Kasashe irin su Afirka ta Kudu da Nijeriya suna bin bayan Ghana wajen samar da hasken lantarki ga mutanensu/Photo:Reuters

Wani sabon rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya ce a kasar Ghana aka fi samun wutar lantarki a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Rahoton da ke auna yanayin harkokin kasuwanci da rayuwa a Afirka ya ce kimanin kashi 80 cikin 100 na mutanen Ghana ne ke samun wutar lantarki.

Ghana ta zarce kasashe masu arzikin makamashi irin su Nijeriya da Kenya a yanayin samar da wutar lantarki ga mutanensu.

Rahoton ya ce mutum miliyan 600 ko kashi 43 daga cikin 100 na mutanen Afirka ba su samu wutar lantarki ba a 2022.

Rahoton ya kara da cewa kashi 98 cikin 100 ko kuma mutum miliyan 590 da ba sa samun wutar lantarkin suna Afirka kudu da Sahara ne.

Yadda yawan al’ummar Afirka ke karuwa ya fi yadda ake samar da wutar lantarki a nahiyar, in ji rahoton.

Ya kara da cewar Afirka na da kashi 18 cikin 100 na mutanen duniya, yayin da wutar lantarkin da ake amfani da ita a nahiyar ba ta kai kashi 6 cikin 100 na wutar lantarkin da ake amfani da shi a duniya ba.

Rahoton ya ce ya kamata ‘yan kasuwa da gwamnatoci su sake matsa kaimi wajen saka jari a fannin wutar lantaki a nahiyar don ta wadaci nahiyar.

TRT Afrika da abokan hulda