Ana sa ran tattalin arzikin Nijeriya zai habaka da kashi 3.3, in ji Bankin Duniya. Photo: Getty Images

Bankin Duniya ya rage hasashen ci gaban tattalin arzikin kasashen Kudu da Hamadar Saharar Afirkaa bana zuwa kashi 3.4 daga kashi 3.4 cikin 100, musamman saboda lalacewar tattalin arzikin Sudan a yakin basasa.

Sai dai kuma, ana sa ran habakar za ta kasance sama da ta shekarar da ta gabata ta 2.4, madalla da sayayya da zuba jarin 'yan kasuwa, in ji Bankin Duniyaa ranar Litinin a wani rahito da ya fitar na tattalin arzikin yankin.

"Wannan farfadowa ce da take tafiyar hawainiya," in ji Andrew Dabalen, shugaban sashen kula a Afirka na Bankin Duniya yayin ganawa da 'yan jaridu.

Rahoton ya mayar da hankali kan habakar shekara mai zuwa da zai kamakashi 3.9, sama da hasashen da Bankin ya yi a baya na kashi 3.8.

Rahoton ya kuma ce sakko da hauhawar farashi a kasashe da dama zai bayar da dama ba mahukunta su fara rag yawan kudin ruwan basussuka.

Habakar Tattalin Arzikin Nijeriya da Afirka ta Kudu

Sai dai kuma, hasashen habakar na fuskantar hatsari babba daga rikicin 'yan bindiga da sauyin yanayi irin su fari, ambaliyar ruwa da guguwa, in ji rahoton.

Da a ce babu rikicin Sudan, wanda ya lalata tattalin arziki da janyo yunwa da tsugunar mutane, da habakar yankin a 2024 ta zama sama da yadda aka yi hasashe da rabin maki, daidai da hasashen watan Afrilu, in ji mai bayar da basussukan.

Girmamar tattalin arziki a kasar da ta fi kowace ci gaba a yankin, Afirka ta Kudu, ana sa ran zai karu da kashi 1.1 a wannan shekarar, da kashi 1.6 a 2025. in ji rahoton, daga kashi 0.7 na shekarar da ta gabata.

Ana sa ran Nijeriya za ta habaka da kashi 3.3 a wannan shekarar, inda a shekarar 2025 kuma tattalin arzikinta zai girmama da kashi 3.6, yayinda Kenya, mafi karfin tattalin arziki a Gabashin Afirka, na iya habaka da kashi 5 a wannan shekarar, in ji rahoton.

Yankin Afirka ya habaka da kashi 5.3 a tsakanin 2000 da 2014, amma bular annobar Covid ta sanya tattalin arzikin yin kasa a baya-bayan nan.

Biyan basussuka

"Jimilla gaba daya, idan da hakan zai ci gaba tsawon lokaci, zai zama babbar matsala," in ji Dabalen.

Tattalin arzikin kasashe da dama a yankin ya rasa zuba jarin gwamnatoci da 'yan kasuwa, in ji shi, kuma farfadowa ta hanyar samun zuba jari kai tsaye ta fara ne a 2021 wanda har yanzu ba sosai ake samu ba.

"Yankin na bukata da yawa, na bukatar zuba jari sosai don samun farfadowa cikin hanzari... sannan ya iya rage yawan talauci," in ji shi.

Girmama a yankin na sam8un cikas daga yawaitar bashi a kasashe irin su Kenya, wadda ta fuskanci zanga-zangar adawa da karin kudin haraji a watannin Yuni da Yuli.

"Akwai matsalolin jinkiri na biyan kudin ruwan zuba jari," in ji Dabalen, yana mai alakanta hakan ga yadda gwamnatoci suka koma rantar kudade daga kasuwannin kudi a shekaru goman da suka gabata, mai makon daga hukumomin kudi irin su Bankin Duniya.

TRT Afrika da abokan hulda