

An nada Tinubu shugaban Kungiyar ECOWAS. Hoto: Facebook/Bola Ahmed Tinubu

Ko an dauki hanya?

Matakin shugaba Tinubu na haramta tsarin kasuwanni biyu na hada-hadar kudin kasashen waje, da kuma karya darajar Naira, abu ne da ake wa kallon kyakkyawan shiri.

Injiniya Kabir Ringim yana cikin wadanda suka yi amanna da wannan tsari, inda ya ce, "Na goyi bayan shirin na gwamnati saboda ba za a iya ci gaba da ciyo bashi ana tokare Naira ba. Kuma 'yan tsirarun mutane ne suke ribatar tsohon tsarin"

Sai dai kuma, karyewar darajar Naira ya haifar tsadar kayayyakin, kasancewar Nijeriya ta dogara da shigo da kaya daga kasashen waje wanda ake lissafawa a farashin dalar Amurka.

Baya ga sauya tsarin canjin Naira, Shugaban ya kuma dakatar da shugaban babban bankin kasa, Mr. Godwin Emefiele, wanda ke tsakiyar wa'adinsa na biyu. Masana suna fahimtar wannan matakin a matsayin kokarin Tinubu na karfafa ikonsa kan madafun tattalin arzikin kasa.

Victory Iniobong, wata 'yar kasuwa ce da ke birnin Uyo na jihar Akwa Ibom da ke yankin Niger Delta. Kuma tana cikin kangin tattalin arziki inda ta ce, "Mun yi zaton ganin rayuwarmu ta inganta, amma tashin farashin kayayyaki ya da karyewa Naira suna uzura mana".

Nada ministoci

Tinubu ba sanara da sunayen ministocinsa ba har sai ranar 27 ga watan Yuli, lokacin da ya mika jerin sunayen ministoci ga majalisar dokokin kasa. Majalisarsa ta zartarwa ta kunshi minitoci 45 kuma an kaddamar da ita a ranar 21 ga Agusta.

Tun a watan Yuni ne Shugaba Tinubu ya cire shuwagabannin tsaro na kasar, inda ya maye gurbinsu da sabbin shgabannin rundunonin soji, da na 'yan sanda, da na hukumar hana fasa-kwauri.

Malam Tijjani Musa ya yi nuni da yadda shugaba Tinubu ya nada mataimakansa, da kuma sakataren gwamnatin tarayya, wanda haka ya nuna shugaban ya zo da shirinsa. Amma sai aka ga kwan gaba kwan-baya yayin nada ministoci".

Tijjani ya kara da cewa, "Muna da dalilin rage buri har sai mun ga yadda shugaban da manistocinsa za su yi nazarin matsalolinmu da na tattalin arzikinmu, musamman tallafawa kananan masana'antu".

Bola Tinubu ya sha rantsuwa a matsayin shugaba na biyar bayan dawowar Nijeriya mulkin farar hula a shekarar 1999. /Hoto: Facebook/Bola Tinubu

Rikicin Nijar

Makonni shida da kama aikin shugaba Tinubu, sai aka zabe she a matsayin shugaban kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka, wato ECOWAS, a yayin wani taron kungiyar da aka yi a Ghana.

sai dai kuma, a makonsa na uku da fara jagorancin ECOWAS, sai sojoji suka hambarar da gwamnatin dimukuradiyya a kasar Nijar, wanda hakan ya tsunduma kasar da ke makotaka da Nijeriya.

Wannan turka-turkar juyin-mulki ta faru ne duk da cewa shugaba Tinubu ya yi gargadin cewa ECOWAS ba za ta lamunci kafa gwamnati ta haramtacciyar hanya a kashashe mambobinta ba. Ya yi gargadin ne bayan samun juyin-mulki a kasashen Mali, da Burkina Faso, da Guinea.

Da yawan mutane suna ganin rikicin Nijar zai zama wani ma'auni na yadda shuagab Tinubu zai nuna sanin makamr diflomasiyya, don taimaka wa yankin Afirka ta Yamma ya cimma muradun cigaba.

Wa'adin da ECOWAS ta saka wa sojin Nijar na su mayar da mulki ga tsohon shugaba Mohamed Bazoum ko su fuskanci harin soji, bai yi wa mutane da dama dadi ba.

Mallam Tijjani ya ce "An yi gaggawa wajen barazanar hari kan Nijar, musamman ganin ba a nemi sahalewar majalisar dokokin kasa ba, da kuma sauran 'yan kasar Nijeriya".

Bayan wata guda da kifar da gwamnati a Nijar, ba a samau wani ci-gaban a zo a gani ba, wajen warware rikicin da mayar da mulki ga farar hula.

Lokaci na tafiya yayin da Shugaban na Nijeriya ke kokarin neman mafita game da matsalar siyasar ta Nijar.

Yayin da gwamnatin Tinubu ta cika kwana 100 cikin wa'adinsa na shekaru hudu, wasu 'yan Nijeriya sun fara karaya, amma kuma ba su fitar da rai kan gwamnatin za ta yi abin a zo a gani ba nan gaba.

TRT Afrika