Bankin Duniya ya ayyana kudin Nijeriya wato Naira, cikin kudaden da suka fi rasa darajarsu a fadin nahiyar Afirka. Naira ta rasa kashi 40 cikin 100 na ƙarfinta idan aka kwatanta da dalar Amurka bayan da aka karya darajarta a watan Yuni.
A cewar wani rahoto mai taken ‘Africa’s Pulse', wanda ya yi sharhi kan batutuwan da za su shafi tattalin arzikin Afrika a nan gaba, na watan Oktoban nan, an bayyana cewa Naira ta rasa kashi 40 cikin 100 na ƙarfinta a musayar dalar Amurka.
Rahoton na Bankin Duniya ya ce a bana Naira da kuma kudin kasar Angola, wato Kwanza su ne suka fi rasa daraja a yankin Afirka, daga farkon shekara zuwa yau. Hakan ya faru ne sakamakon wasu matakai da manyan bankunan kasashen suka dauka.
Matakin da Babban Bankin Nijeriya ya dauka na barin Naira ta yi gogayya da dalar Amurka da sauran manyan kudade a kasuwar hada-hadar kudade, ya haifar da gagarumar faduwar darajar Naira daga N473.83 kan duk $1, zuwa sama da N800 duk $1.
Rahoton ya nuna cewa faduwar ta yi ta faruwa ne a hankali, tun watan Maris na shekarar 2020, amma kuma sai abin ya yi tsamari bayan da Babban Bankin Nijeriya ya janye tallafin da yake bai wa Naira. Daga nan ne tazarar farashi tsakaninsu ta karu matuka.
A Afrika dai, sauran kudaden da suka fuskanci faduwar daraja a 2023 sun hada da kuɗaɗen:
- Sudan ta Kudu (faduwar kashi 33%)
- Burundi (faduwar kashi 27 %),
- Jumhoriyar Dimukradiyyar Congo (faduwar kashi 18%)
- Kenya (faduwar kashi 16%)
- Zambiya (faduwar kashi 12%)
- Ghana (faduwar kashi 12%)
- Rwanda (faduwar kashi 11%).