Karancin zuba jari zai kawo cikas wurin ci gaba a kasashe masu tasowa, in ji rahoton bankin duniya Photo/ AFP Archive

Bankin Duniya ya bayyana cewa za a samu raguwa mafi yawa a ci gaban tattalin arzikin duniya a cikin shekaru 30 daga nan zuwa shekarar 2030.

Bankin ya bayyana haka ne a wani rahoto da ya fitar a ranar Litinin mai taken “raguwar ci gaba na tsawon lokaci: Sauyi, abin da ake sa rai da tsare-tsare.”

“Kusan duk wasu abubuwa da suka habaka tattalin arziki da kawo ci gaba a shekara 30 da suka wuce na gushewa.

"Sakamakon haka, tsakanin 2022 zuwa 2020 ma’aunin tattalin arzikin kasashen duniya wato GDP ana sa ran zai ragu da kusan kashi uku bisa hudu daga matakin da yake a shekaru 10 na farkon karnin da muke ciki zuwa kashi 2.2 cikin 100 a duk shekara,” kamar yadda bankin ya bayyana.

Ga kasashe masu tasowa, ana zaton bunkasar tattalin arziki zai ragu da kashi 4 cikin 100 a duk shekara zuwa shekarar 2030, wanda hakan ke nufin ya ragu daga kashi shidan da yake kai a duk shekara daga shekarar 2000 zuwa 2010.

“Wannan raguwar za ta fi karfi ne musamman a lokutan da ake fuskantar matsalolin kudi a duniya ko kuma matsin tattalin arziki,” kamar yadda bankin duniyar ya yi gargadi.

Shugaban bangaren tattalin arziki na Bankin Duniya Indermit Gill ya ce, wannan raguwar da ake samu na da tasiri matuka ga karfin da duniya ke da shi na magance wasu matsaloli da ake fuskanta da suka hada da talauci da karancin riba da sauyin yanayi.

“Idan kasashe za su yi amfani da tsare-tsare na ci gaba mai dorewa, bunkasar tattalin arzikin za ta iya karuwa da kashi 0.7 wanda hakan ke nufin zai kai kashi 2.9 a duk shekara,” kamar yadda rahoton ya bayyana.

TRT World