An saka hannu kan yarjejeniyar Kawancen Kasashen Sahel a birnin Bamako. / Hoto:X/Kanar Assimi Goita

Daga Abdulwasiu Hassan

Sabon kawancen soji tsakanin kasashe uku na Yammacin Afirka, wato Nijar, da Mali, da Burkina Faso, ya jawo babbar muhawara a yankin. Kawancen zai iya tasiri kan karfin fada-a-ji na ECOWAS, da ma rayukan al'ummar yankin nahiyar.

Shugaban mulkin soji na Mali, Assimi Goita, wanda ya kwace mulki a 2020, ya bayyana cewa "Yarjejeniyar Liptako-Gourma ita ce kadarkon gamayyar kasashen yankin Sahel don kafa tsarin tsaron juna, da taimakekeniya don kare al'ummarmu".

Wannan cigaban da aka samu yana zuwa ne bayan takun-saka da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Nijar, wanda ya janyo wa kasar fushin ECOWAS, da takunkumin tattalin arziki, har ma da barazanar amfani da karfin soji.

Wannan sabon kawance da ya hada Nijar da kawayenta biyu da suke adawa da ECOWAS, wani babban mataki ne mai nuna za a samu gagarumin sauyi kan tsarin karfin kasashe, inda tasirinsa zai wuce iyakokin yankin.

Rushewar tasirin Faransa

Wasu masu fashin baki suna ganin kafuwar wannan Kawance na kasashen Sahel, wata alama ce da ke nuna zagwanyewar tasirin Faransa a yankin Afirka ta Yamma.

"Tasirin Faransa a Yammacin Afirka yana ta tabarbarewa", in ji Kabiru Adamu, wani mai sharhi kan harkokin tsaro. Ya fada wa TRT Afrika cewa hakan yana bayyana a kasashen da suka koma karkashin mulkin soji.

Kawancen ya zo ne yayin da kyamar Faransa yake yaduwa a Yammacin Afirka. / Hoto: Getty Images

Ya kara da cewa, "Kan wannan ne, kasashe kamar Nijar, da Burkina Faso, da Guinea da Mali suka nuna karara yadda tasirin kyamar Faransa yake".

Farfesa Issoufou Yahaya, wanda ke karantarwa a Jami'ar Abdou Moumouni da ke babban birnin Nijar, shi ma yana ganin wannan sabon kawancen a yankin Sahel a matsayin wata alamar Faransa tana rasa tasiri a Yammacin Afirka.

Ya bayyana cewa, "Ba a yi mamakin ganin cewa duka kasashen a baya Faransa ce take rarraba kansu ba. Mutane suna bukatar su fahimci cewa wannan daya ne daga dalilan da suka sa kasashen uku suka hada kai."

Da alama juyin mulkin Nijar ya zuzuta wutar kyamar Faransa a cikin kasar. A hukumance, gwamnatin Faransa ta yi ta cewa za ta saurari zababbiyar gwamnati ne kadai.

Amma bayan makonni ana tataburza, a karshe Faransa ta sanar da cewa za ta janye dakarunta da jami'an ofishin jakadancinta daga Nijar, kamar yadda gwamnatin sojin mulkin kasar ta nema.

Farfesa Yahaya ya fada wa TRT Afrika cewa, "Tun da ana kirga Nijar cikin kasashe matalauta a duniya, duk mai hankali zai yi tambaya, 'Ta yaya zai yiwu a ce matalauciyar kasa ta bukaci jakada da dakarun Faransa su bar kasarta, kuma Faransa ta ce ba inda za su je?' Wannan ya nuna akwai wata a kasa, wato arzikin ma'adanan Nijar".

Wannan zargi kan tsohuwar uwargijiyarta yana da alaka da arzikin albarkatun yankin, kuma ya taimaka wajen ingiza wutar kyamar Faransa, ba wai a Nijar kawai ba, har a fadin yankin.

Ta'azzarar takun-saka

Rajin kyamar Faransa ba shi ne kadai batun da wannan kawance zai tunzura ba. A cewar masu fashin baki, yarjejeniyar ta kara ruruta takun-sakar diflomasiyya a yankin da ke matukar bukatar zaman lafiya.

An yi ta yin zanga-zanga a Nijar tun bayan juyin mulkin na watan Yuli. / Hoto: Getty Images

Farfesa Kamilu Fagge na Tsangayar Nazarin Siyasa, a Jami'ar Bayero ta Kano, ya fada wa TRT Afrika cewa, "Samun wata kungiyar a Yammacin Sahel zai iya kawo baraka a yankin. Za a samu tsagi biyu — masu goyon bayan ECOWAS da sauran".

A cewarsa, mafi munin abin da zai faru shi ne za a samu gogayya tsakaninsu, har ta kai Nijar, da Mali da Burkina Faso, sun fara karkata zuwa gun Rasha da China.

Masanin tsaro Kabiru Adamu yana ganin hadin guiwa tsakanin kasashen uku zai dakushe tasirin Faransa da na ECOWAS a yankin gabadaya.

Ya kara da cewa, "ECOWAS tana da mambobi 15. Idan guda uku suka fice daga duk wata yarjejeniyar soji a cikin kungiyar, za a iya samun wasu ma, da za su yi tunanin yin hakan don nuna goyon baya."

Ko da hakan bai faru ba a yanzu, Farfesa Yahaya ya jaddada cewa kawancen zai iya haifar da barazana ga ECOWAS. "Ina ganin kwanakin ECOWAS sun fara karewa. Sabon kawancen ya shirya karbar duk kasar da take da ra'ayi iri nasu."

Yaki da ta'addanci

Yayin da sabon kawancen soji na Sahel da kuma ECOWAS suka mai da hankali kan tunkarar junansu, masu sharhi ba sa mayar da hankali kan ta'addanci da rikice-rikicen da ke barazana ga zaman lafiyar yankin.

Kasashen uku sun ce kawancensu zai sanya ido kan yakar ta'addanci a iyakokinsu. / Hoto: Getty Images

Ministan Tsaro na Mali, Abdoulaye Diop ya fada a wani taron manema labarai bayan sanya hannu kan yarjejeniyar cewa, "Wannan Kawance zai hada da kawancen sojoji da na tattalin arziki tsakanin kasashen uku. Babban burinmu shi ne yaki da ta'addanci a kasashen uku".

A baya duka kasashen uku suna cikin kungiyar kawancen G5 Sahel, wadda Faransa ke mara wa baya, wadda ta hada da kasashen Chadi da Mauritania. An kafa G5 ne a shekarar 2017 don tunkarar kugiyoyin ta'addanci a yankin. Tuntuni Mali ta bar kungiyar bayan juyin mulki a kasar.

Adamu ya bayyana cewa, "Gaskiyar magana ita ce yaki da ta'addanci batu ne na kasa-da-kasa. Tabbas, akwai babban bangaren yaki da ke cikin gida. Amma, babu kasar da za ta iya yakin ta'addanci ba tare da tallafin sauran kasashe, musamman makwabtanta ba".

"Kenan, ware kansu da kin yin aiki tare da gamayyar kasashen yankin ko kulla hadin gwiwa da kungiyoyi kamar ECOWAS zai iya zama mafarin matsaloli."

Farfesa Kamilu Fagge yana ganin cewa abubuwa suna gyaruwa. "A yanzu dai, ina ganin batun sabuwar takaddama tsakanin kungiyoyin biyu zai mamaye duk wata tattaunawa".

Yayin da wannan sauye-sauye ke faruwa don kokarin samun fifiko tsakanin bangarorin biyu, al'ummar yankin Yammacin Afirka za su yi fatan matsalolin siyasa da na diflomasiyya ba za su rusa dorewar zaman lafiya da wadata a yankin ba.

TRT Afrika