Daga Mazhun Idris
Afirka ta Kudu ta gurfanar da Isra'ila a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, bisa hare-haren Isra'ila kan Gaza, wanda kasar Afirka ta Kudun ta ce "sun kai matakin kisan kare-dangi".
Rikicin na Gaza yana faruwa ne a can Gabas ta Tsakiya, amma batu ne da ya damu kasashen Afirka, har ta kai wata kasa a nahiyar tana magana kan batun.
Matakin na Afirka ta Kudu yana nuni da muhimmanci da kuma tasirin muryar kasashen Afirka a batutuwa da siyasar duniya bakidaya.
A birnin New York, inda shedikwatar Majalisar Dinkin Duniya take, kasashen Saliyo da Aljeriya sun samu zama sabbin kasashen Afirka da suka shiga Kwamitin Tsaro na MDD a matsayin na wucin-gadi, wanda yake da mambobi-15. Hakan ya sanya adadin mambobin Afirka ya kai uku.
Dr Tasiu Magaji, wani masanin kimiyyar siyasa ne da ke Jami'ar Bayero a Nijeriya. Yana kallon wannan batu a matsayin mai muhimmanci a siyasar duniya. Kuma ya yi hasashen cewa kasancewar kasashen Afirka a kwamitin zai karfafa samar da daidaito da yin adalci.
"Kasashen da ba na dindindin ba wadanda kuma ba su da wata manufa kan rikice-rikicen duniya, idan ba neman zaman lafiya ba, za su nemi ganin Kwamitin Tsaron yana adalci a ayyukansa. Za su yi tasiri kan muhawarar duniya kuma su shigo da batutuwan da suka shafe su," Dr Magaji ya fada wa TRT Afrika.
Shigo da sabbin dabaru
Saliyo da Aljeriya suna cikin sabbin kasashe biyar da Babban Zauren MDD ya zaba don shiga kwamitin Tsaro, kan wa'adin shekaru biyu, wanda zai fara a wannan watan. Kasar Mozambique, ta uku a Afirka a Kwamitin Tsaron tana ciki har karshen shekarar 2024.
Karin wakilcin da Afirka ta samu a zauren da ya fi kowanne muhimmanci a Majalisar Dinkin Duniya yana zuwa ne tattare da wasu nauye-nauye da fatan cimma buruka.
"Saliyo da Aljeriya za su iya neman kawo karin bayyana adalci a MDD da kuma muhawara kan samar da zaman lafiya, da tsarin saka takunkumi, da sauran matakai da Kwamitin Tsaron ke dauka," a cewar Dr Magaji.
A yunkurin neman zaman lafiya da tsaro, yawaitar kasashe mabambanta a Kwamitin Tsaron, ana sa ran zai haifar da samuwar fahimtar batutuwa da suka kebanci yanki, saboda mabambantan mambobi suna da shawarwarin tsaro da za su bayar a zauren.
Dr Magaji ya kara da cewa, Saliyo tana da kwarewa kan rikice-rikice da samar da zaman lafiya a Yammacin Afirka, yayin da Aljeriya take da kwarewa kan magance matsalolin tsaro a Arewacin Afirka.
Wani bangaren shi ne habaka muhawara tsakanin kasashe da ke da matsayin mambobin wucin-gadi, wanda zai haifar da hadin-kai tsakanin mambobin MDD, musamman kan batutuwan da suka shafi yankunansu.
Hadin-gwiwa wani abu ne da da ke gina maslaha da samar da kyakkyawan hukunci kan kalubalen duniya da na wasu yankuna kebabbu. Wannan ya hada da batutuwan da ake watsi da su, wadanda ba dole su zamo kan-gaba ba wajen mambobin dindindin na zauren.
Dr Magaji ya yi kira ga Saliyo da ta gabatar da batun tasirin sauyin yanayi kan tsaro a Yammacin Afirka. A wani bangaren kuma, Aljeriya za ta iya nuni kan bukatar mayar da hankali kan masu zuwa ci-rani a Turai, da sauran batutuwan da ke damun Arewacin Afirka.
Neman daidaito
A hakikanin gaskiya ko da mafi rinjayen mambobin Kwamitin Tsaron sun goyi bayan wani mataki, kasashe biyar suke da shi, wato Amurka, da Birtaniya da Faransa da Rasha da China za su iya hawa kujeran na-ki. Wannan ne ya sa kasashen Afirka suke ta neman samun kujerar dindindin da kuma ikon hawa kujerar na-ki a zauren.
Dr Magaji ya yi bayanin cewa, "Saka karin kasashen Afrika a Kwamitin Tsaro shi kadai ba dole ya kara yiwuwar samun kujeran dindindin ba ga nahiyar. Samun matsayin dindindin batu ne mai sarkakiya, wanda ke bukatar goyon baya daga sauran mambobin MDD".
Kasashen Afirka sun farar da kudure-kudure da dama, har da kudurin Ezulwini Consensus na 2005, wanda yake yakin neman kawo sauyi a zauren Kwamitin Tsaro na MDD. Tarayyar Afirka ta yi ta neman kawo sauyi a majalisar tun shekarar 1999 da aka gabatar da shelar Sirte Declaration.
Duk da cewa kasashen Afirka 54 sun kai kashi 28 cikin dari na adadin mambobin Majalisar Dinkin Duniya, nahiyar ba ta da kujerar dindindin ko da guda, a Kwamitin Tsaro.
Cikin kasashe goma masu kujerar wucin-gadi a zauren mai kasashe-15, Aljeriya da Saliyo sun cike guraben da kasashen Gabon da Ghana suka bari, bayan da wa'adinsu na shekaru biyu ya kare a watan Disambar 2023.
Kason da wakilan Afirka suke da shi a zauren mai kasashe 15 yanzu ya kai kashi 20 cikin dari.
Amfani da dama
"Akwai wani tsarin kawo sauyi a MDD wanda ke gudana kuma yake da manufar sabunta tsarin majalisar da kuma yadda take zartar da hukunci," cewar Dr Magaji. "Wannan zai ba da dama ga Afirka ta gabatar da kudurin neman kujerar dindindin."
Masu sharhi suna ganin MDD tana bukatar mutunta muryar kasashen Afirka, wanda hakan zai faru ne kadai idan nahiyar tana da tabbataccen mazauni a zauren majalisar, wanda zai dace da matsayin Afirka a duniya.
Nuna muhimmanci ga Afirka a harkokin duniya ya kamata ya wuce matsayin saka kasashen Afirka a zauren Kwamitin Tsaro lokaci bayan lokaci. Babban manuni shi ne idan aka ba Afirka mazaunin dindindin, ko da maras ikon hawa kujerar na-ki ne.
Tabbas, duniyan nan ba ta kasashe biyar ba ce, kuma kamar yadda Dr Magaji ya jaddada, "tsarin da ake da shi yanzu a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba shi da daidaito, kuma babu dimokuradiyya cikinsa".