Daga Coletta Wanjohi
Hukumomi uku ne suke auna karfin kasashen Afirka wajen biyan basussuka a duniya – su ne: Standard and Poor's (S&P) da Moody's da kuma Fitch – abin yana ci gaba da zama abin takaici a nahiyar ganin yadda wadannan hukumomi ba sa yi wa nahiyar adalci.
Shi ma Shugaba William Ruto na Kenya ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ya kira "amfani da alkaluman da ba su da sahihanci".
"Hukumomin da ke auna karfin biyan basussuka kada su bari a yi amfani da su wajen tatsar kasashe masu tasowa wajen samar da alkaluma da ke jirkita kudin ruwa, wanda hakan ke sa biyan bashin ke da dan karen wuya," in ji shi.
Tun shekarar 1994, Afirka ta Kudu ta zama kasa ta farko daga nahiyar da aka auna karfin biyan basussukanta, daya daga cikin hukumomin auna karfin biyan basussuka sun auna karfin biyan bashin akalla kasashe 32.
Bayan wani lokaci, bakin kasashen Afirka ya zo daya kan cewa hukumomin uku "ba sa yi musu adalci" a kan alkaluman da suke fitar wa a kansu.
Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya kan Kasuwanci da Ci gaba (UNCTAD) ya ce alkaluman mara sahihanci kan Afirka ya sa su biyan kudi sosai wajen biyan kudin da ke kan bashinsu, kudin da za su biya zai ragu idan da a ce alkaluman sahihai ne bisa la'akari da karfin tattalin arzikin kasashen.
"Kasashen Afirka suna biyan kudin ruwa nunki takwas a kan basussukan da suka ciyo idan aka kwatanta da takwarorinsu a nahiyar Turai, kuma nunki hudu fiye da Amurka saboda alkaluma marasa sahihanci daga hukumomin auna karfin biyan basussuka na duniya," in ji Sakatariya Janar ta UNCTAD Rebeca Grynspan.
Labari bangare daya
Ana nazari mai zaman kansa ne don auna karfin biyan bashin kasa saboda bai wa masu zuba jari damar fahimtar hadarin da ke tattare da zuba jari a kasar da kuma hadarin da ke tattare da siyasar kasar.
Ko da yake sukar alkaluman da suka fito daga hukumomin auna karfin biyan basussuka, wanda hakan yake taimaka wa tsare-tsaren manyan cibiyoyin kudi na duniya da ke sanya kasashe dogaro kan tsare-tsaren tattalin arziki – abin da ke sa shakku kan ko hukumomin suna amfani da alkaluman masu zaman kansu.
"Yana da muhimmanci sosai a ce an samar da sahihan alkaluman kan karfin biyan basussukan kasashen Afirka, wanda kai-tsaye yake nuna yawan kudin ruwan da za su biya da sauran tsare-tsaren biyan bashin," kamar yadda wani rahoto na Shirin Ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.
Wani rahoto na Shirin Ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2023 ya bayyana cewa: "Kasashen Afirka za su iya samun rarar dala biliyan 74.5 idan da a ce ana samar da sahihan alkaluman auna karfin biyan basussukan kasashen nahiyar."
"A kula da labarin da aka samu daga bangare daya," in ji Ken Gichinga, babban masani kan tattalin arziki a cibiyar nazari kan tattalin arziki ta Mentoria Economics a Kenya, cibiyar tana samar tsare-tsare ga kamfanoni a nahiyar Afirka.
"Idan da a ce muna da hukumomi da za su yi amfani da alkaluma wajen daukar mataki, da abin ya zama mai hadari. Wasu hukumomi suna auna kasa ne saboda muhimmancin gwamnati da kananan abubuwa da ke shafar wani bangare na tattalin arzikin. Saboda mai zuba jari ba shi da cikakkun alkalumma," in ji Gichinga.
A shekarar 2023, Ghana da Nijeriya da Kenya da Masar da kuma Maroko sun samu kankanin maki bayan hukumomin S&P da Moody's da kuma Fitch sun auna karfin biyan basussukansu. Nijeriya da Kenya sun yi watsi da alkaluman inda suka ce alkaluman ba su yi la'akari da ci gaban da kasashen suka samu ba ta fuskar tattalin arzikin cikin gida.
"Ba na ganin ya kamata a damu da wadannan hukumomin auna karfin biyan basussuka," in ji Erick Mokaya, wanda ya kafa Mwango Capital, wani shafi da ke nazari kan tattalin arziki a intanet.
Ya ce wadannan hukumomi suna duba abin da yake zahiri ne da kuma bukatar samar da sauye-sauye ta fuskar tattalin arziki.
"Za ka iya amincewa da bayanansu lokaci zuwa lokaci, da ma a lokuta da dama, yawancin kasashe ne suke biyansu kudi don su yi aikin. Tabbas, za su iya kin amincewa da su, amma ba su ki amincewa da su gaba daya ba."
A samar da hukuma ta Afirka
Wani rahoton hadin gwiwa na cibiyar Africa Peer Review Mechanism da Hukumar Tattalin Arzikin ta Majalisar Dinkin Duniya kan Afirka ta zargi hukumomin Moody's da Fitch da kuma S&P da "tafka manyan kura-kurai a alkalumansu".
Kuma duk da haka su ake dogaro da su wajen daukar matakan da suka shafi kudi a duniya.
A shekarar 2019, Tarayyar Afirka ta yi yunkurin kafa hukumar auna karfin biyan basussuka ta Afirka. Ko da yake, har yanzu batun samar da hukumar auna karfin biyan basussuka a nahiyar bai tabbata ba.
Mokaya ya ce abu ne "mai wuya" a samar da hukumar saboda hukumomin auna karfin biyan basussuka uku ba a iya maye gurbinsu ba.
"Ta yaya hukumar auna karfin biyan basussuka ta Afirka ta kasance mara goyon bayan kowane bangare? Shin za ta ba kasashen Afirka alkaluma masu kyau ko da kuma bayanai sun bukaci kasar ta kara bunkasa tattalin arzikinta?" in ji shi.
Wasu masana suna cewa idan ana so a yi nasarar kafa hukumar a Afirka, matakin farko shi ne a yi nazari kan muhimman alkaluma da suka shafi Afirka.
"Mun fara ganin tasowar hukumomin auna karfin biyan basussuka na Afirka, amma sai sun bunkasa nazarinsu da hasashensu dangane da kasuwa," kamar yadda masanin tattalin arziki Gichinga ya bayyana.
“Idan suna so a amince da su, to sai sun yi abin da ya wuce fitar da alkaluma kawai. Ya kamata su nuna zurfin fahimtarsu kan tattalin arzikin duniya ta amfani da bayanan da za su iya samu."
Yayin da nahiyar take ci gaba da jiran yiwuwar samun hukumar auna karfin biyan basussuka, masana suna cewa abin da zai magance matsalar a gajeran zango shi ne tattara bayanai da yada su tsakanin hukumomin auna karfin biyan basussuka na duniya na yanzu, a wani kokari don a yi musu adalci.
Wannan zai rage matsalar cogen alkaluman da ke mayar da Afirka wadda ke da hadari a idon masu zuba jari da cibiyon bayar da basussuka.