Akwai bukatar Afirka ta ba da fifiko wajen samar da kayayyaki masu yawa don samun ci gaba mai dorewa, in ji kwararru: Hoto/ Getty

Daga Abdulwasiu Hassan

Hoton wani ƙaramin kwale-kwale a kan teku dauke da mutane cikin yanayin firgici da tashin hankali ya zama labarin da Ƙasashen Yammacin Duniya ke ganin baƙin haure 'yan Afirka da ke kokarin ƙetarawa zuwa kasashen Turai ko ta halin kaka.

Abin takaici yawancin ire-iren labaran nan gaskiya ne kuma galibin mutanen, matasa ne 'yan Afirka, wadanda ke fuskantar hadarin mutuwa a cikin Hamadar Sahara ko ta Tekun Bahar Rum, da nufin samun rayuwa mai inganci wadda ba su da tabbacin samu.

Wani abin baƙin ciki shi ne, matasan ba su san sun bar wata nahiya mai wadata da albarkatun ƙasa masu ɗimbin yawa ba.

To, a ina matsalar take? Ci gaban nahiyar Afirka ya ragu sosai a ma'aunin masana'antu.

Afirka ta Kudu ce ke gaban sauran kasashen Afirka wajen samar da ayyukan yi na masana'antu: Hotuna/Getty 

Yawancin bakin haure suna mafarkin samun ayyukan yi a kasashen da suka ci gaba a masana'antu saboda sun yi imanin cewa babu irin wadannan ayyuka da damarmaki a Afirka.

Alkaluma dai sun kafa hujja kan wadannan ra'ayoyin, na cewa har yanzu hanyoyin samar da kayayyaki masu yawa sun yi kasa a nahiyar, duk da cewa kasashe da dama sun iya kokarinsu.

Gaza cika mafarkinsu

Farin cikin da ya biyo bayan samun ‘yanci daga mulkin mallaka a kasashen Afirka da dama ya kawo kyakkyawan fata daga yunkurin samar da masana’antu da shugabanni suka yi bayan samun ‘yancin kai.

Kafa masana'antu tun daga na masakun tufafi zuwa na sarrafa abinci da masana'antar hada motoci sun haifar da farin ciki mara misaltuwa a wannan yunkuri.

Sai dai mafi yawan masana'antu da aka kafa a lokacin ba su wani jure zama ba saboda yanayin rashin daidaiton kasuwanci.

An iya cewa ci gaban masana'antu ba su zo daidai da yanayin karuwar al'ummar nahiyar ba, lamarin da ya taka rawa wajen tabarbarewar hasashen ci gaban tattalin arzikin da ake sa ran zai samu.

Rashin samar da ababen more rayuwa na daya daga cikin manyan matsalolin da ke janyo koma baya wajen samar da kayayyaki masu yawa don samun riba a nahiyar: Hoto/ Getty

Yayin da bukatu da yawan al'ummar Afirka suke dada karuwa, gazawarta nahiyar wajen cin gajiyar wadannan abubuwa sun tasiri ga kasashe masu arzikin masana'antu, lamarin da ke ci gaba da wakana har zuwa wannan lokaci.

Sannu a hankali cikin tafiya

Sannu a hankali cikin shekaru goma an 'dan samu ci gaba a yunkurin samar da masana'antu a nahiyar.

"An samu ci gaba masu yawa a kasashen Benin da Habasha da Eritrea da Gabon da Guinea da Mauritaniya da Mozambique da Senegal da kuma Seychelles, darajar kasashen dukka ya dagu zuwa matsayi na biyar ko sama da haka a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2019," kamar yadda rahoton mau'ni Masana'antun Afirka na shekarar 2022 ya yi nuni.

Kazalika, sigar farko ta rahoton, wanda bankin raya kasashen Afirka ya fitar, ya bayyana cewa, mafi yawan kasashen Afirka na samun ci gaba a sannu a hankali wajen bunkasar masana'antu.

"Cikin bayanai ma'aunin dalla-dalla, kasashen da matsayinsu ke kan gaba sun hada da wadanda ake samu riba da kuma kaso mai yawa a yanayin samar da kayayyakin su da ake fitarwa wasu kasashen," in ji rahoton.

Rahoton ya bayyana Afirka ta Kudu a matsayin kasar da ta fi samun ci gaba a fannin masana’antu a nahiyar, sai kuma kasar Morocco da Masar da Tunisia da Mauritius da Eswatini da Senegal da Nijeriya da Kenya da kuma Namibiya.

Kazalika rahoton ya bayyana kasashe goma masu karancin matsayi a ci gaba masana'antu a nahiyar kamar kasar Laberiya da Malawi da Sao Tome da Principe da Chadi da Comoros da Eritriya da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Saliy da Guinea-Bissau da Burundi da kuma Gambiya.

"Ta fuskar samun bunkasa, yankin dake da kokarin a wannan fannin shi ne Gabashin Afirka, wanda ke samu karin kashi 0.8 cikin dari a kowace shekara, sai Afirka ta Yamma da karin 0.66 cikin 100 sai kuma yankin Afirka ta kuddancin Afirka dake da karin 0.12 cikin 100 a cikin nahiyohin Afirka biyar a kowace shekara," in ji rahoton.

Hatta Afirka ta Kudu har yanzu tana da karancin kaso a kudaden shigarta na GDP daga masana'antu duk da kasancewarta a sahun gaba wajen habaka masana'antu a nahiyar.

Ya zuwa shekarar 2020, ma'aikatar masana'antu ta Afirka ta kudu ta samar da kaso 12 cikin 100 na kudaden shigar kasar, a cewar rahoton bankin baitul- malin kasar.

Koma bayan da aka samu

Abubuwa da dama sun taka rawa a koma bayan da aka samu wajen ci gaban masana'antu a nahiyar.

"Daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da cikas ga ci gaban Afirka a fannin masana'antu shi ne gazawa wajen samun riba a kudaden shiga," kamar yadda Dakta Isa Abdullahi masani kan tattalin arzikin kasa daga Jami'ar Tarayya ta Kashere a jihar Gombe na Nijeriya.

Kwararru na ganin akwai bukatar gwamnatin kasashen Afrika su kara himma wajen inganta fannin ilimin fasaha a tasakanin al'ummar matasan nahiyar. Hoto/Getty 

Kamal Tasiu Abdullahi, wani dalibin digirin digirgir a fannin tattalin arziki a jami’ar Istanbul, ya yi amanna cewa rashin sarrafa kudaden da ake samu daga kayayyakin da ake hadawa na daya daga cikin abubuwan da ke kawo cikas ga masana’antu.

"Rashin amfani da kudaden shigar da ake samu daga yawan kayayyakin da ake samarwa don bunkasa ci gaban masana'antu na taimakawa wajen rage yawan abubuwan da Afirka ke samarwa duniya," in ji shi.

Kamal ya yi nuni kan rashin ababen more rayuwa kamar sufuri da karancin samar da wutar lantarki a matsayin wasu daga cikin dalilan da ke haifar da tsadar samar da yawan kayayyaki a yawancin sassan nahiyar.

Kwararru sun bayyana rashin samun isasshen ilimi a fannin fasaha da kudade da kuma rashin daidaito a fannin siyasa daga cikin manyan kalubalen ci gaban masana'antu suke fuskanta.

Mafita

Duk da wadannan kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu, ana kyautata zaton cewa nahiyar Afirka ta na da karfin da za ta iya bunkasa masana'antu.

Akwai bukatar kasashen Afirka su ci moriyar al'ummar nahiyar sama da biliyan 1.2 ta hanyar yin cinikayya cikin 'yanci a tsakanin juna, a cewar kwararru: Hoto/ Getty

Rahoton Bankin Duniya a shekarar 2021kan habaka masana'antu a yankin kudu da hamadar sahara ya nuna cewa yankin ya samu gagarumin karin kashi 148 a ayyukan yi daga masana'antu daga cikin adadin mutana miliyan 8.6 a shekarar 1990 zuwa miliyan 21.3 a shekarar 2018.

Masana sun imanin cewa nahiyar za ta iya samun fiye da hakan ta hanyar hada kai da manyan masana'antun duniya masu daraja da kuma kafa manufofin da za su inganta yadda ake gudanar da ayyuka yadda ya kamata da rage gurbatattun yanayin kasuwanni da kuma inganta fasahohi akai-akai don inganta tattalin arziki.

Kazalika sun yi kari da cewa, akwai bukatar a samar da yanayin daidaito a harkar cinikayyar kasa da kasa a tsakanin kasashen nahiyar domin taimakawa masana'antu cin gajiyar kasuwar al'ummar Afirka mutum fiye da biliyan daya.

"Muna gudanar da kasa da kashi 20 cikin 100 na kasuwancinmu a Afirka, sannan muna gudanar da fiye da kashi 80 cikin 100 na kasuwancinmu a wajen nahiyar," in ji Dakta Isa, yana mai kari da kan cewa. "Yawan yin cinikaiyar a cikin nahiyar zai kara bunkasa ci gaban masana'antu."

Kamal ya ce za a iya cimma hakan ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar 'yancin cinikaiya nahiyar Afirka wato African Continental Free Trade Agreement (AfCFTA).

Dokta Isa ya ba da shawarar kan a ba da fifiko wajen samun ma'aikata masu basira da kwarewa aikace-aikace.

"Muna bukatar mu maido da iliminmu kan fasahar kere-kere da za ta kai ga samar da ci gaba maimakon mallakar takardar shaidar kammala karatu kawai," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Yarjejeniyar ita ce, idan har dukka sassan nahiyar suka yi aiki a tare, ba shakka miliyoyin mutane a fadin Afirka za su tsira daga kasadar kwarara zuwa nahiyar Turai da nufin samun kyakkyawar makoma, wanda a karshe ya ke zama hangen dala ba shiga birni ba.

TRT Afrika