Daga Pauline Odhiambo
Ciki da haihuwar yara ƙanana a yankin Ashanti na Ghana na fuskantar ƙalubale game da yin awo, musamman ma injin haska mahaifa don duba lafiyar jariri.
"Afri Emo", wanda ke nufin "Barka da arziki bayan nasarar fita daga wani ƙangin wahala", na bayyana irin hali da yanayin da mata ke shiga wajen raino da haihuwar ciki.
Abin baƙin ciki, ba koyaushe ne ake samun ƙarshe mai faranta rai ga matan karkara a Ghana ba, inda kayan kula da lafiyar masu juna biyu suka yi ƙaranci, abin da ke janyo mutuwa bayan haihuwa.
Edmund Atweri, mai shekaru 36 da ke aikin jinya kuma daraktan zartarwa na wata ƙungiya mai zaman kanta da ake kira 'Divine Mother and Child Foundation' (Gidauniyar Iyaye Mata da Yara Ƙanana), na gudanar da aikin samar da kayan kula da lafiya ga mata masu shirin haihuwa a wasu yankunan Ghana da ke da nisa.
"Muna zuwa ƙauyuk don gwada mata masu juna biyu da injin zamani na ultrasound, matan da ba za su iya biya a manyan asibitoci ba. A wasu garuruwan, asbiti mafi kusa na da nisan kilomita da yawa daga inda suke," Edmund ya fada wa TRT Afrika.
Dauke da injin haska mahaifa mai dadin aiki, Edmund na yawan zuwa yankunan karkara a motarsa inda yake duba matan da ke da juna biyu.
Ya ce, "hanyoyin kauyukan ba su da kyau, wanda ke nufin a wasu lokutan sai na ajiye motar a lokacin da hanyar ba za ta biyu da mota ba. Sai na hau babur ko jirgin ruwan kwale-kwale don karasawa kauyukan da ke tsibirai.
"Wajibi ne na yi wannan tafiya saboda na san irin halin da matan yankunan ke ciki da yadda suke tsananin bukatar injin na ultrasound."
Awon ciki don riga-kafi
Ana amfani da fasahar ultrasound don auna ciki, da duba girma da lafiya jariri, da kuma duba yiwuwar wata matsala ga mahaifiyar.
Duk da cewa wannan gwaji ba zai zama daidai dari bisa dari ba, amma wani tagomashi da yake da shi shi ne yadda ba shi da wata illa, ba zafi, kuma ba ya cutar da uwa da jaririn da ke cikin ta.
Duk da bukatar auna mata don riga-kafi, a yankuna da dama babu irin wadannan injina na ultrasound. Mafi yawancin mata masu ciki na dogara kan hanyar gargajiya don bukatun haihuwar jaririansu.
Wani rahoto da USAID ta fitar a 2024 ya bayyana cewa kashi 18 na mata masu juna biyu na rasa rayuka a Ghana, kuma za a iya kawar da hakan.
A 2023, mutuwa yayin haihuwa a Ghana ta kai mata 243 a duk mata 100,000. Adadin ya ragu zuwa 240 a shekarar da ta gabata. Hasashen da aka yi na 2025 da 2026 kuma shi ne mutane 237 da 234.
Ungozoma na gargajiya
Kamar yadda mata da dama ke haihuwa a kauyukan Ghana, Edmund na lissafa kansa a matsayin wanda ya yi nasarar tsallake mutuwa yayin haihuwa.
"An haife ni a wani ƙaramin ƙauye ƙarƙashin kulawar ungozoma. Na girma a kauyen kuma na ga mata masu shirin haihuwa na ziyartar wannan mata. Na girgiza matuka ganin cewa wasu matan na zuwa wajen matar a yayin da suke zubar da jini sosai, kuma wasun su na mutuwa ma a yayin haihuwar," ya fada wa TRT Afrika.
"Wannan ne abin da ya sanya na karanta aikin jinya. Ina son na ba wa mata da yara da yawa damar tsira a rayuwarsu."
A yayin da yake samun horo, Edmund ya ƙware kan aikin jinyar marasa lafiya a karkara, don samar da kula ga lafiyar masu juna biyu a yankunan da ba sa samun damar hakan.
Matsalolin juna biyu
A lokacin da ya yi aiki a matsayin ma'aikacin jinya, Edmund ya ga irin haɗarin da ake fuskanta a lokacin da mace ke da juna biyu.
"Daya daga cikin lokutan da ba zan manta da su ba shi ne lokacin da muka ziyarci gundumar Atiwa a gabashin Ghana. Mun hadu da wata mace da ke da ciki na tsawon watanni bakwai. A gwajin baya da aka yi mata an fada mata za ta haifi 'yan biyu. A lokacin da muka duba ta, mun gano 'yan biyun sun mutu a ciki," in ji shi.
Abin da muka gano ya gigita kowa matuka saboda bayanan gwajin da suka gabace shi.
"A lokacin da muka haska cikin, matar ta fada mana tuni ta riga ta sayi kayan jarirai na 'yan biyun da ba a haifa ba. Bakin cikin da ta nuna a lokacin da ta samu labarin yaran sun mutu na ta bibiya ta."
A lokacin nakuda da ma farkon daukar ciki, mata da dama a yankunan karkarar Ghana na dogaro kan babura a matsayin abin hawa. Wadannan babura na tafiya kan hanyoyi marasa kyau da ke da gargada, wanda hakan na cutar da mata masu juna biyu, musamman wadanda cikin bai yi kwari ba.
"Lokacin da cikina ya kai kusan watanni uku, na je kasuwa don sayen kayan abinci kuma na hau babur a hanyar dawowa gida. A lokacin da na zo gida, sai na fara zubar da jini," in ji Adwoa Boagye mai shekaru 32.
"Likitan matan da na ziyarta ya auna tare da haskawa don tabbatar da jariri na nan kalau. Daga nan, sai ya fada min cewa na daina hawa babura idan ina da ciki. Na bi shawararsa inda na haihu watanni hudu baya ba tare da wata matsala ba."
Tsarin kula da lafiya
Edmund ya kudiri niyyar kyautata yanayin kula da lafiyar mata masu ciki da ba su da hali, ciki har da samar da tsarin sufuri marar hatsari a yankunan karkara na Ghana.
Ya dogara kan neman kudade daga ma'aikatar lafiya ta Ghana, da daidaikun mutane masu bayar da tallafi da kungiyoyi masu zaman kansu da suke aiki tare.
A yayin da ya yi nasara da samun cigaba sosai, har yanzu ana bukatar aiki da kayan aiki da yawa don kawar da kalubalen da ke damun fannin kula da lafiya.
"Duk da mun samar da awo da ultrasound kyauta, har yanzu akwai mata da yawa da dole su dinga zuwa asibiti don yin gwaje-gwaje da awo. Shirina shi ne na hada dukkan wadannan abubuwan a waje guda, sannan na samu motar hawa ta aiki kawai," in ji Edmund.
"Ina samun karfin gwiwar yin wasu abubuwan da yawa saboda ina son tabbatar da cewa na daina ganin ana rasa rayuka yayin haihuwa."