Turkiyya da Masar na sun ƙudiri aniyar ƙarfafa alaƙarsu ta kasuwanci da kashi 50, daga dala biliyan 10 zuwa dala biliyan 15.
Wannan manufa za ta zama babban abin mayar da hankali a kai a wajen Babban Taron Haɗin Kan Turkiyya da Masar da za a yi a ranar Larabar nan, a yayin da shugaba Erdogan zai karɓi baƙuncin takwaransa na Masar Abdel Fattah el Sisi a Ankara.
Tattaunawa tsakanin shugabannin biyu za ta hada da batun ƙarfafa alaƙar tattalin arziki, tare da batutuan yankunansu kamar yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.
Ana sa ran a yayin taron za a sanya hannu kan yarjeniyoyin kusan 20 a ɓangarori daban-daban, ciki har da sha'anin tsaro, makamashi, yawon buɗe ido, kiwon lafiya, ilimi da raya al'adu.
Yarjejeniya zurfafa dangantaka
Tun tale-tale alaƙar kasuwanci tsakanin Turkiyya da Masar na da matuƙar muhimmanci.
Ana sa ran ziyarar ta Sisi za ta ƙara haɓaka zuba jarin Turkiyya a Masar, wanda a yanzu ya haura na dala biliyan uku.
A 2022, fitar da kaya dag Turkiyya zuwa Masar ya kai na dala biliyan uku, inda shigo da kaya daga Masar yake sama kaɗan da ya kama dala biliyan ɗaya, wanda ya kawo adadin zuwa dala biliyan 6.1.
Mafi yawan kayan Turkiyya da ake fitarwa zuwa Masar sun haɗa da injina, bakin ƙarfe, farin ƙarfe, da robobi, inda dag Masar zuwa Turkiyya ake sayen roba, takin zamani da baƙin ƙarfe.
Masar ce kasa ta 19 a jerin kasashen da Turkiyya ke zuba jari kai-tsaye inda take da dala miliyan 294, daga dala biliyan 46.5 na zuba jarinta kai-tsaye a ƙasashen waje. Ita ce ƙasa ta 36 a jerin ƙasashen da suka jari kai-tsaye a Turkiyya inda take da jarin dala miliyan 45, daga dala biliyn 130 d ake da shi.
Haka zalika ayyukan haɗin kai a ɓangarorin tsaro da faɗaɗa haɗin kai a sashen makamashi, musamman lamarin LNG, makamashin nukiliya, da makamashi mara gurɓata muhalli na daga batutuwan da za a tattauna a wajen taron.
Masar, 'muhimmiyar' ƙawa ga Turkiyya
Mustafa Denizer, shugaban Majalisar Kasuwancin Turkiyya-Masar da ke ƙarƙashin Hukumar Alaƙar Kasuwancin Ƙasashen Waje (DEIK) ya ce zuba jarin Turkiyya a Masar ya ƙaru a 2007 inda yanzu yake da ma'aikata 100,000.
Denizer ya ci gaba da cewa yanki mai muhimmanci da Masar take ciki da farashin makamashi da albashin ma'aikata mai rahusa ne ya sanya ta zama mai muhimmanci ga Turkiyya, inda ta zama ƙasa ta biyu da Turkiyya ke samar da kayayyaki.
Da yake bayyana cewa Masar na daya daga manyan abokan kasuwancin Turkiyya a arewacin Afirka, ya ce manufar haɓaka kasuwancin ƙasashen zuwa dala biliyan 15 abu ne da za a iya tabbatarwa saboda kyautatuwar alaƙar kasuwanci, siyasa da tattalin arziki a tsakanin ƙasashen biyu.