Jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta Kudu, ɗaya daga cikin waɗanda suka yi gwagwrmayar ƙwatar 'yanci da ke Afirka, na fuskantar ƙalubale mafi girma a zaɓe mai zuwa, kuma a karon farko cikin shekara 30 za ta iya rasa rinjaye a majalisar dokoki, kamar yadda kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta bayyana.
Ga matasa masu zaɓe, kaucewa gwagwarmayar 'yanci da jam'iyyar ta cim ma a baya da kuma neman mafita daga matsin tattalin arziki da ake fama da shi a yanzu na ƙara zame musu abu mai wahala.
Bayan jagorantar gwagwarmayar ƙalubalantar mulkin tsiraru farar-fata, jam'iyyar na fuskantar matsalolin taɓarɓarewar tattalin arziki, da rashin ayyukan yi da zargin cin hanci da rashawa da rashin wutar lantarki da ya kassara mafi yawan ƙasashen Aifirka.
Tafiyar hawainiyar haɓaka
Tabbas halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki na ɗaya daga abin da ke kan gaba a tunin matasa lokacin da suke tafiya mfunan kaɗa kuri'a a babban zaɓen ranar 29 ga Mayu.
Yanayin samar da ayyukan yi ba ya biyan buƙatun masu neman aiki, wanda hakan ke sanya a samu masu zaman kashe wando da adadinsu ya kai kashi 32 a 2023, kamar yadda alƙaluman Bankin Duniya suka bayyana a watan da ya gabata.
Baitulmalin ƙasar ya ce bunƙasar kasar da kashi 0.8 tun 2012 bai wadatar ba wajen rage talauci da rashin ayyukan yi.
"Tattalin arzikin ba ya bunƙasa duk da cewa mun fuskanci ƙarancin kuɗi a duniya a lokacin annoba," in ji David Monyae, Farfesa kan Nazarin Kimiyyar Siyasa.
"Ƙasar kanta ta gaza yin wasu abubuwa da wasu ƙasashe suka iya gudanarwa a ƙarƙashin irin wannan yanayi a duniya."
Matsalar lantarki da rashin ayyukan yi da ƙarancin shigar matasa harkokin shugabanci sun janyo rashin yarda daga ɓangaren matasa masu jefa kuri'a waɗanda ba lallai su fita rumfunan zaɓe ba, in ji Otsile Nkadimeng, Shugaban Ƙungiyar Wayar da Kai ta 'SoWEVote'.
Matsalar lantarki
Mafi yawan matasa ba sa 'kallon kawunansu a matsayin wani ɓangare na gwamnati," in ji shi yayin tattauna wa da TRT Afrika. Matasa "Ba su san ANC a matsayin wadda ta kuɓutar da ƙasar ba," in ji Nkadimeng.
Nkadimeng ya buƙaci matasa da su fita su jefa kuri'a a zaɓukan, duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
A Afirka ta Kudu, haɓaka cikin tafiyar wahainiya ta afku ne sakamakon rashin wadatacciyar lantarki da ke kawo cikas ga ayyukan tattalin arziki tun 2007. Cibiyoyin lantarki na ƙasar sun tsufa saboda biris da aka yi da su tsawon shekaru, kuma farfaɗo da su zai ɗauki wasu shekaru biyu.
Katsewar lantarki, ta kawo raguwar hakar ma'adanai da samar da kayayyaki, wadanda tubala ne guda biyu na habakar tattalin arziki. Matsalar ta kara yawan kudaden da ake kashe wa wajen samar da kayayyaki da shafar gudanar da ayyukan gwamnati.
Bankin Duniya ya yi hasashen katsewar lantarki a kowacce rana ya kai na awanni 4, wanda ya yi daidai da kwanaki 289 a 2023.
Wannan tsananin rasin lantarki ya shafi farfaɗowar tattalin arziki bayan Covid-19 wadda ta kassara ƙasar sosai.
Zargin cin hanci da rashawa da ta'annati da kuɗaɗen gwamnati ma wata babbar matsala ce. A 2022, an miƙa wa Shugaba Syril Ramaphosa wani rahoto da aka fitar na tsawon shekaru huɗu kan cin hanci da rashawa a karkashin tsohon shugaba Jacod Zuma, ga shugaba.
Babban batun cin hanci na baya-bayan nan shi ne na Shugaban Majalisar Dokoki Nosiviwe Mapisa-Nqakula wanda ta yi murabus daga matsayitsayinta yayin da ake tsaka da gudanar da binciken rashawa a lokacin da take matsayin ministar tsaro. Ta musanta aikata wani laifi.
Hukumar Afirka ta Kudu da ke sanya idanu kan ayyukan cin hanci, ta musanta kalaman shugaban Ramaphosa kan cin hanci da cewar ya ragu a lokacin wa'adin mulkinsa na farko.
"Cin hanci da rashawa ya ƙaru sosai a shekaru goman da suka gabata," in ji Karam Singh, daraktan zartarwa na hukumar.
Laifukan tashin hankali
Yawan rashin aikin yi ya ƙara rura wutar laifuka da kuma ƙyamar baki.
Ƙasar ta samu rahoton kisan kai kusan 84 a kowace rana tsakanin watan Oktoba zuwa Disamban 2023. Sakamakon hakan ya nuna cewa matakin rashin daidaito a ƙasar na daga waɗanda suka fi yawa a duniya, inda ya fi shafar baƙaƙen mutane.
Wani shirin ƙasa kan yaƙi da kyamar baƙi da nuna wariya bai rage tashe-tashen hankula ba, a cewar Ƙungiyar Kare Hakkin 'Dan’adam ta Human Rights Watch a wannan watan.
Rahoton ya yi gargadin cewa kalaman ƙyamar baki da 'yan siyasa ke amfani da su a lokutan yaƙin neman zabe na iya haifar da karin tashin hankali kan ƙyamar baki.
Jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance ta ce taɓararɓewar tattalin arziki ka iya dauwama tare da tsananta yanayin rayuwar 'yan Afirka ta Kudu idan har jam'iyyar ANC ta ci gaba da mulki.
Sai dai jam'iyyar ANC ta ce, ta ɗauki matakai na kyautata jin daɗin 'yan kasar a tsawon shekaru sannan ta yi alkawarin inganta yanayin rayuwa ta gaba.
Hasashen da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi ya nuna cewa Afirka ta Kudu za ta dawo da matsayinta a na ƙasa mafi ƙarfin tattalin arziki a nahiyar Afirka a shekarar 2024.