Hauhawar farashin kayan abinci na karuwa a Nijeriya inda a watan Oktoba hukumar NBS a Nijeriya ta ce hauhawar farashin abinci na kan maki 31.52. / Hoto: Getty Images

Sakamakon hauhawar farashin sukari, Ishaq Abdulraheem wanda wani mai gidan burodi ne a Nijeriya ba shi da wani zabi. Karuwar farashin burodi na nufin rage ciniki, wanda hakan ya sa mai sana’ar gasa burodin ya yanke shawarar rage adadin burodin da yake samarwa da rabi.

Ga masu kamfanonin burodi da dama, suna ta kokarin ci gaba da gudanar da sana’ar duk da hauhawar farashin man fetur da kuma fulawa, wanda tashin farashin sukari a halin yanzu ya sa lamarin ya kara kazancewa.

Ana bukatar sukari domin yin burodi, wanda abinci ne ga ‘yan Nijeriya miliyan 210, haka kuma ga jama’a da dama wadanda suke gwagwarmayar samar da abinci a gidajensu, burodin yana samar musu da sinadarai masu sa kuzari a jiki.

Sai dai karuwar farashin sukarin – wato karin da aka samu na kaso 55 cikin 100 a cikin watanni biyu – na nufin kamfanonin gasa burodi kadan za su yi aiki kuma su samar da burodi kadan.

“Babban lamari ne wannan,” in ji Abdulraheem.

Sukari a halin yanzu ya yi tsada mai yawa wadda ba a taba samun irin ta ba tun daga 2011, musamman saboda karancinsa bayan rashin yanayi mai kyau da ya kawo cikas ga tsirrai a Indiya da Thailand, wadanda su ne kasashen da suka fi samar da sukari a duniya.

Wannan shi ne bala’i na baya-bayan nan da ke samun kasashe masu tasowa wadanda ke fama da karancin abincin yau da kullum wadanda suka hada da shinkada da wake.

Isa Ahmed na nuna sukarin da yake sayarwa a Abuja. / Hoto: AP

Kasashen da suka dogara da shigar da kayayyaki

Brazil ce kasar da ta fi samar da sukari a duniya, sai dai girbin da ta yi a halin yanzu zai taimaka ne kawai a shekarar 2024.

Har zuwa lokacin, kasashen da suka dogara da shigar da sukari daga waje musamman kasashen Afirka su lamarin ya fi shafa. Misali Nijeriya, na sayen kaso 98 cikin 100 na kayayyakin hada sukari daga kasashen waje.

A 2021, kasar ta haramta shigar da sukarin da aka sarrafa wanda ya sa aka yi shirin gina wata babbar masana’antar sarrafa sukari da kuma sanar da aikin kan dala miliyan 73 domin fadada aikin sukarin.

Sai dai hakan duk wasu shirye-shirye ne masu daukar lokaci. ‘Yan kasuwa kamar su Abba Usman a halin yanzu na fuskantar matsala.

Buhun sukari kilio 50 da Usman ke saya a mako guda da ya gabata kan dala 66 a halin yanzu yana kan dala 81.

A daidai lokacin da farashi ke ci gaba da hauhawa, kwastamomi na kara raguwa. Ana ganin hakan ya samo asali ne sakamakon sauyin yanayi da dumamar yanayi ta El Nino wadda ke jawo tsananin zafi da karancin ruwan sama da ambaliya.

Masana kimiyya na ganin cewa matsalolin da ake fuskanta na sauyin yanayi na sa El Nino na kara karfi. Indiya ta sha fama a watan Agustan da ya gabata sakamakon karancin ruwan sama, inda tsirrai a yammacin jihar Maharashtra wadanda akasarinsu rake ne, sun samu matsala.

Haka kuma a kasar Thailand, irin tasirin da El Nino ta yi ba wai ya shafi adadin girbin da aka yi ba kadai, har shi kansa ingancin girbin, in ji Naradhip Anantasuk, shugaban manoman sukari na Thailand.

Yana sa ran tan miliyan 76 kadai na rake za a sarrafa a 2024, idan aka kwatanta da miliyan 93 da aka sarrafa a bana.

AP