Matakin na Amurka ya zo ne kwanaki kaɗan bayan China ta karbi baƙuncin ɗaya daga cikin manyan tarukanta da Afirka a Beijing.  Hoto: Reuters  

Daga Kazim Alam

Matakin da Amurka ta ɗauka na goyon bayan samar da kujeru biyu na din-din-din ga ƙasashe Afirka a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC) a yanayin da ake ciki wani yunkuri ne na mayar wa China martani kan komai, a cewar wani tsohon jami'in diflomasiyyar Afirka.

Bayan kujeru biyu ga kasashen Afirka da ta nuna goyon bayanta akai, Amurka ta kuma ba da shawarar samar da wata kujera ta karɓa-karɓa ga ƙasashen dake ƙananan tsibirai.

Ɗaya daga cikin sassan MDD mafi ƙarfi - akalla a ka'idance- Kwamitin Tsaron na da alhakin samar da tsaro da zaman lafiya a duniya, kuma yana da karfin saka takunkumai da hana saye ko mallakar makamai.

Kazalika zai iya ba da umarnin amfani da ƙarfi, kuma duk matakin da ya ɗauka zai shafin dukkan ƙasashe mambobin majalisar.

Matakin na Amurka ya zo ne kwanaki kaɗan bayan China ta karbi baƙuncin ɗaya daga cikin manyan tarukanta da Afirka a birnin Beijing, wanda ya samu halartar babban sakataren MDD Antonio Guterres.

''Mai yiwuwa babban dalilin sauyin matsayin Amurka game da batun samun wakilcin Afirka a Majalisar Dinkin Duniya shi ne don ta mayar wa China martani sannan da karin tasirin huldar Rasha a Afirka,'' kamar yadda Andebrhan Welde Giorgis, Tsohon jakadan Eritrea a Belgium, Faransa da Birtaniya, ya shaidawa TRT World.

A yanzu haka dai China ita ce babbar abokiya a fannin tattalin arziki da cinikayya a nahiyar Afirka.

Beijing ita ce babbar wadda ke ba da lamuni ga Afirka, inda kasashe masu tasowa a fadin nahiyar ke ƙara ɗogaro kan kudaden China don biyan bukatunsu na samar da ababen more rayuwa da makamashi.

Fiye da ƙasashen Afirka 50 ne suka hallara a birnin Beijing a makon da gabata domin halartar babban taron China da Afirka.

Don ƙara ƙarfafa ikonta a matsayinta na ƙasa mai ƙarfi da ke tasowa wajen karawa da Amurka a duniya, shugaban China Xi Jinping ya yi alƙawarin ba da tallafin kuɗi na dala biliyan 50 ga nahiyar Afirka, kana ya ɗauki alwashin haɗa kan al'ummar nahiyar don zama 'mai ƙarfin gaske''.

''Yana da ƙyau a yi a la'akarin da tasirin China a Afirka a cikin 'yan shekarun nan wanda ke nuna ''tsananin kishi da ke ara tasowa'' a cewar Giorgis shugaban kungiyar kare hakkin al'ummar kasar Eritriya wato Eri-Platform.

Masana sun ce Amurka na son gyara alaƙa da Afirka ne, la'akari da yanda ƙasashen nahiyar da dama suka nuna rashin jin daɗin su ga Washington bisa goyon bayanta ga yakin da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda ya yi sanadin kashe mutane sama da 41,000 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi nazari kan shirye-shiryen jawabin da jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta gabatar a ranar Alhamis.

An ba da rahoton cewa, Amurka za ta ba da sanarwar goyon bayanta a hukumance kan daftarin shawarwarin don yin garambawul ga Yarjejeniyar MDD don fadada Kwamitin Tsaro na Majalisar.

Ƙasashe 54 ne daga cikin 193 mambobin Majalisar Dinkin Duniya daga Afirka suke.

UNSC na da mambobi 11 ne a lokacin da aka kafa MDD a 1945, adadin ya ƙaru a shekarar 1965 zuwa mambobi 15.

Sannan ya unshi zaɓaɓɓun ƙasashe 10 waɗanda suka rike matsayin na tsawon shekaru biyu baya ga mambobi biyar na din-din-din wato- Rasha da China da Faransa da Amurka da Birtaniya- waɗanda duk suke ikon fada aji na veto.

Wakiliyar na Amurka ta ce Washington ba ta goyon bayan faɗaɗa ikon veto fiye da kasashe biyar da ke rike da ita a halin yanzu.

Wannan batu ne na cece-kuce kamar yadda kungiyar Tarayyar Afirka ta yi imanin "cikakkiyar wakilcin Afirka a Kwamitin Tsaron" na nufin samun kujeru biyu na din-din-din da ke da dukkan hurumin... "ciki har da samun ikon fada aji ".

Giorgis ya ce rashin samun matsayin kasashen Afirka biyu a cikin ƙasashen masu ikon fada a ji a Majalisar Dinkin Duniya ba zai yi “muhimmanci ba ko kadan”.

Matsayin zama mamba mara ikon fada a ji da za a baiwa kasashen Afirka a UNSC ba zai banbamta matsayin da na mabobin 10 da ke da kujera da ba na din-din-din ba, waɗanda ba su da wani "tasiri ba" kan muhimman batutuwan yaƙi da kuma samar da zaman lafiya ba, in ji shi.

"A yayin da ake koƙarin yin garambawul a UNSC, ya kamata Afirka ta ƙara kaimi wajen samun matsayin na Veto'', a cewar Giorgis.

La'akari da yawan jama'arta da kuma karfin tattalin arziki da kuma kwanciyar hankali na cikin gida da suke da su, manyan ƙasashen da ake fafutukar neman kujerun biyu na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya su ne Nijeriya da Afirka ta Kudu da Masar da kuma Aljeriya, in ji shi.

"Abin da ake buƙata shi ne cikaƙƙen sake fasalin tsari da yanayin ayyukan MDD gaba ɗaya da kuma UNSC musamman don daidaita su da yanayin da duniya ke ciki wanda ya samo asali tun 1945," in ji shi.

TRT World