An soma yakin Sudan ne a ranar 15 ga watan Afrilu bayan fafatawan sojojin Sudan da dakarun RSF. Hoto: TRT World  

Daga Coletta Wanjohi

Sudan, wacce ke fama rigingimu na fatan taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya MDD da aka tsara yi game da sanarwar Sakatare-Janar António Guterres wanda ya jaddada aniyar majalisar na tallafa wa kasar wadda ke yankin arewacin Afirka zai kai ga samar da "turba ta zaman lafiya da kwanciyar hankali".

Kalaman Guterres na zuwa ne a daidai lokacin da tawagar hadin gwiwa ta MDD da ke Sudan ke shirin kawo karshen wa'adin aikinta karkashin aikin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya karshe.

Ana iya cewa, karshen wani babi ya nuna mafarin wani a yankin kusurwar Afirka, inda dakarun da ke karkashin jagorancin shugaban rundunar sojin Sundan Janar Abdel Fattah al-Burhan ke ci gaba da fafatawa da dakarun RSF da Janar Mohamed Hamdan Dagalo ke jagoranta tun daga ranar 15 ga Afrilu na bara.

''Ya zuwa yanzu MDD ba ta shiga cikin lamarin rikicin sudan ba tukunna'' kamar yadda Mukaddashin Ministan Harkokin Waje a majalisar rikon kwarya na Sudan karkashin Janar Al- Burhan Ali Hussien ya shaida wa TRT Afrika.

"Duk wani yaki a duniya yana karewa ne a kan teburin tattaunawa. Har yanzu muna da burin samar da zaman lafiya," in ji shi.

Ko da yake kokarin shiga tsakani da kasashen yankin suke yi har yanzu bai samar da sakamako mai kyau ba tukuna, sai dai watakila furucin ministan harkokin wajen ne kawai hanya ta yarda karfin tattaunawa ba.

"Ba da jimawa ba sakatare- janar na MDD ya nada wakili na musamman wato (tsohon mataimakin firaministan Aljeriya Ramtane Lamamra) wanda a yanzu haka yake kokarin tattaunawa da masu ruwa da tsaki da manyan kasashen yankin, da kuma makwaftan Sudan don tsara wani abu, muna bukatar mu ga inda wannan shiri zai kai mu a ɗan gajeren lokaci, "in ji Hussien.

Rikicin Sudan ya raba sama da mutane miliyan 10 da muhallansu tare da wasu da dama da suka yi gudun hijira zuwa kasashe da ke makwabtaka kamar Chadi. / Hotuna Wasu

Daga cikin muhimman batutuwan da za a tattauna a zaman kwamitin sulhu na MDD mai zuwa ya hada da nemo hanyoyin da za su taimaka wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan tare da tabbatar da an ci gaba da kai kayan agaji ba tare da cikas ba.

Kazalika majalisar na iya yanke shawarar tsawaita wa'adin kwamitin ƙwararru kan takunkumin Sudan wanda zai kare a ranar 12 ga watan Maris.

Yarjejeniyar watan Mayu

Gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta ce maido da zaman lafiya kasar na daga cikin yarjejeniyar da bangarorin biyu da ke rikici da juna suka kulla wata guda bayan fadan ya barke.

"Wannan yarjejeniya ita ce zabi mafi kyau da ake bukata wajen fita daga yaki,'' in ji Ministan Harkokin Wajen Hussien yayin da ya ke batu kan yarjejeniyar tsagaita wuta na gajeren lokaci da kuma shirye-shiryen jin kai na ranar 20 ga Mayu, 2023 da brinin Jeddah ta jagoranta.

Masarautar Saudiyya da Amurka ne suka kulla yarjejeniyar.

''Matsayar ita ce, ƴan bindiga su bar duk wani gine-gine na gwamnati da kuma gidajen zaman al'umma saboda mutane su samu damar koma wa matsugunansu, sai dai ana su bangaren rundunar RSF ba ta mutunta sa hannun da ta yi a yarjejeniyar ba. yin haka kuwa ba zai kaimu ga ko'ina ba," in ji Hussien.

Fadar da babu ƙaƙƙautawa

Yarjejeniya da yunƙurin da aka yi na ganin Sojojin Sudan da RSF sun ja da baya ba su yi nasara ba.

Yayin da rikicin ya kusa cika shekara biyu, ƴan sudan na ci gaba da fuskantar tashin hankali da firgicin harbe-harbe alburusai.

Rahoton MDD ya ce "RSF ta samu gagarumun ci gaba, inda ta ƙwace iko da mafi yawan yankunan Darfur da yammacin Kordofan, da manyan yankunan Khartoum da Omdurman".

Wasu 'yan Sudan da ke neman mafaka a kasashe da ke makwabta da su, sun iso da raunuka. / Hoto: MSF

Kalubalen jin kai da rikicin ya haifar yana dada karuwa. A cewar MDD, kusan mutane miliyan 25 - akalla rabin al'ummar Sudan - na bukatar agaji.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da ayyukan jin kai ya yi kiyasin cewa mutane miliyan 10.7 rikicin ya raba da matsugunansu, ciki har da mutane miliyan tara da ke cikin kasar.

MDD ta bayyana hakan a mastayin " mafi girman rikici na gudun hijira a duniya".

Rahotanni daga cibiyar samar da bayanai da wuraren da ke fama da rikici sun nuna cewa sama da mutane 13,000 ne aka kashe a fadan.

"Matsalar ita ce kasashen duniya ba sa ba da isassun tallafi ga jama'a. Suna yawan magana amma taimakonsu kadan ne," in ji ministan harkokin wajen Hussien.

Kimanin mutane miliyan 1.7 ne daga Sudan suka nemi mafaka a kasashe da ke makwabta wadanda suka hada da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Chadi da Masar da Habasha da Libya, da kuma Sudan ta Kudu.

"Mu ƴan'uwa ne, mun bar iyakokinmu a bude ga masu neman mafaka, kuma muna maraba da su, har ma da wasu ƴan kasarmu da ke zama a Sudan da suke son dawowa," kamar yadda James Morgan, ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasashen duniya na Sudan ta Kudu ya shaidawa TRT Afrika.

Hukumomin agaji sun fuskanci tsaikon rashin samun damar shiga wasu sassan Sudan saboda fadan da ya hana raba kayayyakin agaji.

Hussien ya ce kamata ya yi su dora alhakin hakan a kan ‘yan bindigan, ba wai gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ba.

"A bangaren gwamnatin Sudan kuwa, muna iyakacin kokarinmu wajen ganin an kai kayan agaji, duk da cewa muna fama da yaki, kuma tattalin arzikin kasar ya tabarbare, muna taimaka wa ƴan gudun hijira a cikin kasar da ma masu neman mafaka a wasu wuraren," in ji shi.

"Misali a kasar Chadi, mun sayi abinci daga kasuwannin cikin gida, kan muka rarraba wa ‘yan gudun hijirar Sudan da ke kasar”.

Yunkurin shiga tsakani

A watan Janairun bana ne shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ya nada wani babban kwamiti kan Sudan.

A lokacin da tawagar mai mutane uku ta gana da Janar al-Burhan, rahotanni sun ce ''Sudan na da kwarin gwiwa kan hanyoyin da kungiyar Tarayyar Afirka za ta iya dauka, amma sai har kasar ta dawo da cikakken matsayinta na mamba kuma kungiyar ta dauke ta a haka.''

Ali Elsadig Ali Hussien, Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan na gwamnatin rikon kwarya ta kasar ya halarci taron  diflomasiyya na Antalya. Hoto: TRT Afrika

Tun daga ranar 6 ga watan Yunin 2019 ne kungiyar tarayyar Afirka AU ta dakatar da Sudan daga kungiyar.

Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU ne ya dauki wannan mataki bisa la'akarin da "kin kafa gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin farar hula" da kasar ta yi tun bayan ganawarsu ta farko bayan juyin mulkin ranar 11 ga watan Afrilu, 2019.

AU ta dage kan cewa "kafa gwamnatin rikon kwarya ta farar hula mai inganci" ita ce kadai mafitar rikicin Sudan.

Sai dai shirin gudanar da zabukan gama gari ya ci tura sakamakon rikicin da kasar ke fama da shi.

Yunkurin shiga tsakani na nahiyar ya gamu da cikas a lokacin da Sudan ta dakatar da matsayinta na zama mamba a kungiyar IGAD domin nuna adawa da gayyatar da aka yi wa Janar Dagalo zuwa taronta.

Kungiyar mai mambobi takwas ta dade tana aiki wajen ganin an sasanta tsakanin dakarun da ke fada da juna.

Sudan ta zargi kungiyar IGAD da kafa wani misali mai hatsarin gaske ta hanyar "keta 'yancin kanmu".

Makwabciyarta Sudan ta Kudu, wadda ta samu ƴancin kai daga Sudan a shekarar 2011, ba ta cire rai ba.

"Shugaban kasarmu Salva Kiir yana bakin kokarinsa wajen ganin ya gabatar da janar-janar din biyu da ke fada da juna a gaban tebirin tattaunawa.

Amma hakan bai samu ba, amma duk da hakan bai yi kasa a gwiwa ba," a cewar takwaran Hussein na Sudan ta Kudu.

AU ta yi imanin cewa ƴan Sudan ne kawai za su iya magance rikicin kasarsu, kuma abin da suke bukata shi ne goyon bayan yin hakan.

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan ita ma ta amince da hakan, tana mai cewa duk goyon bayan da makwabta da sauran hukumomi za su bayar, dole ne zaman lafiya ya fito daga ƴan Sudan da kansu.

TRT Afrika