A karshen watan Yuli, kana daga cikin wadanda suka raka Shugaba Macron zuwa Kamaru, Benin da Gini-Bissau. A matsayin ka na babban jigo a taron Afirka-Faransa na karshe da aka gudanar, me ne ne ya ba ka damar zama babban jigon? Akwai batutuwa da dama da na warware. Game da Kamaru, babbar tambayar ita ce batun mika mulki. Shugaba Paul Biya zai zama ya mulki kasar nan na shekru 40. Shi ba dawwamamme ba ne. Kasar na fuskantar kalubale da matsaloli da dama. Ta yaya za mu tabbatar da wannan mika mulki ba tare da an janyo hayaniya da za ta kawo matsala ga cigaban kasar da zaman lafiyar yankin ba? Yana da muhimmanci a tattauna da Faransa, wadda ta zama kawar alfarma ga Kamaru.
Ya kamata a bijiro tare da tattauna batutuwa da tambayoyin da suka shafi gwagwarmaya da yake-yaken da suka biyo bayan yunkurin neman ‘yancin kai. Benin da ta shiga cikin hali mawuyaci dake jan hankalin kowa, na son zama bude ga duniya a bangarorin yawon bude da raya al’adu don ta zama jagora a yankinta. Ina da sha’awar ganin wannan ta tabbata. Aiyukan zane da hotuna na Faransa da za a kaddamar a Cotonou, zan so ganin haka ta tabbata.
Duba da kalu-bale da sukar da kake fusknat kan wannan aiki, ta yaya tunaninka a matsayin mai nazarin diddigi kan lokutan bayan mulkin mallaka, game da Faransa da kasashen da ta raina, da kuma ita kanta Faransan dake kokarin bayyana kanta ta hanyar amfani da dabarunka na kulla alaka tsakanin kasashe biyu--- a lokacin da dole wani ya zabi wani a kan wani?
Yana da muhimmanci kwarai a yi watsi da nuna bambanci ko wariya wanda a koyaushe zai sanya mu nuna “adawa”... Abun da na fadawa shugaban Jamhriya, Emmanuel Macron, shi ne na rubuta a litattafaina---ba kari ba ragi. Kuma na yi amfani da tunani iri daya a tattaunawata da shi. Babu Mbembe da ya hadu da masu mulki ya canja magana. Akwai yiwuwar mutum ya rike akida daya yayin mu’amala da masu mulki-- na siyasa, kudi ko addini.
Mene hakikanin kariyarka a lokacinda ka daukimatakin nakiya kamar yadda aka ga kana yi?
Kariyarka shi ne fuskantar kanka. Ba ta da alaka da jama’a. Mataki ne na yin daidai a gaban kanka. An san nawa matsayin--- an bayyana shi a litaffaia da yawa cikin yaruka da dama da aka fassara. Wannan ra’ayin da na bayyana a lokacin da na hadu da Shugaban Jamhuriya, kuma shi nake bayyanawa a duk inda na je shiga tsakani. Yarda da kai, shi ne karfin mutum, idan mutum ya tsaya tunanin yin wuru-wuru, to zai zama yana bata lokacinsa, niyyarsa da karfinsa ne kawai.
"Karfin mutum”, “Tunanin kanka”... Ra’ayoyinka na sabawa da wannan zamanin, wana aka fi raja’a kan a dinga tunanin jama’a dukka, “Mu”.
Magana ta gaskiya babu wani abu na ‘hadin kai’ a wannan zamanin. Akwai wani abu da ya game ko’ina. Muna ganin yadda l’umu ke tasowa. Amma ba jama’a ne masu hadin kai waje guda ba. Idan muna son mu sake gina al’umu masu karfi, dole ne mu jure kalubale, mu sake dawo da karfi wajen aiyukanmu masu tsauri. Babu wanda zai iya gina jama’ar siyasa, ba tare da tunanin tsanaki ba.
Abun takaici, a wannan lokacin na kafar sadarwa ta zamani, muna shaida zaizayewar tunanin kawo cigaba, a saboda haka, ake da damar ka tsaya kyam kuma a kan ra’ayinka--- shi ne a ce tsagwaron ‘yanci. Wannan sharadi ne ga Afirka matukar tana son sauyi a tattaunawar alakarta da kasashen duniya. Abu ne na bayyana kai ga batu na tarihi da ya rataya a kan mutum. Abun na sanya a gaba shi ne kokarin sauya yanayin da alakar Afirka da Faransa ke ciki ta yadda za ta bar zama kamar wasan yara, mara hayaniya.
An tabo batun Kamaru a watan Yuni, Aljeriya a Agusta--- kasashe biyu da suke kan gaba game da rikicin zamanin mulkin mallakar Faransa. Ya za ka bayyana ziyarar ‘Kawance’ da Emmanuel Macron ya kai Aljeriya, kusan shekara guda bayan kalaman da ya yi marasa kyau kan “hayar kwakwalwa’ da gwamnatin Aljeriya ke da shi?
Muna rayuwa a duniyar da mutane da dama ba sa son su kula kowa. Daga yanzu, ana kallon sulhu a matsayin yaudara, shin wannan ce irin duniyar da muke son ginawa? Duniyar da mafi karfi yake kakaba ra’ayinsa a kan duniya? Ba wannan ne ra’ayina game da duniya ba.
Dadin dadawa, a al’adar siyasa da falasafar inda na fito, manyan [shugabanni] da suka yi adawa da mulkin mallaka, kamar Patrice Lumumba da Ruben Um Nyobe duk sun nemi a yi sulhu da tattaunawa. Wadanda suka yi musu kallon ‘yan ta’addane suka ki yarda su yi magana da su. Da a ce Nelson Mandela bai yi magana da makiyansa ba, ina Afirka ta Kudu za ta kasance yau?
Karara za mu ga ya zama dole mu yarda da batun sulhu--- amma da tabbacin sai ta zama tattaunawa tsakanin masu matsayi daya don gina duniyar da take mallakinmu dukka. Zabin da ya rage kawai shi ne a gina ta tare.
Idan Macron ya je Aljeriya, to yana bukatar albarkatun gas, Aleriya kuma na son sayar da gas din ta. Amma ya sanya mun yi imanin da mu ke da wuka da nama wajen bayyana farashin hajarmu. Ba wai batun a sayar musu yadda suka ga dama ko su sata ba ne.
Saboda rikicin Yukren, malamin siyasa Bertrand Badie ya bayyana cewa “Manyan kasashe daidai suke wajen daukar hatsari” Wannan batu dake magana kan daidaito na nuni da Afirka, saboda rikicin makamashin, na iya samun wani karfi a yau. Za ka iya bayyana rikicin Yukren a matsayin wata dama ta tarihi kamar yadda Covid ta ama?
Bertrand Badie ya fadi gaskiya. Abun dake fayyace duniya shi ne na cewa dukkan mu muna fuskantar hatsari na bai daya. Amma kuma matsayin rauni ba daidai ba ne a tsakanin kasashe. Mun ga haka ta fuskar samun allurar riga-kafin Corona.
Ba a iya kawar da nuna rashin daidaiton fuskantar hatsari gaba daya ba. Ama kuma, manyan abubuwan dake barazana ga rayuwar dan adam a ban kasa abu guda ne. Domin rayuwa, dole mu hada kai mu fuskance su.
Duk wannan na bayani kan ole mu tattauna tare da sake nazari kan dawo da saka kowa a cikin al’amura da yanke shawarwari; China na iya magana da Amurka, Amurka ta yi da Rasha, Rasha ta yi da NATO, Turai da Afirka...
Game da halan, dole ne kowa ya zama yana magana da kowa?
Mene ne daya zabin game da tattauna? Shi ne a fara yaki har sai an fito da Nukiliya? Shin wannan ne zabin da ya ragewa dan adam a yau a matsayin mafita?
A watan Yuli, Türkiye ta yi kokarin hada Yukren da Rasha inda suka sanya hannu kan yarjejeniyar bayar damar fitar da hatsi zuwa kasashen waje. Shin Turai za ta iya janye tsanar da take nunawa Turkiye saboda amfanin kanta? Wannan yarjejeniya ta hana afkuwar yunwa a Afirka da wasu sassan duniya.
Duba da akidoji, wadannan amfani na kai ba za su hadu waje guda ba. A lokacin da muke da tunanin da ya sabawa amfanin wani, dole ne mu yi kokarin hade su waje guda. Wannan ne aikin diplomasiyya. Sai an dakatar da fada mana cewa mu yi watsi da hakan, wanne abu muke da shi a gabanmu don tattauna domin matsawa gaba?
Türkiye na da ra’ayi [kan Afirka], amma Afirka ma na da bukatu a wajen Türkiye. Nahiyar na da bukatar yin kasuwanci da Turkiye, wajen assasa abubuwa tare. Dole ne mu doshi hanyar duniya da za a kulla alaka ta kasa da kasa. Idan ka samu nasara, Na rasa: Dole ne mu manta da wannan batun. Babbar tambayar na zuwa ne wajen tabbatar da dukkan mu mun iya rayuwa a duniyar nan. Wannan ne [babban] kalubalen da sakafar karni na 21 ke fuskanta.
A Aljeriya, Macron ya yi kira ga matasan Afirka da su ‘yantar da kawunansu daga “Cin fuskar faransa” wajen nuna yatsa ga China, Rasha da Turkiye. Me kake tunani gme da hakan?
Game da batun ra’ayoyin adawa da Faransa, muna bukatar gudanar da zuzzurfan nazari da bincike. Me ya sa muka kawo wannan mataki? Akwai dalilai na tarihi da tattalin arziki.... Yadda muka dauki wannan abu da muhimmanci, shi zai sanya a warware shi cikin sauri. Haka kuma, kungiyoyin farar hula a Afirka na da rawar takawa wajen kwaskwarima ga siyasa, da tabbatar da ta zama abun dabbakawa a aiyuka da dama.
Game da rikicin Yukren, ka yi magana kan “mulkin mallakar Rasha” Tsakanin Emmanuel Macron da Vladmir Putin, kan sulhu, wanda da fari ya taho a hankali, amma a yanzu ya rikice...
Emmanuel Macron ya ci gaba da magana da Macron, amma a bayyane take karara cewa tattaunawar ba ta yi karfi ba, amma akalla dai wayoyin hannunsu a bude suke ga juna. Za mu iya saka ran za a kawo karshen yakin Yukren. Dole ne mu dauki matakin magance tushen yakin. Kuskure ne a yi tunanin daya daga cikin su na da gaskiya dari bida dari, sannan dayan kuma ba shi da ita.
A yadda kafafan ya da labarai suke dakko rahoto kan rikicin, bangaren dake jan hankalinmu don tausayawa, na hana mu kallon gaskiya kan “waye kan daidai waye ba haka ba”....
Ba haka abun yake ba sam ---- ko a tarihin mulkin mallaka ba haka ba ne. tarihi ba ya aiki ta wannan fuska. Dole ne mu dawo ga hankali na kwarai. A tattaunawar jama’a ta bogi, muna rasa hankali mai kyau, ind ahakan zai amfani hakaito da tunani mara kyau a kwakwalen mutane. A rikici irin wannan, Ina sake maimaitawa: Babu wanda zai zama 100 bisa dari daidai ko ba daidai ba; ba abu ne da zai yiwu ba.
Dadin dadawa, Yarjejeniyar Minsk (2014) da yarjejeniyar da ta ci gaba da amsa wannan suna a (2015) na kan wannan magana kuma suna son dabbaka zaman lafiya.
Wannan yaki ne mummuna saboda yadda kasashe biyu ‘yan uwa suka koma abokan gaba suna kashe junansu, wanda hakan zai bude kofar babban bala’i. Abun da ya fi shi ne a rabu son zuciya a koma kan magance tushen rikicin. Rasha da Yukren za su ci gaba da rayuwa a kusa da Turai bayan wannan yakin. Ba su da wani zabi. Za su fara shirye-shiyen rayuwa bayan yaki.
A shekarar 2020, an zarge ka da ra’ayin kyamar Yahudawa a Jamus bayan bayar da misali kan nuna wariyar Afirka ta Kudu da bukatun Falasdinawa. A wannan bazarar ma an sake tattauna irin wannan batu tsakanin wakilai 38 na al’umu ---- ‘Yan gurguzu, ‘Yan tawayen Faransa da EELV sun sanya hannu kan “Nuna wariya da aka assasa” a Isra’ila. A bayyana yake karara cewa akwai batutuwa masu rauni a tattaunar da jama’a ke yi. Ta yaya a wannan zamanin za mu dawo kan gaskiya da turba mai kyau?
Na je Afirka ta Kudu, ina na yi rayuwata ta samartaka a can, tsawon shekaru 22. Kasa ce mai kyau. Yakin wariyar launin fata ya dauki tsawon shekaru. A wasu lokutan wanan kasa ta mika kanta ga sake farowa daga farko wajen ginuwa. Domin dakatar da yakin, don dawo da tattaunawa, domin bayyana abun da ke fruwa ya cutar da kowa. Shi kansa mai zaluncin ya zama kamar ba mutum ba wajen murkushe wadanda yake zalunta.
Wannan ramako ne ya tilastawa mutane su sauya tunaninsu gaba daya game batun a zo a hada kai waje guda --- domin tunkarar abun da ya faru, a karbi gaskiya tare d daukar alhaki. Hanya ce da gyara ke farowa.
Siyasar gaskiya, amincewa ko ikirari, sulhu da gyara: wannan ce hanya. Wadannan labarai na tarihi. Nuna goyon baya ga tarihi da abubuwan da suka faru marasa kyau ga dan adam, na da matukar muhimmanci. Ina tunanin hakan na nufin kyamar Yahudawa da Nuna Wariyar Launin Fata. Idan har za a ci gaba da batun waye ya fi shan wahala, ba za mu taba warware wannan batu ba.