Wani hayaki na tashi a lokacin arangamar da aka yi tsakanin ɗakarun sa kai na gaggawa RSF da sojojin Sudan a birnin Khartoum. Hoto / Reuters  

Daga Mazhun Idris

Babu wani yaki da ya fi wani kyau ko muni, sai dai a wannan fikirar hankalin duniya ya fi karkata kan tashe-tashen hankula da suka fi mamaye kafafofin yada labarai.

Yayin da Isra'ila ta kwashe tsawon shekara guda ta na kan luguden wuta a Gaza da kuma yakin Rasha da Ukraine sun kai a kwatanta da yakin cacar baka, bala'in rashin ayyukan jinƙai da ya mamaye Sudan tun daga watan Afrilun bara da alama ba ya idon duniya.

Ƙiran da Turkiyya ta yi a baya-bayan na ɗaukar mataki ta bakin jakadanta a Sudan Faith Yildiz, wani muhimmin tunatarwa ce kan cewa dukan ayyukan jinƙai ya cancanci kulawa da shiga tsakani.

''Bai kamata a yi watsi da Sudan ba,'' in ji wakilin, yana mai jaddada cewa, akwai buƙatar duniya ta taimakawa al'ummar ƙasar da ke yankin arewacin Afirka wajen yaki da da bala'in matsalar jinƙai da yunwa da kuma gudun hijira.

A taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da aka kammala kwanan nan, Sakatare-Janar Antonio Guterres ya taɓo batun rashin hukunta ƙasashe masu ta da kayar baya, da kuma rashin adalcin duniya wajen tallafa wa al'ummomin da ke cikin tashin hanakali da sauran wasu dimɓin matsaloli da ka iya dabaibaye duniya, inda ya ƙarkare da cewa babu wanda yake da tabbacin yaushe za a iya kawo arshen waɗannan tarin matsaloli.

Wani abin mamaki shi ne, sai daga ƙarshe babban sakataren na MDD ya ambaci Sudan a yayin da yake lissafo muhimman tashe-tashen hankula da ake fama da su a sassan duniya da dama.

A zahiri, mafi akasarin masu jawabi a taron majalisar na shekara-shekara mai wakilai 193, ciki har da shugabannin ƙasashen Afirka, ba su mayar da hankali sosai kan rikicin da aka kwashe watanni 18 tana cin Sudan.

Ƙin tsagaita wuta a cikin ƙasar

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Yakin Sudan tsakanin Sojojin ƙasar ƙarkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun gaggawa na Rapid Support Forces (RSF), ƙarkashin jagorancin Mohamed Hamdan Dagalo, ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 20,000 ya zuwa yanzu.

Tom Perriello, wakilin Amurka na musamman a Sudan, ya bayyana munin lamarin, yana mai cewa adadin waɗanda suka mutu na iya zarce mutum 150,000 idan aka ci gaba da gwabza yakin.

Yakin da ake gwabzawa tsakanin Sojojin Sudan da dakarun RSF ya kuma raba mutane miliyan 12 daga matsuguninsu, adadin da MDD ta ce shi ne mafi muni da aka taba samu.

Sama da 'yan gudun hijirar Sudan 800,000 ne a halin yanzu suke neman mafaka da kariya a ƙasashe makwabta. Kazalika rikicin ya kuma tilastawa sama da mutane 220,000 da suka dawo daga Sudan sake barin ƙasar.

Janar biyu da ke adawa da juna

Ba kamar sauran rikice-rikice da ake fama da su a duniya ba, karin matsin lamba na duniya na iya zama muhimmi mataki na dakile rikicin Sudan.

Richard Gowan, Darektan MDD a fannin kula da rikice-rikicen kasa da kasa, na son Amurka ta jagoranci yunkurin jawo hankalin kasashen duniya kan yakin Sudan.

Yunƙurin yankuna da ƙasashen duniya da dama wajen samar da zaman lafiya ya gaza kawo ƙarshen zubar da jini zuwa yanzu, lamarin da ke nuni da cewa a yanzu dole sai ƙasashen duniya sun tilasta wa bangarorin biyu da ke rikici da juna su amince a soma tattaunawa tare da ƙarfafa matakan jinƙai ga rkicin.

A yayin taron MDD karo na 79 da aka gudanar a ranar 24 ga watan Satumba, Shugaban Amurka Joe Biden ya bukaci ''duka ƙasashe su daina samar da kayan yaki ga manyan janarorin biyu da ke yaki da juna a ƙasar.''

Yakin Sudan ya jawo mafi munin yanayin jinƙai a duniya.  

'Yan gudun hijira da cututttuka

Sudan, wacce ke da faɗin kasa ta uku mafi girma a Afirka kuma mai yawan jama'a kusan miliyan 50, tana da tarihin karɓar 'yan gudun hijira cikin aminci.

Ƙasar da ke yankin arewacin Afirka, da ke da tarihi tun daga zamanin Fir'auna, ta taɓa karbar bakuncin 'yan gudun hijira na biyu mafi yawa a Afirka.

Sannan ta kasance matsuguni ga 'yan gudun hijira sama da miliyan daya daga Sudan ta Kudu, da Eritriya da Siriya, da Habasha, da Chadi, da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Amma tun daga shekarar bara Sudan ta kasa rike 'yan kasarta.

Tuni dai har wasu ‘yan gudun hijirar sun nemi mafaka a ƙasashe masu nisa kamar Yaman da ke tsallaken tekun Bahar Maliya, babban jami’in kula da ‘yan gudun hijira na MDD, Filippo Grandi, ya yi gargadin cewa, a yanzu haka wasu iyalai da suka rasa matsugunnansu na kan hanyar shiga kasashen Libya da Tunisiya don zuwa Turai.

Ƙididdigar baya-bayan nan da ƙungiyoyin MDD suka yi fitar sun yi nuni da cewa "mutum biyu daga ciki uku 'yan Sudan sun gaza samun kulawa ta lafiya.'' Sannan kimanin yara miliyan 19 ne aka tilastawa barin makaranta.

A watan Satumba, ƙungiyar kula da lafiya ta duniya Medecins Sans Frontières (MSF) ta bayyana yanayin kiwon lafiya a sassan Sudan a matsayin "rikicin da ya zarce kowanne".

Wata manaja a MSF, Dakta Gillian Burkhardt ta shaida wa TRT Afirka cewa ta ga mutane da yawa sun mutu cikin sa'o'in farko da aka kwantar da su a asibiti ''saboda sun riga sun shiga cikin mawuyacin hali kafin a kawo su wurin mu.''

Musamman take magana kan halin da ake ciki a asibitocin Nyala da Kas dake Kudancin Darfur, inda jarirai 48 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar sankarau tsakanin watan Janairu zuwa Yuni.

Rahoton na MSF ya kuma ambaci mutuwar mata masu juna biyu 46 a asibitoci biyu a tsakanin watan Janairu zuwa Agusta, inda aka kuma samu mutuwar kashi 78 cikin 100 na masu juna biyu a cikin awannin farko 24 da aka kwantar da su.

Waiwaye kan El Fasher

A ranar 27 ga watan Satumba, aka kai hari kan wata kasuwa a birnin El-Fasher na Sudan, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 18.

Wannan dai ya faru ne kwanaki huɗu bayan da shugabannin ƙasashen duniya suka hallara a birnin New York domin halartar taron MDD, lamarin da ke nuni da yadda rikice-rikice daban-daban suka dabaibaye Sudan.

Matsuguni ga sama da mutane miliyan 1.7, ciki har da mutane 500,000 da ke gudun hijira, El Fasher babban birni ne a Arewacin Darfur, kuma yana kusa da iyakar Libya da Chadi.

A sansani mafi kusa na 'yan gudun hijira Zamzam, ana fama da tsananin yunwa a yayin da MDD ke fafutukar tattara kuɗaɗe don kai taimakon jinƙai.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa fiye da rabin al'ummar Sudan na fama da yunwa ko kuma ƙarancin abinci mai gina jiki iri daban-daban.

A watan Fabrairu, MDD ta buɗe wani asusun tallafi na dala biliyan 4.1 don kawar da yunwa da kuma taimakawa 'yan gudun hijirar da ke samun mafaka a ƙasashe maƙwabta.

A ranar 1 ga watan Agusta ne aka ayyana matsalar yunwa a yankin Darfur ta Arewa, a yanzu haka kuma an yi imanin cewa wasu yankuna na cikin haɗari.

A cikin wannan baƙin yanayin baki-ɗaya, ɗaiɗaikun shirye-shirye na ayyukan jinƙai suna samar da ƙyakyawar fata.

Turkiyya da Kuwait sun haɗa gwiwa don aikewa da wani jirgin ruwa mai ɗauke da kayan agaji zuwa Sudan kwanan nan, inda zai kai kusan tan 2,500 na kayayyakin agaji da darajarsu ta kai sama da dalar Amurka miliyan biyu. An karbi kunshin tallafin a Port Sudan a ranar 2 ga watan Oktoba.

TRT Afrika