Daga Sylvia Chebet
Tarihi gabaɗayansa ya ƙunshi tattaro bayanai game da abubuwan da suka faru. Kowane abu da ya faru yana wakiltar wani lokaci ne keɓantacce, muhimmin al'amari ko kuma wani muhimmin mataki da idan aka haɗe su waje guda, suke bayyana cikkaken labari game da rayuwarmu gaba ɗaya.
Uƙubar da Gaza ke ciki a sakamakon martanin isra'ila na kisan kiyashi babu ƙaƙƙautawa da ta mayar kan hare haren kwanton ɓauna da mayaƙan Hamas suka kaddamar ranar 7 ga watan Oktoba yana nuni da wannan alaƙa da ke haɗe mutanen nahiyoyi, na da da na yanzu da ma na nan gaba.
Yayin da yankin Gabas Ta Tsakiya ke kan gaɓar tsunduma cikin yaƙi gadan-gadan, inda tuni Iran ta bi sawun masu mayar da martani kan yaƙin da Isra'ila ta kaddamar, wane abu ne game da tashin hankalin na Falasdinawa da ke tunatar da Afrika game da azabtarwar da ta fuskanta a baya?
An kashe Kusa mutane 50,000 a Falasɗinu, galibinsu mata da ƙananan yara, yayin da Isra'ila ke yunƙurin kawar da Hamas ta kai hare hare ta sama da jefa bamabamai ta ƙasa babu ƙaƙƙautawa.
Adadin mutanen da suka mutu ya kusa ya kai na kisan kiyashin Namibia sama da shekaru ɗari da suka gabata, yayin da dakarun Jamus suka halaka asalin ƴan ƙabilun Herero da Nama su 70,000 a ƙoƙarin da suke yi na faɗaɗa Daular Jamus.
David Monyae, mataimakin farfesa a fannin kimiyyar siyasa da hulɗar ƙasa da ƙasa a Jami'ar Johannesburg, ya yi imanin cewa abin da ke faruwa a Falasɗinu shekara ɗaya kenan yanzu, ya bayyana munin kisan kiyashin da Jamus ta aikata a Namibia tsakanin shekarun 1904 da 1908.
Monyae yana kallon yaƙin da Isra'ila ke yi da Falasdinawa a matsayin wani yunkuri na gangan na "rusa tarihin al'umma - rusa masallatai da makarantu da maƙabartu da ma duk wani abu da ke bayyana al'umma ta fuskar al'adarsu da kundayensu da ma tunaninsu".
Ƙuncin Falasɗinawa
Dabarar rusa matsugunai da Isra'ila ke amfani da ita ta samar da Falasdinawa kimanin miliyan biyu da ba su da matsuguni kuma talauci ya musu kanta.
Yayin da ƴan Namibia suka yi fama da abin da aka sani da kisan kiyashi na farko a ƙarni na ashirin a hannun dakarun Jamusawa, maƙwabtansu a Afrika ta Kudu za su fuskanci babin tashin hankali na wariyar launin fata da aka fara daga 1948 zuwa 1994 ƙarƙashin gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya.
Aƙalla ƴan asalin Afrika ta Kudu su 21,000 ne za a kashe a tashin hankalin siyasa da ya wakana, yayin da sauran al'ummar suka sha fama da wariyar launin fata.
"Ina tunanin mun ga wasu kisan kiyashin da Turawan mulkin mallaka suka aikata - Birtaniya musamman - ko a Kenya ne a kan Mau Mau, a Uganda ko Zimbabwe," Monyae ya bayyana.
A Congo, dakarun Belgium ƙarƙashin Sarki Leopold suna sare hannayen mutane.
A cewar Monyae, kisan kiyashin da ake yi a Gaza na tunatarwa game da abin da yawancin Afrika ta yi fama da shi. Ƴan mulkin mallaka sun azabtar da su tsawon gwamnan shekaru.
Mulkin wariyar launin fata a Afrika ta Kudu sun yi amfani da irin wannan dabarar - yin amfani da karfin tuwo wajen saka kowa ya yi ladaf.
"Mun taɓa ganin haka, mun san mene ne shi, kuma muna magana babu tantama cewa abin da muka gani wariyar launin fata ne. Tsantsar wariya ce bisa ƙyamar fatar mutum," Monyae ya faɗi haka game da abin da ke faruwa a Gaza.
Ya yi Allawadai da abin da su ma Hamas suka yi. "Hakan ba yana nufin mun yarda da harin rashin imani a kan Isra'ila ba ne, musamman ma fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, irin wanda Al Qassam Brigade na Hamas suka ƙaddamar ranar 7 ga watan Oktoba shekarar s 2023. Muna allawadai da tashin hankali ko wane ne ya haddasa shi.
Martani farko bisa Shari'a
Ƙasar Monyae ta asali, Afrika ta Kudu, ta shigar da ƙara a kan Isra'ila a Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya (ICJ) ranar 29 ga watan Disamba shekarar 2023, kusan watanni biyu da fara yaƙin, domin amsa tuhumar aikata laifin kisan kiyashi a Gaza.
Yayin da za a iya kwashe shekaru kafin a yanke hukunci, Afrika ta Kudu ta gabatar da buƙata ta wucin gadi da ta nemi ICJ ta umurci isra'ila ta dakata da kai hare harenta a Falasɗinu saboda ta saɓa wa Yarjejeniya Kan Kisan kiyashin ta shekarar 1948.
ICJ ba ta amince da hakan ba bisa la'akari da ƴancin da Isra'ila ke da shi na kare kanta biyo bayan harin da Hamas ta kai mata na 7 ga watan Oktoba 2023.
Amma dai, kotun ta yarda cewa yanayin da ake ciki a Gaza mummunan bala'i ne.
Mai Shari'a Joan Donoghue ta lura cewa bala'in da yara ke fuskanta babban abin takaici ne sannan ta umurci isra'ila da ta ɗauki duk matakan ganin ta kauce wa ayyukan kisan kiyashi.
Sai dai Kotun ta Majalisar Ɗinkin Duniyar ba ta da hurumin aiwatar da umurnin nata.
Hare haren na Isra'ila a Gaza na ci gaba babu ƙaƙƙautawa na tsawon shekara kuma ya bazu zuwa Rafah da West Bank da aka mamaye da kuma ƙasashe masu makwabtaka na Lebanon da Yemen da Syria da kuma Iran.
"Duk yaƙe yaƙe munanan abu ne, amma wannan shi ne mafi muni da na taɓa gani, musamman dabarun da wanzazziyar ƙasa ke amfani da su, Monyae ya jaddada, yana nuni da fashewar kayayyakin sadarwa a lokaci guda a Lebanon.
Abin da Isra'ila ke yi kusan abin da wasu kungiyoyin ƴan ta'adda ke yi ne. Waɗannan dabaru ne da ƙasa a cikin ƙasashen duniya, da ke bin dokokin ƙasa da ƙasa, ba sa amfani da shi kuma ba a ƙyale su su yi amfani da shi.
Ƙarfin-faɗa-a-jin MDD Da ke rauni
Bazuwar tashin hankalin na zuwa ne lokacin da duniya ke sake nazari game da ikon da MDD ke da shi na tirsasa azzalumar ƙasa kamar isra'ila da kuma rage wahalhalun da fararen hular da ake kai wa hare haren ba tare da wani laifi nasu ba.
"Ƙungiyoyi irin su MDD ba su cancanci sunansu ba idan ba za a ƙyale su sauke alhakin da ke kansu ba da kuma cika alƙawarin da ta ɗauka na samar da zaman lafiya da tsaro a faɗin duniya," Monyae ya faɗa.
Yaƙe yaƙen da ke gudana a halin yanzu na Ukraine, da Myanmar, da Sudan da Gabashin Congo sun sake dagula lamarin, suna lashe kuɗaɗe da kuma rage tasirin da MDD ke da shi na share hawayen mutane mabuƙata.
Ƙasashen duniya, su ma, har yanzu ba su gano bakin zaren matsalar isra'ila da Falasdinawa ba.
"Ƙasashen duniya ba sa magana da murya ɗaya. A tsaka da wannan kisan kiyashin, ɗinbin makamai ake kai wa Isra'ila. Amurka ta kashe dala biliyan $8.7 kawo yanzu wajen ɗaura wa Isra'ila ɗammara," Monyae ya lura.
"Wannan shi zai janyo wasu ƙasashen suka bi sawu. Idan Russia da China da sauransu suka shiga, kuma Allah ya kyauta, idan muka samu kanmu a wannan yanayin, wataƙila sai mun yi amfani da wani abu mafi haɗari kamar yaƙi da makamin nukiliya. A kalli yaƙunan duniya na ɗaya da na biyu, haka waɗannan suka fara."
Tuni an kawar da hankalin duniya kan yaƙin sari-ka-noƙe da ake fama da shi a halin yanzu da suka haɗa da talauci, da cututtuka da kuma sauyin yanayi.
Babu mai yin nasara a yaƙi
"Afrika ba za ta samu cigaba ba idan ana gwabza yaƙe yaƙen da ba su da iyaka," Monyae ya yi gargaɗi.
"Abin da yaƙi yake yi shi ne ya dagula al'amurra, domin na san mutane da dama ba za su mutu sanadiyyar bam da kuma hare haren da muke gani ba, face sanadiyyar abubuwan da za su biyo bayan waɗannan yaƙe-yaƙen."
Raba ɗinbim mutane da muhallansu sakamakon tashin hankali shi ma yana haifar da wani matattarar cututtuka, yunwa da rashin tsaro, musamman ga mata da ƙananan yara.
"Fushi da takaici tsakanin mutane za su zamo barazana ga zaman lafiyar yankin da abin ya shafa na tsawon gwamman shekaru, ko ma tsawon shekara ɗari. Ba zai yiwu ka cim ma zaman lafiya ta hanyar amfani da bamabamai ba," in ji Monyae.
"Afrika a shirye take ta rungumi isra'ila ne kaɗai idan za ta bi dokokin da ƙa'idojin ƙasa da ƙasa, waɗanda ke kare haƙƙin bil adama da kuma tabbatar da mutunci da ƴancin cin gashin kai na al'ummar Falasɗinawa, wanda abu ne da Afirka ta yaƙa a wani lokaci.
"Nahiyyar na kallon Falasɗinawa a matsayin mutane da suka cancanci ƴanci kamar kowa," Monyae ya bayyana.