Daga Abdulwasiu Hassan
Bazuwar haramtattun makamai a hannun mutanen da ba hukuma ba, ta jefa Afrika cikin yaƙi da wani abokin gaba da ba a ganinsa, da ke addabar nahiyar.
Kama daga Somalia da Habasha, da Mali, da kuma Sudan, zuwa Sudan Ta Kudu, da Nijar, da Nijeriya da kuma Libiya, safarar haramtattun makamai na ci gaba da ƙaruwa, da haddasa tashin hankali da rikice-rikice da kuma aikata manyan laifuka a sassa masu yawa na nahiyar.
Miliyoyin mutane sun rasa rayukansu a wannan tashin hankalin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, wanda ya haɗa da ta'addaci, yayin da ƙarin wasu miliyoyin mutanen sun rasa muhallansu.
Wannan shi ne girman tashin hankalin da yake hana nahiyar cim ma muradin 16.4, wani ɓangare na Muradin Majalisar Dinkin Duniya A Kan Ci-gaba Mai Ɗorewa, domin rage haramtattun hanyoyin samar da kuɗaɗe da makamai zuwa shekarar 2030.
Abin tambaya a nan shi ne, ta wacce hanya ake samar da waɗannan haramtattun makaman da ke ratsawa tsakiyar Afrika?
Amsar ba mai sauƙin samuwa ba ce, amma alƙaluma sun bayyana wani ɓangare na batun.
Makamai da ke hannun fararen-hula
A cewar wani bincike da Cibiyar Tattara Bayanai A Kan Ƙananan Makamai, mai ƙawance da Cibiyar Nazari A Kan Harkokin Ƙasa Da Ƙasa Da Ci-gaba, mai mazauni a Geneva, adadin ƙananan makamai da ke hannun fararen-hula a Afrika ya kai sama da miliyan 40 a 2017.
Ƙasashen Yammacin Afirka su ne kan gaba da kimanin makamai miliyan 11 daga cikin waɗancan - wato miliyan 10,972,200, jimilla. Sai Afrika ta Arewa mai bi mata da kimanin makamai miliyan 10,241,000.
A Gabashin Afrika, makamai miliyan 7,802,000 ne suke hannun fararen-hula, yayin da aka samu miliyan 6,012,000 a yankin Afrika ta Kudu.
Yankin Afrika ta Tsakiya ne cikamakin jerin yankunan, wanda ke da makamai masu lasisi miliyan 4,981,000 a hannun fararen-hula.
Wataƙila alƙaluman su tayar da hankali, amma ba komai ba ne, idan aka kwatanta da alƙaluman wasu yankunan da dama, da ke wajen nahiyar.
Afrika na da 5% na adadin makamai da ke hannun fararen-hula a faɗin duniya. A nahiyar, 3.2% na fararen-hula na riƙe da ƙananan makamai, a cewar Cibiyar Tattara Bayanai A Kan Ƙananan Makamai, mai ƙawance da Cibiyar Nazarin Harkokin Ƙasa Da Ƙasa Da Ci-gaba, ta Geneva a Switzerland.
Wannan ai ba wani abu ba ne, idan aka kwatanta da 46.3% a ƙasashen yankin Amurka.
Amma a nahiyar da har yanzu akwai yankunan da babu iko na hukuma a cikinsu, ko da ɗan wannan adadin ƙananan makamai, zai kasance babban hatsari ga miliyoyin mutanen da ba sa riƙe da makamai.
A jibge haramtattun makamai cikin su, ai kamar wata nakiya ce da aka dasa, ake jira ta tashi.
Hanyoyin da ake amfani da su wajen safarar haramtattun makamai
Masharhanta sun yi imanin cewa, haramtattun makamai na shiga hannun mutanen da ba hukuma ba, galibi ta hannun gurɓatattun jami'an tsaro da kuma ƴan fasa-ƙwauri.
"Abubuwa guda biyu ne suke ta'azzara bazuwar makamai a sassan Afirka daban daban - rikice rikicen cikin gida da kuma durƙushewar gwamnatoci a wasu ƙasashen," wani masanin tsaro, Guruf Kaftin Sadeeq Garba mai ritaya, ya gaya wa TRT Afrika.
Da zarar an fara rikici, lokaci kawai za a jira, kafin haramtattun makamai su faɗa hannun da ba su kamata ba, a jefa rayuwar fararen hula cikin hatsari.
"Muna da shaidun da ke nuna cewa, ana sace makamai da albarusai daga rumbunan makamai na sojoji da ƴan'sanda.
Akwai ƙa'idojin bayar da makamai da albarusai na gwamnati, amma wani lokacin ana watsi da su," in ji Shehu.
"A matsayina na wanda ya yi aikin soja, na san cewa akwai tsayayyiyar doka da ke tabbatarwa idan jami'ai za su fita kowane aiki, za a ba su wasu makamai masu lambobi a jikinsu.
"Idan akwai buƙatar wani ya yi harbi, ya kamata ka ɗauko kwanson albarusan da ka harba, ka dawo da shi."
Jami'an tsaro ba su kaɗai ba ne ke da alhakin sanadiyar shigar makamai hannun miyagu. Ita ma harkar safarar makamai ta zama ruwan dare.
Ɗaya daga cikin hanyoyin safarar makamai ita ce daga Libya zuwa ƙasashen Afrika yamma da Sahara, abin da shugabanni, kamar tsohon shugaban kasar Nijeriya, Muhammadu Buhari suka zarga da haddasa tashin hankali a yankunansu.
A ƙasidarta ta 2019, Cibiyar Tattara Bayanai A Kan ƙananan makamai, ta lissafo hanyoyin fasa-ƙorin haramtattun makamai da dama, kamar tsakanin Benin da Najeriya da Burkina Faso da Cire d'voire, da Guinea Bisau da Senegal, da Gambia da Senegal, da Liberia da Saliyo/Guinea da Algeriya da Mali, da Chadi da Nijar, da Najeriya da Nijar da yankin Tafkin Chadi da kuma Nijar da Mali.
Toshe Kafofin
Masana tsaro sun jaddada cewa, muhimmin abu wajen hana bazuwar makamai da albarusai, shi ne ƙarfafa matakan bayar da makamai a rumbunan makamai.
"Game da makamai da albarusai da tuni suka shiga hannun miyagu ko ɓarayin daji, hanya ɗaya tilo da za a kawar da su, ita ce ta yin amfani da dabarar kai samame," Shehu ya gaya wa TRT Afrika.
"Mutanen da ba su da niyyar yin ta'adi za su iya sayen makamai ba tare da bin ƙa'idoji yadda ya kamata ba, saboda hakan ne ke faruwa a inda tsaro ya yi rauni. Ya wajaba ka saka ingantaccen tsari na bayar da lasisi."
Shehu ya yi sauri ya ƙara da cewa, kar a yi watsi da harkar sayarwa da sayen makamai domin halattaccen sha'ani, idan ba haka ba kuma ƙilu ta jawo bau.
Akwai muhimmanci a saka tsauraran dokoki, musamman domin a tabbatar makamai ba su shiga hannun miyagu ba."
Ita ma Cibiyar Tattara Bayanai A Kan Ƙananan Makamai, ta bayar da shawarar matakai da dama da ya kamata a ɗauka domin yaƙar fasa-ƙwaurin makamai.
Sun haɗa da ƙarfafa aiki tare tsakanin hukumomi na ƙasa da ƙasa da kuma masu sama wa ƙasa tsaro, da inganta hanyoyin tattara bayanan sirri da kuma amfani da hukumomin MDD a yankin wajen kyautata fahimta da ɗaukar mataki game da bazuwar haramtattun makamai.
Yayin da gwamnatoci suka sabunta alƙawuransu a Makon Raba Mutane Da Makamai Na Majalisar Dinkin Duniya (Oktoba 24 zuwa 40) don magance barazanar haramtattun makamai da ke ƙaruwa, mutane a faɗin Afrika suna fatan za su ci gaba da gudanar da harkokin gabansu ba tare da fargaba ba.