Kayan Turkiyya a wani babban kanti da ke Gabashin Afirka/ AA

Daga Lulu Sanga

Ba abin mamaki ba ne ka ji dan kasuwa a Tanzaniya yana tunkahon cewa kayayyakinsa na Turkiyya ne.

Har ta kai wasu suna sanya wa shagunansu sunan Turkiyya ko kuma Uturuki, wanda yake nufin Turkiyya a harshen Swahili.

Daga cikin fitattun shagunan kayayyakin Turkiyya a Tanzaniya akwai na labulen Turkiyya da abayar Turkiye da wajen cin abincin Istanbul da shagon kayan yara na Uturuki.

Wannan ba sabon abu ba ne a manyan kasuwannin kasar irin su Kariakoo da sauran manyan birane kamar Dodoma da Mwanza da Arusha, kai har ma da masu sayar da kayayyaki a kafofin sada zumunta.

Masu shagunan sukan yi kurin cewa, 'Kayayyakina na Turkiyya ne." Hakan ke sakawa farashin kayayyakin su zama daban a kasuwannin.

A da can, kayayyakin kasar China ne suka mamaye kasuwannin Tanzaniya, musamman a bangaren sutura da kayan lataroni da kayayyakin gida, amma saboda yadda mutane suke son kayayyaki masu karko, sai sannu a hankali suka fara komawa sayen kayayyakin Turkiyya, wanda hakan ya sa suka danne na China.

Kafar yada labarai ta TRT Afirka ta zanta da Bahati Mwanjala, 'yar kasuwa da ke safarar kayayyaki daga China da Turkiyya. Ta ce kayayyakin Turkiyya sun fi na China karko.

"Idan ana batun inganci ne, kayayyakin Turkiye sun fi karko, sannan sun fi tsada. Amma ya danganta ne da yanayin aljihun kwastoma da zabinsa.

"Wadanda suke da kudi ba su cika damuwa da tsadar kaya ba, wanda hakan ya sa suka fi sayen kayayyakin Turkiyya. Amma masu karamin karfi, sun fi sayen kayayyakin China," in ji ta.

Shin Turkiyya na nufin inganci ne a Tanzania?

TRT Afirka ta yi magana da Christian Kivengi, wani kwastoma da ya fi sha'awar sayen kayayyakin Turkiyya, wanda ya ce bai cika damuwa da tsada ba matukar kayayyakin suna da kyau da inganci.

A cewarsa, kayayyakin Turkiyya sun fi inganci sannan a ganinsa sun fi zama na alfarma.

"Mun sayi wasu yaduka a dala 400 amma akwai bambanci sosai. Yadin ba ya kodewa ko kama zufa. Ba za ka kwatanta kayayyakin nan na Turkiyya da na China ba: daga gani ka san akwai bambanci."

A game da al'adun Turkiyya, ya ce "Idan har kasuwancin yana da kaka, to wannan shi ne kaka mafi tsawo a kasar nan.

"Babu kakar farko ko ta biyu. Wani lokacin a kan dade kafin kayayyakin su karaso daga Turkiye, amma da kayan sun iso za ka san ba ka yi jiran banza ba," in ji Bertha Robert, wanda yake sayo kayayyaki daga kasar Turkiyya, a zantawarsa da TRT Afirka.

Wani masani kan harkokin kasuwanci, Kelvin Kibenje, ya ce Tanzaniya na bukatar karin kamfanoni domin bukatuwar mutanen kasar, wanda hakan ya sa da yawa daga cikin 'yan kasuwar Tanzaniya suke neman kayayyakin daga kasashen waje, musamman yankin Asia da Turai.

Sai dai saboda yanayin cigaban duniya da karin bukatar kayayyakin a kasuwa, yanzu 'yan kasuwa sun fara mayar da hankalinsu kan kayayyakin Turkiyya.

A shekarun baya, kwat din Turkiyya ne suka fi fice, amma yanzu kusan komai ciki har da sutura da kayan lataroni kai har ma da janareta duk ana shigowa da su daga Turkiye.

"Idan kana so ka nuna wa mutum cewa kayayyakinka suna da nagarta, dole ka ce masa kayayyakin Turkiye ne. Da ka fada haka, mutane za su yarda da kai.

"Akwai kasashe guda biyu da 'yan kasuwar Tanzaniya suke shigo da kaya, amma daya ne da an ambata ake nufin inganci: shi ne kayayyakin Turkiyya," in ji masanin a zantawarsa da TRT.

Kabanje ya ce yawancin 'yan kasuwar da suke zuwa masa domin neman shawarwari a kan shigo da kayayyaki suna da zabi.

Masu karamin karfi da matsakaita suna shigo da kayayyaki daga wasu kasashe, amma masu jari mai girma sun fi son shigo da kayayyakin Turkiye.

A hasashensa, nan da shekara biyar 'yan kasuwa da suke shigo da kayayyaki daga Turkiyya da masu manyan kantuna da masana'antu ne za su mamaye kasuwannin Tanzaniya.

TRT Afrika