Alkaluman sun karu da kashi 6.2 cikin 100 a bangaren gine-gine da kuma kashi 1.2 cikin 100 a fannin noma, sai dai a wannan lokacin an samu ragin kashi 2.6 cikin 100 a masana'antu/ Hoto: Taskar AA

Alkaluman tattalin arzikin Turkiyya da ake fitarwa a kowane uku a duk shekara sun yi nuni da cewa a rubu'i na biyu cikin shekarar 2023 an samu karin kashi 3.8 cikin 100, adadin da ya zarce hasashen kasuwa, a cewar bayanan hukumar kididdiga ta kasar TurkStat.

Jumullar kudaden kayayyakin cikin gida da Turkiyya ta samu yanzu ya karu da kashi 60.7 cikin 100 akan na bara na Lira tiriliyan 5.5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 271.5 a tsakanin watan Afrilu zuwa Yunin 2023, a cewar Hukumar TurkStat.

"Mun fara ganin sakamako mai kyau a manufofin da muka aiwatar. Za kuma mu ci gaba da daukar matakan da suka dace don tabbatar da dorewar matakan da kuma tabbatar da an daidaita su," in ji Ministan Kudi da Baitulmalin Turkiyya Mehmet Simsek.

Masana tattalin arziki sun yi hasashen tattalin arzikin Turkiyya zai karu da kashi 3.5 cikin100 a kwata ta biyu ta kowace shekara.

Adadin da aka samu ya biyo bayan hasashen kashi 3.9 cikin 10 na shekara-shakara cikin kwata ta farko ta 2023.

A watanni ukun farko zuwa watan Yuni, tattalin arzikin Turkiyya ya habaka da kashi 3.5%, lamarin ya nuna sauyin da aka samu a koma bayan kashi 0.1% na shekarun baya.

Sashen cinikayya na sari da sayen daya-daya da kuma ayyukan sufuri da fannin ajiya da wauraren kwana da kuma wuraren abinci - sun ba da gudunmowa ta kashi 6.4 cikin 100 na kudaden shigar kasar na shekara- shekara a tsakanin watan Afrilu zuwa Yuni.

Alkaluman dai sun karu da kashi 6.2 cikin 100 a bangaren gine-gine da kuma kashi 1.2 cikin 100 a fannin noma, sai dai an samu ragin kashi 2.6 cikin 100 a ayyukan masana'antu a wannan lokaci.

Kudaden da ake biya a kayayyaki da ayyukan ake shigowa da su kasar sun karu da kashi 20.3 cikin wata uku idan aka kwatanta da bara, yayin da kayayyakin da ake fitarwa suka ragu da kashi 9 cikin 100.

Baki daya zuwa wannan lokaci dai jumullar kudaden da gwamnati ta kashe sun karu da kashi 5.3 cikin 100.

Kazalika hukumar TurkStat ta ce ci gaban kudaden shiga na Turkiyya a 2022 ya ragu kadan zuwa kashi 5.5 cikin 100.

TRT World