Daga Dayo Yusuf
Akwai wani karin maganar Hausa da cewa "Idan ka ga gemun dan'uwanka ya kama da wuta, to ka shafa wa naka ruwa".
Wannan abu ne da za iya kwatance da shi a kowanne yanki na duniya, kuma za a iya fahimtar ma'anarsa daga gargadin da wani dan majalisar dokokin Ghana ya yi na cewar 'yan majalisar su yi a hankali, ko kuma su fuskanci fushin jama'a, kamar yadda ake gani a Kenya a tun watan Yuni.
Kenya sun dumama gari saboda yadda majalisar dokoki ta amince da doka mara kyau. Shugaban majalisa wannan babbar maana ce. Na ga yadda ka daki abokan aikinmu har sai da suka kai kasa."
A yayin da ake ta guna-guni da kus-kus-kus a tsakanin jama'a, dan majalisar ya ci gaba da gargadar abokan aikinsa cewa wannan ba batun dariya ba ne.
Ganin yadda matasa da ransu ya ɓaci suna shiga ginin majalisar dokoki, suna ƙone-ƙone, tare da tirsasa wa 'yan majalisa neman mafaka, ya zama wani babban kiran a tashi a farka ga kasashen nahiyar.
Kiran a dauki mataki
Tun bayan da matasa suka fara boren adawa da sabuwar dokar karin haraji a Kenya, kafafan sadarwa na zamani sun cika da sakonnin gargadar gwamnatoci kan su yi taka tsan-tsan game da yiwuwar fuskantar irin wannan lamari.
Masana suna alakanta zanga-zangar adawada karin haraji a Kenya da boren Larabawa.
"Bayan an zabe su, wakilan jama'a da dama na manta wa cewa zababbu ne su, kuma an zbe su ne don su hidimtawa jama'a." in ji Ade Daramy, yayin tattauna wa da TRT Afirka.
"Ba wai a iyakacin kenya ne kawai ba; mutane na son a saurare su, a kuma nemi shawarwarinsu. Batun shi ne kar ku yanke danyen hukunci da kanku."
Masana na bayyana matsalar na iya yaduwa a kasashen da gwamnatocinsu ba su da kunnuwan sauraren jama'a.
An fara gudanar da wasu -zanga-zanga a Afirka da suka dauki tsawon lokaci, da korafin jama'a kan yadda gwamnatocinsu suka yi biris da su, n Wamoto Wabete, wani kwamishinan 'yan sanda mai ritaya a Uganda.
Shata layi
"Darasi ne daga bangarori biyu. Ya zama dole gwamnatoci su yarda sun hau mulki ne don hidimtawa jama'arsu, su ma jama'a su fahimci cewa an zabi gwamnati ne ta halastacciyar hanya don ta wakilce si." Wamoto ya fada wa TRT Afirka.
Ga lamarin 'yan kasar Kenya, gargadi ga dukkan bangarorin biyu ya zama ruwan dare, kafin fara boren.
"Muna bukatar mu kula sosai yayin da muke kwatance," in ji Ade. "Yanayin Kenya na da bambanci. Lamarin na iya zama daya, amma hanyar tunkararsa da warware shi na iya bambanta."
Fushin jama'a ya shafi yadda ake gudanar da gwamnati da 'yancin amfani da 'yan sanda.
Ade ya shaida wa TRT Afirka cewa "Mun ga me ya faru a Sanagal a lokacinda matasa suka yi kokarin zanga-znga ga gwamnati. An dinga murkushe mutane da ya kai ga rasa rayuwa da da dama."
Matasa a Siyasa
Yana da ra'ayin cewar wannan dama ce ga matasa ta su shiga siyasa a kasashensu daban-daban.
"Ina da yakinin suna da sha'awar shiga siyasa, duba ga bayanan da aka tattara. Idan karin matasa suka hada hannu waje guda a wata jam'iyyar siyasa ko suka kafa tasu jam'iyyar, za su iya kawo sauyi."
Tun bayan fara zanga-zangar adawa da dokar karin haraji a ranar 25 ga Yuni, Shugaba William Ruto ya janye wasu daga cikin bukatun gwamnati.
"Alama ce mai kyau yadda gwamnati ta saurari jama'a, ta kuma bayyana niyyarta na ba wasu daga cikin abubuwan da suka bukata. Amma ya kamata masu zanga-zangar su fahimci meye ya dace. Ba ka bukatar tsawaita zanga-zangar har ta zamo wani abu mara kyau, hakan na iya bata kokarin naka baki daya." in ji Wamoto
Matasa da dama a fadin Afirka sun nuna yaba wa a yayinda zanga-zangar ta Kenya ta yadu sosai.
Amma Ade ya yi gargadin cewa ya kamata irin wannan zanga-zanga ta zama mataki na karshe, a yi ta a lokacin da tattauna ta ci tura.
Ya fada wa TRT Afirka cewa "Ni da ba Saliyo nake kuma na ga illar zanga-zanga. Na gargadi mutane kan kada su yi fatan ganin abu irin haka. Rikici koyaushe mummuna ne."